Mummunar Cikawa : Wani mutum ya barwa iyalinsa abin kunya, bayan ya mutu a lokacikin da yaje kwartanci

- Yansanda sun kama matar da kwarto ya mutu a dakinta

Wani magidanci mai mata da 'ya'ya ya gamu da ajalinsa a ranar Laraba 9 ga watan Agusta a lokacin gidan wata budurwarsa dake rukunin gidajen kwalejin horar da mayakan Najeriya a babban birnin Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Magidancin ya rasu ne bayan daya kammala mu’amala tare da budurwar tasa yayin daya kai mata ziyara da misalin karfe 10 na safiyar ranar.

Rundunar Yan sandar jihar ta tabbatar da mutuwar Magidancin bayan da budurwa tasa mai suna Bridget ta kai kara ofishin Yan sanda dake Gwarinpa.

Bridget ta bayyana ma yansanda cewar bayan da suka kammala abin da suka saba da Magidancin ne, sai ya tashi ya sanya kayansa, yana shirin tafiya gida, kwatsam sai ya yanke jiki ya fadi matacce.


Sai dai mun samu labarin a yanzu haka Yan sanda sun garkame Bridget, inda suka garzaya da gawar mamacin zuwa asibitin Asokoro don gudanar da bincike akansa, kamar yadda DPO Nurudeen Sabo ya shaida.



Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)