Wata Tsohuwa Mai Shekaru 92 Ta Kashe Danta

'Yan sanda a Amurka sun ce wata tsohuwa mai shekara 92
ta kashe danta mai shekara 72 da bindiga domin ta hana shi
kai ta gidan kula da tsofaffi.

Anna Mae Blessing, wadda ake tuhuma da kisan gilla ta
nuna rashin jin dadinta game da aniyar danta na kai ta
gidan kula da tsofaffi, kamar yadda takardun da aka
gabatar a gaban kotu suka bayyana.

"Ka raba ni da raina, a kan haka zan dauki naka," haka
rahotanni suka ruwaito tsohuwar na cewa lokacin da 'yan
sanda suka zo gidan da take zaune da danta da buduwarsa
a Arizona.

Misis Blessing ta fada wa 'yan sanda cewa ta so ta kashe
kanta.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar 2 ga watan Yuli a garin
Fountain Hills, da ke karamar hukumar Maricopa, in ji
kafofin watsa labarai na garin.
Dan Misis Blessing, wanda ba a bayanna sunansa ba ya so
ta koma gidan kula da tsofaffi saboda babu "jituwa"
tsakaninsu.

'Yan sanda sun ce mahaifyar mutumin ta boye bindigogi
biyu a cikin rigarta kafin ta tunkari danta a cikin dakinsa.

A lokacin da gardama ta kaure tsakaninsu, ta fitar da daya
daga cikin bindigogin da ke hannunta, wadda ta saya a
shekarar 1970 kuma ta harbe shi.
'Yan sanda sun samu dan a mace, kuma akwai raunukan
harbin bindiga a wuyansa da makogoronsa.
Misis Blessing ta kuma nuna wa buduwar danta mai
shekara 57 bindiga, wadda ta kwace bindigar daga
hannunta ta jefar a wani bangare na dakin.
Sai kuma ta fitar da bindiga ta biyu, wadda ta fada wa 'yan
sanda cewa mijinta da ya rasu ne ya ba ta a shekarar 1970.
Sai dai budurwar ta kabe bindigar daga hannun Misis
Blessing kafin ta tsere kuma ta kira ofishin 'yan sanda.
'Yan sanda sun gano Misis Blessing kan wata kujera da ke
dakinta. Daga bisani ta fada mu su cewa ya kamata "a sata
ta yi barci" saboda abin da ta yi.
Ana zarginta da kisan gilla da sace mutum, kuma za ta biya
dala 500,000 a matsayin beli.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)