Azraa Complete - Halima MK

🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*_AZRAA_*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

© *HALIMA MK*


🌈 *KAINUWA WRITERS ASSO* ✍🏻

*BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*

*WANNAN LITTAFIN K'IRK'IRAREN LABARI NE BANYISHI DAN CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA INYAYI DAI-DAITO DA HALI KUSKUREN ALK'ALAMI AKASAMU*

*SADAUKARWA GA :*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISA* *{KE ALHERI CE}*

*PAGE 1*

*SOKOTO BIRNIN SHEHU*

*D'*akin taron makil yake da jama'a inda kowane gaban tebur abubuwan motsa bakine yayinda ango da amarya bakinsu yakasa rufuwa don murna mawak'a ko sai k'ara baza fasaharsu sukeyi don kwason rabonsu, abokan ango kuwa basuyi k'asa a gwiwa ba wurin yimasu ruwan nairori

Tasowa yayi cikin isa datak'ama najin cewar shi wani ne yayinda 'yan mata suka zuba mashi namujiya ko Allah yasa a dace Wanda shi baisanma sunayi ba bandir d'in 'yan 1k yabud'e yanama amarya da ango yayyafinsu batare da yaji wani d'ar ba nayadda yaketa k'ara farka wasu bandir d'in take holl d'in yad'auki sowa mawak'a ko sai k'ara bud'e baki suke suna kod'ashi yayinda yakejin kanshi nak'ara fasuwa dukda shi ba mutum bane Maison nuna yanadashi

Duk wannan shagali da ake baisa ta d'ago fuskartaba asalima tunaninta yatafi wurin Ummarta data bari ita d'aya kasancewar ita kad'aice gareta shiyasa duk abinda ake Allah Allah take agama ta tafi wurin mahaifiyarta, don ma bikin yazarmata dole dabata kai wannan lokacin ba, to Amma Maryama Usman ta wuce komai wurinta shiyasa dukda banbancin dake tsakaninsu na ita talakace likis sab'anin Maryama diyar masu dashi wanda a tarayarsu bata tab'a nuna mata wani banbanci ba ko kyamatar talaucin da suke da shi ba asalima tana k'ara shige mata don tasaki jiki da'ita da nuna mata bawani banbanci tsakin talaka da maik'udi

Nazarinta ne yakatse da taji ana kiran sunanta a matsayinta na babbar aminiyar amarya datazo ta rufe taro da addu'a

Batare da b'ata lokaci ba ta tashi cikin kwarin gwiwa ta amshi bututun maganar tarufe taron, tare da yin addu'u'eh na zaman lafiya ga ma auratan da fatan nuna na 'yan baya haka

Ganin har k'arfe shadaya na dare ta wuce yasa tak'ara shiga cikin damuwa, Amarya Maryama ce tak'araso inda ta hangota tsaye tace "sorry Umma ko?

D'agama mata Kai kawai tayi, itakuwa Maryama ganin 'yan miskilanci nata nakusa yasa taja hannunta zuwa wajen mota, back seat ta bud'e mata tare da had'a hannayenta wuri guda alamar tayi hak'uri tana zuwa, bata jira taji mizataceba ta rufe mata k'ofar motar sanan ta wuce wajen angon nata, sai da suka gama bankwana da mutane sannan suka kama hanya

Batare da d'aukar lokaci ba sukayi parking a k'ofar wani d'an akurkin gida dake unguwar mabera, sauke ajiyar zuciya tayi tare da fad'in Alhamdulillah, kallonsu tayi cikin salonta Wanda naturally haka Allah yayita tace "saida safe" tare da rufe k'ofar motar sannan ta wuce cikin gidan

kallon juna sukayi suka saki murmushi lokaci d'aya,sannan yaja motor suka wuce unguwar Sama road, bakin wani tangamemen gida yayi parking wanda fadar tsaruwasa bata lokaci ne, bata d'auki wani dogon lokaci ba sukayi sallama ta shige gida

Washe gari dubun jama'a suka shaida d'aurin auren Maryama Usman Canji da Angonta Muhammed Mutawalkil kan sadaki Naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba, daga haka aka cigaba da shagulgulan biki har aka sada amarya d'akinta dake cikin gwiwa lowcost

