Kotun Tarayya ta amince ta saurari bukatar a tsige Buhari


Wata babbar kotu a Najeriya ta amince da bukatar da wasu
lauyoyi suka shigar na bai wa majalisar dokokin kasar
umarnin tsige Shugaba Muhammadu Buhari.

Alkalin babbar kotun da ke garin Osogbo jihar Osun, Mai
shari'a Onyetenu ce ta bayar da umarnin a ranar Laraba,
bayan da wani lauya - Kanmi Ajibola da Sulaiman Adeniyi
wani dan rajin kare hakkin dan Adam suka bukaci kotun ta
dauki wannan matakin.
Batun takardun shaidar kammala karatun sakandare na
Buhari na daga cikin bukatu hudu da mutanen biyu suka
gabatar a gaban kotun, inda suke zargin shugaban da saba
wa kundin tsarin mulkin kasar bayan rantsar da shi da
takardun da suka kira na bogi.
Sai dai tun lokacin yakin zabensa ne kwalejin gwamnati a
Katsina, inda Buhari ya kammala sakandare ta fitar da
takardar shaidar kammala karatun a shekarar 1961.
Zuwa yanzu gwamnatin Buhari ba ta ce komi ba game da
batun, sannan majalisar dokokin kasar ma ba ta ce komi ba
zuwa yanzu.

Lauyan da ya shigar da karar Mista Kanmi Ajibola ya shaida
wa BBC cewa kotun ta amince da bukatar ne bayan
gamsuwa da hujjojinsa.
Ya ce: "Kotu ta ba ni hurumi a kan karar da na shigar inda
na nemi a tilasta wa majalisun dokoki biyu na Tarayyar
Najeriya da su fara shirin tsige shugaban kasa Muhammadu
Buhari."
Mutanen biyu sun ruga kotu ne bayan majalisa ta yi biris da
bukatar farko ta tsige Buhari da suka shigar watanni uku da
suka gabata.
Sauran bayanan da suka gabatar a gaban kotun da suke
kalubalantar Buhari sun hada da gazawar gwamnati wajen
kawo karshen yawaitar kashe-kashe a rikicin makiyaya da
manoma.
Sannan sun zargi shugaban da yin gaban kasa wajen kashe
kudin kasa ba tare da amincewar majalisa ba.
A cikin bayanan da suka gabatar wa kotun, sun ce
"shugaban ya yi rantsuwa cewa zai mutunta kundin tsarin
mulki da kare rayuka da dokiyoyin 'yan kasa."
"Na kafa hujja a gaban kotu kuma bayan gamsuwa da karar
cewa shugaba Buhari ya gaza wajen kawo karshen kashe-
kashe a kasar, kotu ta ba da umarnin a tsige shi" in ji
Akanmi.
Kotun ta dage sauraron wannan karar zuwa 30 ga watan
Oktoba 2018.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)