Jarumin Bollywood Suniel Shetty ya koma waka


Jarumin fina-finan kasar Indiya, Suniel Shetty, da aka jima
ba aji duriyarsa ba a fina-finai, yanzu zai fara waka bayan shafe shekara 18 rabonsa da wakar.

Suniel Shetty ya ce, yana matukar kewar magoya bayansa, hakan ya sa ya yanke shawarar ba ri ya taba waka, amma
ta cikin fina-finai ba.

Mutane da dama dai ba su san jarumin ya taba yin waka a
shekarar 2000 tare da wasu yara inda aka sawa wakar suna 'Jantar Mantar'.

Rahotanni sun ce, yanzu jarumin ya rera wata 'yar
takaitacciyar wakar bidiyo amma tallan wata tashar rediyo
ce wakar.

Suniel Shetty, ya ce ya yi wa tashar rediyon wadda ba a
budeta ba tukunna waka ne don ya dawo da basirarsa ta
waka.

Jarumin ya ce, saboda jimawar da ya yi bai yi waka ba, sai
da ya yi ta gwaji kafin a dauki wakar.
Suniel Shetty, ya ce, duk da muryarsa ba ta dadi a wajen
fitar da sautin waka, shi mai sha'awar wakar ne.

Koda aka tambayeshi ko ya taba waka a cikin fina-finan
Indiya, jarumin sai ya yi dariya, sannan ya ce " Bai taba yi
ba, amma kuma idan har magoya bayansa suna bukatar ya
rinka waka a cikin fina-finan kasar, to zai gwada".

Jarumin ya ce, ya samu kwarin gwiwar yin waka ga
sabuwar tashar rediyon ne, saboda goyon bayan da ya
samu daga iyalansa.

Wanene Suniel Shetty?
Masu kallon fina-finan kasar Indiya dai, za su iya sanin kowaye Suniel Shetty.

Jarumi ne wanda ya fito a cikin fina-finai sama da 110.

Yana daga cikin jaruman Indiya maza da suka iya fada a cikin fim.

A bangaren soyayya ma, Suniel Shetty ya iya yin soyayya da budurwa a cikin fim.
Baya ga fitowa a cikin fina-finai, Suniel Shetty ya na shirya fim, kuma dan kasuwa ne.
Kazalika ba a fina-finan Hindu kadai ya ke fitowa ba, har ma na Malayalam daTamil da kuma na turanci.

Suniel Shetty ya fito a cikin fina-finai da suka yi suna
kamar, Bhai da Dhadkan da Mohra da da Gopi Kishan da kuma Sapoot.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)