Tafe take cikin wani irin yanayi Wanda dukda irin zafin rannan da ake na garin sokoto baisa tajita ba itadai babban burinta taga tak'arasa gidan kawun nata Wanda basu da wata tazara tsakanin gidansu danashi, tare da addu'ar Allah yasa wannan Karon yataimaka masu da abinda zata saima Ummartata magani

Kasancewarshi mutum ne mai d'an banzan mak'o Wanda yana dashi amma bai iya taimakon kowa hatta iyalanshi basu cika ammafana dasamunshi ba, shi karan kanshi yana buk'atar abubuwa amma gani yake da yatab'a dukiyar komai na iya k'arewa a cewarshi

Sallama tayi, Amaryarshi da yayi kwanan nan ce ta amsa tare da fad'in " *Azraa* ce to bismilla wuccike"

Bayan gaishe gaishe tare da tambayar ya Ummarta take?

Murmushi ne tasaki wanda iyakarshi lebenta tace "lafiya, ko kawu na nan kuwa?

"yanzun nan yafita"
cewar Adama matar kawu, kallonta tayi da daradaran idonta tace "dama Umma ce ta aikoni don Allah inyadawo a fad'amashi tanason ganinshi"

Daga haka ta gyara zaman hijabinta Tamik'e da zummar tafiya, Adama ta takalleta tace "badai tafiya zaki ba, bazaki bari yadawoba tunda banisa yayi ba"

"bakomai Aunty sauri nake nabarta ita kad'ai kuma yau jikin nata sai a hankali shiyasa" tak'arasa maganar cike da k'osawa kasantuwarta bamai son yawan magana bace,daga haka tayi sallama da su ta wuce gida

Dai-dai k'ofar gidansu taga yayi parking d'in motarshi k'irar Anaconda black wani siririn tsaki tasaki tare da furta iska na wahalar da mai kayan kara, d'an anace sarkin naci tare da k'arasawa inda yake

Murmurnshi ya fad'ad'a tare da cewa "Azraah sarauniyar mata ko a cikin dubu daban kike"

Kallonshi yayi tace "Rasheed yakake" daga haka ta wuce cikin gida batare da taji amsarshi ba, girgiza kai kawai yayi don yasan halin mutuniyar tashi

yaro yasa yace ya gayama Umma Rasheed ne yana son shigowa ya gaisheta, bayan fitowar yaron yace tace yashiga

"Umma barka da gida, yak'arfin jikin? "jiki Alhamdulillahi Rasheedu ya wurin su hajiyarka ka"

"suna lafiya tama ce agaisheki" "ina amsawa" a fakaice yakalli sashen da mutuniyar tashi take kafin yasake kai dubanshi ga Umma yace

"Umma ko zamuje Asibiti naga kwanakin nan jikin ya matsa maki"

"a'a Rasheedu basai munje ba, dama inason muyi wata magana dakai kan wannan hidimar da Kake mana yayi yawa"

Nunfasawa yayi yace "Umma mudai albarkarku mukeso da kuma addu'ar neman bud'i na alkhari"

"to Allah yasa albarka cikin rayuwarku" "ameen" daga haka suka cigaba da firarsu wanda Azraa najinsu amma batasa masu baki ba hasalima bazaka tab'a cewa tana wurin ba, Haka yagama firarshi da Umma ya wuce gida

Yau Monday Wanda ko bature natsoronta, hakan takasance da Azraa tana tasauri ta tafi skull wanda har lokaci yashige tana neman makara, kasancewar ta tsaya yima Ummarta wasu 'yan aikace aikace

"Umma na shirya zantafi" "Allah yabada sa'a Azraa Allah yatsare" "Ameen Ummata"

Usman Danfodiyo University sokoto, zaune take gaban department d'insu kasancewar yau lecturer d'in yasamu tsaikon zuwa saboda wani uzuri

Kamar daga sama taga sauran yan class d'insu nata sauri wurin shiga aji, a hanzarce itama tamara masu baya

bayan kamar mitina biyar da shigarshi ya gabatar dakanshi amatsayin Wanda zai d'aukesu darasin turanci

