"Kaico !! Ran Mutum ba a bakin komai yake ba a Nigeria" Cewar Shugaba Buhari

Buhari na bakin ciki da rashin mutunta ran Dan Adam a Nigeria.

Buhari ya bayyana bacin ranshi akan yawan kashe kashe da akeyi a Nigeria, inda yake cewa " Ran Dan Adam ba a bakin komai yake ba a Nigeria."

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 25 ga watan Yuli akan hare haren da aka kai jihar Filato, inda aka yi asarar rayuka sama da Tamanin, inda ya danganta lamarin ga wasu mutane dake yin duk mai yiwuwa don ganin sun tayar da hankula don su samu biyan bukata a zabe mai zuwa.


Buhari ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, inda yace gwamnatinsa na sane da yunkurin da 'yan siyasa ke yi don ribatan rikice rikicen nan;“Mun san akwai bukatu iri iri daku rura rikice rikicen nan, haka zalika muna sane da yunkurin yan siyasa.

"Hakan na faruwa sai wasu yan daba suka shiga fasa shagunan mutane, tare kai ma abokan hamayya a siyasance hari, har ta kai ga suna tare motoci suna kashe mutane idan ka nuna baka tare da wata jam’iyya” Inji Buhari.

Sanarwar ta cigaba da cewa hatta gwamnan jihar, Simon Lalong da kansa ya fatattaki wasu daga cikin yan daban nan da suka sanya shingen kan hanya suna tare mutane, a hanyarsa ta komawa gida daga babban birnin tarayya Abuja.

Daga karshe Buhari yayi kira ga duk wadanda rikicin manoma da makiyaya ya shafa da lallai su kyale doka tayi aikinta, kada su dinga daukar doka a hannunsu, sa’annan yace sun aika jami’an tsaro jihar don kare sake barkewar rikicin.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)