Mai maganin bindiga ya mutu a yayin gwajin ta



Wani mai maganin gargajiya a Najeriya ya mutu bayan da
daya daga cikin abokan cinikinsa ya gwada karfin "maganin
bindigan" a kansa.

Mai maganin, Chinaka Adoezuwe, mai shekara 26 da
haihuwa ya mutu bayan da ya umarci mutumin da ya harbe
shi da bindigar a yayin da yake sanye da wasu layu a
wuyansa.
'Yan sanda a jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar
sun ce an kama mutumin da yayi harbin kuma ana
tuhumarsa da aikata kisan kai.
Maganin bindiga da danginsa kamar maganin wuka na da
farin jini sosai a Najeriya, kuma mutane da dama kan nemi
masu maganin gargajiya da su taimakesu da magungunan.
Amma an sha samun rahotannin wadanda suka mutu
bayan gwajin maganin bindiga a kasar.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)