"Mr Aabid Abdallah By Name" sannan ya d'aura da bayason in yashigo wani d'alibi ya shiga... Banda amsa waya kowace iri ce komin amfaninta ga Wanda aka kira....dadai sauran tsaurori irin na lecturers sannan ya cigaba da gabatar da ginshik'in abinda yatarasu

sauran 'yan matan class ba bayanin dayake suke saurare ba Illah shi dasuke kallo dan bak'aramin tafiya yayi da imaninsu ba

60 Minutes ya d'auka yana sharara masu darasi wanda yanayi kamar yana busa sarewa don dad'in muryarshi Wanda hakan yasa wasu suka k'ara ingiza kansu cikin wutar sonshi

Daga haka suka cigaba da d'aukar darursansu na wannann ranan Wanda ya d'aukesu har zuwa k'arfe biyar na yammacin ranan

Agajiye tadawo likis kasancewar tana azumtar ranan.......

_*Mrs Abdul sule*_
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

© *HALIMA MK*


🌈 *KAINUWA WRITERS ASSO*✍🏻

*SADAUKARWA GA :*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH {KE ALHERI CE}*

*PAGE 2*

*B*ayan ta idar da sallah magrib tajawo cooler da tazuba taliyar hausarta a ciki tahau ci bakaukautawa kasancewar yau azumin ba k'aramin jinshi tayi ba sakamakon ranan da akeyi, bayan kammala cin abincin nata ne Ummarta ta d'aga labulen d'akin tare da cewa

"Azraa ansha ruwa lafiya" "lafiya lau Ummana" daga haka Umma tasaki labulen d'akin takoma tsakar gida tacigaba da laziminta har akayi kiran sallar ishsha'e tayi sallah, Azraa fitowa tayi suka cigaba da firarsu har zuwa lokaci kwanciya bacci yayi suka shige d'aki suka kwanta

Ringing d'in wayarta ne yatasheta daga bacci, ganin maikiran yasa ta zabura ta sauko daga kan 'yar yololuwar katifar datake kwance ba Inda idonta yasauka sai kan wata tsohuwar agogon dake manne jikin bango d'akin k'ara zaro ido tayi dama gasu tubarkalla ta d'aga wayar tace

"nashiga ukku Maryama badai nayi missing test d'inba"

Daga can b'angaren Maryama tace "kwaya kikasha ne har kamar wannan lokacin baki fito ba, ko nida nake amarsu nafito na shigo skull bareke gwauruwa"

"to suda sarkin surutu kincika mani kunne da hayaniya baki gayamani musabbabin kiran ba"

"au haka zaki fad'a, yayi kyau" tare da datse kiran saurin1 fito tayi tsakar gida taga Umma nata aikace alkacenta, "Umma ya akai baki tashe niba gashi har lokaci yashige haka"....... Na d'auka yau baku darasi ganin har shabiyu takusa baki tashi ba shiyasa na kyaleki"

Zanb'uro baki tayi tace "haba Umma Aida kintashe ni" daga haka ta wuce ma kewayi, bata d'auki mitina ishirin ba tafito cikin shirinta na zuwa makaranta, agurguje tayima ummar ta tabankwana ta wuce

Koda ta isa Allah yasa basukai ga farawa ba,batayi zaman dak'ik'a ka d'anba suka fara test d'in

Bayan sunfito ne Mr Aabid ya aiko masu cewar su jirashi zaibasu darasi, bayan kamar mitina ishirin ya shugo ajin nasu suka cigaba da d'aukar darasi, kamar koyaushe hankalin 'yanmata class d'in nakanshi wanda a zahirin gaskiya ba abinda yake koyar dasu bane suke saurare Illah baiwar da Allah yayi mashi nakyau da haiba wanda yake k'ara ingizasu akan wutar sonshi, wanda shi baimasan da zaman sunayi ba

