ABINDA WANI MATASHI YA GANI A CIKIN KABARI


ABINDA WANI MATASHI YA GANI A CIKIN KABARI.

Karanta a Natse... 

A lokacin kalifancin Abdul Malik ben 
Marwan ya ruwaito cewa :

- Wata rana Wani matashi yazo wajena a gigice, hankalinsa a tashe... Yace min ;

-Ya shugaban Mumunai, na aikata babban zunubi, shin Allah zai kar6i tubana?

-Wanne irin zunubi ne? Na tambayeshi

- Wani Babban zunubi. Cewar Matashin

- Zai iya kasancewa, inji kalifa Abdul Malik, ka koma ga Allah domin shine mai kar6ar tuba daga bayinsa kuma yana yafe laifukan bayinsa.

- Yau naje Makabarta, kuma na tona kaburbura wasu mutane, naga tashin hankali ba kadan ba. inji wannan matashi

-Me ka gani?

- A Wannan dare, naje makabarta na tona wani kabari, naga fuskar mamacin ta juye bata kallon Alqibla (Gabas). A tsorace, na juya da niyyar guduwa amman sai naji wata murya daga cikin kabarin tana cemin :

« Baka son sanin me yasa fuskar wannan Mamacin bata kallon Alqibla?»

- Me yasa? Na tambaya

« Saboda a lokacin da yake raye, yana mantuwa da Sallah kuma wannan shine hukuncin wanda ke mantuwa da Sallah.»

- Sai na qara matsawa na qara tona wani qabarin, sai naga siffar  Mamacin ta juye zuwa siffar Alade, kuma wuyansa daure da sarqa. Sai na tsorata, na juya da niyyar guduwa, amman sai naji wata murya daga cikin kabarin tana cewa :

« Baka son sanin Zunubin da wannan mutumin ya aikata, aka mayardashi haka?», na tambaya? aka ban amsa; « Ya kasance yana shan Giya ( barasa ), kuma har ya mutu bai tuba ba, wannan shine hukunci Mashayin giya idan bai tuba ba ».

A lokacin da na tona kabari na uku, ya kai shugaban Mumunai, naga Mamacin an daureshi da wasu Irin manyan igiyoyi, kuma harshensa ya hudo ta doron bayanshi. Na tsorata na juya da niyyar guduwa sai naji wata murya daga cikin kabarin tana mai cewa : 
« Baka son sanin me wannan Mamaci ya aikata aka masa irin wannan hukuncin?» ; Me yasa? Na tambaya; aka ban amsa « Ya kasance bayada aiki sai yada maganganu a cikin mutane ( Gulma ), ya kasance Maqaryaci kuma Munafiki, wannan shine hukuncin masu irin wannan hali ! »

- Lokacin da na tona kabari na hudu, na samu kabarin yana ci da wuta. Na tsorata sosai, na juya da niyyar guduwa sai naji wata Murya tana mai cewa : 
«  Baka son sanin, me wannan mutum yayi aka masa wannan hukunci? » ; Me ya aikata? Na tambaya, sai aka amsa min : 
« Wannan mutumin ya kasance ya bar Sallah kwata kwata, shi yasa wannan ya kasance hukuncinsa ! »

- A lokacin da na tona kabari na biyar, na tarar da Mamacin cikin shiga ta kamala, fuskarshi na kyalli, ga haske a ko'ina da murmushi akan fuskarshi. Na juya da niyyar tafiya sai naji wata Murya daga cikin kabarin tana mai cewa : 
« Baka son sanin me wannan Mamaci ya aikata, yake cikin wannan jin dadi?  » ; na tambaya aka ban amsa :
« Ya kasance tun daga yarintarshi, mai bauta ga Allah, da kuma bin duk wasu dokoki na Allah (T) .»

Bayan wannan Matashi ya dakata da labarinshi sai Kalifa Abdul-Malik yace :

- Wannan ya kasance Darasi ne, ga masu sa6on Allah da irin Nau'oin azabar ake masu idan har basu tuba sun koma ga Allah ba.
Mutum na biyar kuma ya kasance shine sakamako na duk wasu mutane masu bautawa Allah da bin dokokinshi .

Allah Ubangiji kai mana kyakkyawan karshe ......

Please Share

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)