Sanadin Link Complete - Ummeen Yusrah




Kwance take kan Gado hannunta d'auke da waya da alama tanajin dad'in hirar da suke a wani group mai Suna( MATAN AURE GROUP ) wata ke kwararomusu bayanin wani Maganin mata datasha yadda Oga ya gama Rikicewa jiya akata.

Inda 'yan group kowa ke tofa Albarkaci bakinta. Hafsat dake kwance tanajin Dad'in hirar tasu don ita  A duniya indai zataji irin wannan zancen zata iya bata Lokacinta, don yadda zata samu k'warin Gwiwar gara oga wajen harka. 

Sallama akayi tareda shigowa dakin da Gudu yaranta suka haura Gadon. Babban maisuna
Ahmad(sabeer) yace "Umma mun dawo",k'aramar maisuna Asma'u (sabeerah) tace "Umma yunwa nakeji."

 Abbansu na tsaye k'ofa bai Idda shigowa ba. yazubo Mata ido yana kallonta, don yasan bata d'aura Girkiba. Saukowa tayi tace "barin had'a muku tea, kafin na gama abincin."
 
Sai sannan yayi Magana Ranshi a b'ace "habba Hafsat ace kullum sai yara sundawo sannan kice zaki d'aura abinci! wannan wani irin Rayuwace? idan zasu tafi ba wani karyawar kirki sukeba, sannan sundawo ba abinci, kin d'auki dukkan Lokacinki kinbama Waya, wannan wani irin Rayuwace? fisabilillah! bakida Lokacin Gyaran Gidanki, bakida Lokacin yaranki, ace  Kullum kina kan waya. Gaskiya ki gyara nafara gajiya."

Wani kallon Raini tamai tace "uhmmmm saikayi kuma dad'in abin bakai kasaimin wayarba, balle kamin Gori."
Ta Murgud'a mai Baki tayi ficewarta, tabarshi wajen, Shigewa yayi ya cirema yaran kayan Makaranta ,sannan ya masu wanka ya shiryasu  ya sake fita dasu.

Tana zauna a Pallor ya wuce ta. Gidansu yakai yaran bayan sungaida Ummanshi yq kira k'anwarshi Rahma taba yarn Abinci.
Umma tace "ina ummar tasu?"
 "Tana Gida batajin dad'ine."
 "Ayyah Allah ya  bata lafiya Ameen."
 "Ummah nizan wuce sai yamma zanzo in d'aukesu."
  "Toh Allah yabada sa'a."
  
Tags

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)