Ikon Allah Hannun wani mutumi ya makale a jikin Qur'ani

Allah da iko yake, kamar yadda hoton wani mutumi ya karade yanar gizo, a cewar rahotanni Hannun wani mutumi ya makale a jikin Qur’ani bayan yayi yunkurin yin batanci da Qur’anin.



Wani mai amfani da shafin zumunta na Facebook mai suna Brendan Ortono ya yi da’awar cewa yana gurin da abun al’ajabin ya faru, cewa “Babu shakka, ina gurin, na tabbatar da hakan, munyi duk kokarin da zamuyi don muga mun cire Qur’anin daga hannun nasa amma duk kokarinmu a banza, domin mun kasa raba hannun nasa da Qur'anin. Ko yanzu da nake Magana da ku a yanzu, hannuwansa na nan makale da Qur’anin.

Ortono Brenden ya ce mutumin ya fara gudanar da mummunan kudirin nasa ne daga gida inda ya zana tambarin Cross a jikin Qur'ani, wanda kafin ya kai ga aikata ragowar rubutun da ya yi niyya, kawai sai ya ji hannunsa ya makale, kamar yadda yake shaidawa  mutanen da suka taru a wajen.


Duk da haka, har zuwa yanzu ba’a tabbatar da yankin kasar da abun ya faru a ciki ba.

Allah ya kyauta!

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)