LOKACI DABAN YAKE DA KUDI

LOKACI DABAN YAKE DA KUDI

Wata rana wani mutum ya dawo gida daga aiki a makare kwarai, a gajiye ya dawo ya tarar da yaronshi Dan shekara 5 a bakin kofa. Yaron ya tarbeshi yana murna. Bayan mutumin ya huta  kenan, sai yaron nashi yace mashi "Baba ina son na maka wata tambaya?" "Ina jinka." cewar mutumin.
"Baba,  nawa kake samu wurin aikinka a duk awa daya (1 hour)?" 
"Wannan ba matsalarka bace....me yasa kake irin wannan tambayar?" Mutumin ya bashi amsa, cikin yanayin bai son maganar.
"Kawai dai ina son sani ne. Dan Allah fada min... Nawa kake samu duk awa daya?" 
"kasan wani abu? ina samun dubu hudu (4k) ne a awa daya!" 
"Ah!" cewar Yaron, kansa a kasa  ya qara da cewa "Baba, ina son ka aromin dubu 2 (2k)."
Mutumin sai yaji haushi yace " Saboda wannan ne yasa kake min irin wannan tambayar? .... Kana tunanin haka ne zakayi ka samu kudin da zaka sayi kayan wasa? Maza wuce daki ka kwanta, kullum ina wannan aikin tukuru domin ganin na baka kulawa!" 
Yaron bai qara cewa komai ba yayi wucewarsa daki. 
Mutumin ya zauna ya fara tunanin dalilin da yasa yaron yayi masa irin wannan tambayar kawai don ya kawa bashi kudi? 
Bayan kamar awa ( after 1 hour) daya sai mutumin mutumin ya nufi daki ya tarar da yaron kwance yace "Yarona...Bacci kake?" 
"A'a baba idona biyu." cewar yaron tareda dago kansa...
" Bansan me zakayi da kudin ba, amman nasan wata qila kanada bukatarsu ne, ga dubu 2 dinda ka tambayeni."
Yaron cikin jin dadi, ya danyi qara...."Eeeeh, Baba nagode!" Yaron ya nufi inda yake ajiyar asusunsa ya fiddo shi, mutumin ya tsaya yana kallon ikon Allah, Wasu kudin yaron ya fiddo ya gama da wanda babanshi ya bashi yanzu, ya fara kirgawa... Mutumin dai ya kasa daurewa ya tambayi yaron nashi "Me yasa ka bukaci karin kudi, alhali kanada wasu...?" 
"Baba, saboda basu kai yanda nake sonsu ba.." yaron ya fada tareda cigaba da cewa " Baba, yanzu inada dubu 4, kuma nasan su kake samu a duk awa daya, baba yau ina son na sayi Awa daya daga cikin awoyin aikinka?...Dan Allah baba, ina son gobe ka dawo awa daya kafin dawowarka...domin ina son naci abinci tareda kai." Jikin mutumin yayi sanyi. Ya rungume Dan nashi yana kuka, yana neman gafararshi...

Wannan Dan karamin tuni ne ga Magidanta wandanda suke aiki tukuru a rayuwarsu, ta inda suka fi fifita aikinsu akan iyalensu, kar mu taqure lokacin mu wa masoyanmu ( Makusanta zuciyarmu) Mutanen da suke da bukatarmu a koda yaushe.

KARKU MANTA DA TURA WANNAN LABARIN ZUWAGA MASOYANKU. Domin idan aka wayi gari mun mutu, Wurin da mukewa aiki, cikin sauki zasu samu wani su musanyashi da mu. Amman Iyalenmu da abokanan mu wanda bamu ara masu lokacinmu ba fa?

Ku cigaba da Ziyartar shafin mu domin cigaba da amfanuwa da rubutunmu

Www.Ashblog.com.ng



Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)