Kallonsu yake yana nazarin kowane d'alibi, a daidai lokacin da wayar Azraa tad'auki tsuwa alamar shigowar Kira, saitin dayaji ringing d'in wayar yakalla a yayinda ita kuma Azraa nata k'ok'arin datse kiran "get out" abinda kawai ya furta mata tare da maida akalar darasin nashi zuwa test wanda dayawa 'yan ajin sun tsorata kasancewar basu shiryama yinta a wannan lokacin ba, take Maryama wata irin zufa taketo mata data tuna da cewar yakori Azraa wanda ballailai bane yabartar tashigo zarginta ne kuwa yatabbata don jin yadda Azraa ke rok'onshi da yabarta ta shigo amma yayi shuru hakan yasa ta koma bakin inuwar umbrella tazauna ta zubama sarautar Allah ido,mintina 15 kawai yabasu, shugaban ajin ne yayi ma umarni da yatattara mashi takardun kowa Wanda suka zana gwajin

Bayan angama tattarawa yasashi yakaimashi ofis d'inshi, kallo d'aya yayimata lokacin da zai wuce ofis tare da sakin wani siririn tsaki,ko inda zaiwuce bata kallaba bare tasan da wanzuwarshi a wurin dukda lokacin da zai wuce taji tsakin da yasaki

Maryama ce tadafa kafad'arta tace "sorry my Azraa"

"Bakomi aminiyar arzik'i haka Allah yaso" daga haka Maryama taje hannunta suka wuce masallaci

*Azraa* tilon diya ga Malam hasheemu da Hauwa, wanda sukayi aure shekara biyar da suka wuce, saida suka shafe tsawon shekara 4 da aure sannan Allah yabasu haihuwar Azraa wanda daga kanta basu sake haihuwa ba, Malama Hasheemu haifanfan garin tanbuwal ne ta jihar sokoto,shi kad'ai ne ga mahaifansa, Hauwa itama 'yar tanbuwal ce wanda su ukku mahaifata suka haifa Saminu(kawu) Hauwa da kuma Yunusa, cirani ne yakawosu cikin garin sokoto, inda Malam Hasheemu yake sana'ar gasa kaji a gawan nama, itama Hauwa tacigaba da yima wata Hajiya aiki na wanke wanke a nan cikin mabera watau mahaifiyar Rasheed shi kuma Malam Hasheemu yana masu gadi wanda suke zaune cikin boysquaters din gidan

A haka suka cigaba da gudanar da rayuwarsu har Allah yahorema Malam Hasheemu yasayi wani d'ankaramin gida inda itama Azraa yasa ta makarantar boko da arabi

kwanci tashi asarar mai rai hargashi Azraa taga makarantar sakandire cikin rufin Asirin Allah a yayinda sakamakon jarabawar Jam data zana tafito da makin da akeso shine yayi sanadiyar shigarta Usman danfodiyo University, inda suka bata fannin mass com, Batayi wata ukku da shigaba Allah ya dauki ran mahaifinta Malam Hasheemu ta sanadiyar mashin da yakad'eshi Wanda take a lokacin ya amsa kiran mahalilcinshi

Bakaramin tashin hankali su Hauwa da Azraa suka shiga wanda yayi sanadiyar kamuwar Hauwa da hawan jini, ta dalilin hakan yasa tabar aiki gidansu Rasheed wanda Hajiyarsu Rasheed d'in ta temaketa da jari da haka suka cigaba da gudanar da al'amurrar rayuwarsu na yau da kullum, wanna kenan..........

Bayan sunfito daga masallaci ne Maryama ta Kalli Azraa tace "ko muje inrakaki kibashi hakuri kinsan abokin MM Ne"

Yatsina fuska tayi tace "share kawai Maryama, banajin zan'iya bashi hakuri"

"a'a Azraa kidaure dai muje musa meshi kawai mubashi Hak'uri" shuru kawai tayi hakan yasa Maryama ta gane cewar ta amince

Koda suka isa ofis din nashi yana waya saida suka d'auki kamar mitina goma kafin ya datse kiran, "Hajiya Maryama ya maigidan" cewar Mr Aabid

"lafiya lau"....."badai wata matsala ko" k'ara sadda kanta k'asa tayi tace "dama Azraa narako don tabaka hak'uri kan abinda yafaru d'azu a aji"

"ita wanda kika rako bata da baki ne" Maryama ce tak'ara zunkud'ar Azraa karo na biyu natayi magana amma ta nuna kamar batasan tana yiba

"Tunda bata da baki Hajiya Maryama kuna iya tafiya" cike da mamaki sukaga Azraa ta bud'e k'ofar ofis d'in ta fita,gwiwartace tayi sanyi ganin abinda Azraa tayi yasa tabi bayanta batare da tak'ara cemai komi ba

Maryama ce tafe cikin danasanin rako Azraa wurin Mr Aabid............

