MAHAIFIYA



Wanii sabon magidanci ne ( ango) , kiran waya ya tashe shi karfe 3 na dare.

Wayar ta cigaba da ruri, cikin kasala mutumin ya daga wayar ya kara a kunne :
-Hello, waye ?
-Nice, Dana , Mahaifiyarka.
-Ina jinki mama akwai matsala ne?
-A'a Dana, na kiraka ne dan naji Lafiyar ka.
-Eh mama, lafiya kalau nake, amman mama saboda wannan ne kika kirani a wannan lokacin?
-ko na takuraka ne?
-Gaskiya kam mama a wannan lokaci....
- ok shikenan Dana, zan barka ka kwanta, amman ka sani shekaru 26, nima a wannan lokacin kake hanani bacci . Ina sonka Dana, Allah ya Karemin kai.
Ta katse Wayar.
A take Kuka ya kwace masa...

Allah (swt) yace:

( kuma ubangijinka ya hukunta kada ku bauta wa kõwa face shi, kuma game da Mahaifa(biyu) ku kyautata masu kyautawa, koda dayansu ya kai ga tsufa a gurinka ko dukansu biyu, to, kada ka tsawace su, kuma ka fada musu magana mai karamci. kuma ka sassauta musu fikafikan tausayawa na rahama, kamar yadda suka yi reonana, ina karami. )
[Surat 17, ayat 23-24]

Wannan Labari, yana nuna mana tsantsar gaskiya ne, yana tuna mana Muhimmancin iyayen mu. Mu kasance masu kyautata masu a kowanne yanayi kowanne lokaci. Kar mu manta Aljannar mu na karkashin Kafafuwan Mahaifanmu, don haka mu kasance masu gujewa 6acin ran su.

ALLAH YA JIKAN MAHAIFAN MU, YA SAKA MASU DA GIDAN ALJANNA DA MU BAKI DAYA...

Ameen Summa Ameen!

Please share

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)