*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

© *HALIMA MK*

🌈 *KAINUWA WRITERS ASSO*✍🏻

*SADAUKARWA GA :*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH* *{KE ALHERI CE}*

*GIDAN GANDU...... NAKI NE BIEBEE ISAH A DADE ANAYI SAI GASKIYA....... LALLAI KE ALHERI CE...... SAKONKI YA ISO GARENI πŸ’― ANATARE ILYSM😘*

*SA'ADATU ALIYU KABUGA WANNAN SHAFIN NAKI NE HALAK MALAK KIYANDA KIKESO DASHI MK TAMALLAKA MAKI SHI*

*PAGE 3*

*B*ayan fitarta daga ofis d'in direct wani wurin shak'atawa ta nufa dake cikin makarantar, jin yadda zuciyarta take mata tafasa ganin yadda duk wata doka da lecturer zaibayar tana k'ok'ari taga ta kiyaye bama shi kad'ai ba hatta dokokin da makarantar ta shinfid'a tana k'ok'arin taga takiyayesu don ta tserar da mutuncinta amma yau kuskuren rana wani na neman tozarta ta, Uwa Uba burin da taci kan karantun don tasamu taga sun dogara dashi ita da mahaifiyarta, ganin yadda take ta fad'i tashi akan karatun nata amma wani na neman maidata baya akan haka

Bayan tayima kanta wurin zama ne tajawo wayarta don taga waye ya kirata wanda ko sunan maikiran bata tsaya dubawa ba tayi k'ok'arin kashewa, k'utawa tayi don tunawa datayi koma waye yajaza mata salalon tsiya, dogon tsaki tasaki aranta tace Rasheed d'an anace tare da k'ara maida wayar cikin bag d'inta ganin shine ya haddasa mata rashin samun yin gwajin...

Dube dube takama ganin inda zata ga Azraa, amma Allah baisa tayi tozari da hakan ba, wani tunani ne yafad'o mata a rai, take ta maida akalar tafiyarta ta zuwa wurin shak'atawa na cikin makarantar don tasan bata wuce can, yalai ko hakan ya tabbata don hangota datayi, cikin sauri tak'arasa wurinta

"Azraa kin kyauta, inda nasan haka zakiyi mani Wallahi daban rakaki ba amma bakomi" cewar Maryama datayi maganar cikin tsantsan b'acin rai

"Oh My God Maryama minayi nace tunkafi ya fara nabashi hak'uri amma baiyi ba to hak'urin me zansake bashi akaro na biyu" wani irin kallo Maryama tabi Azraa dashi dake nuna kinkyauta sannan tace

"amma....... "look Maryama kinfa dameni da hayani" cewar Azraa tare da d'aukar bag d'inta tayi hanyar fita daga makarantar baki d'aya, kallon zakiyi abinda yafi haka Maryama ta bita dashi tare da jan k'afafuwanta dasuka yimata sanyi ta juya aji

Daidai get d'in makarantar suka had'u da Rasheed dayake ta k'ok'arin tura hancin motarshi don shigowa cikin makarantar, saurin b'oyewa tayi amma ina tuni d'an anacen nata ya hangota, parking d'inshi ya gyara yakashe motar yafito domin k'arasawa inda take

"Allah yataimaki Azraa sarauniyar mata" tare da jifarta da wani irin murmurshi mai nuna tsantsar so ga abinda kake muradi, k'are had'a fuska tayi tana k'ok'arin rab'ashi ta wuce batare da tace mai k'ala ba, ganin hakan yasa yace

"Allah yasa banine sanadiyar d'aukewar annurin fuskar nan ba ma abociyar kyau da haiba wanda haskenta tamkar wata d'an daren shabiyu"

Ta bud'e baki da niyyar tayi magana idanuwanta suka sauka kan na Mr Aabid wanda yake ta jifarta da harara wanda tarasa kota mecece, k'ara speed d'in motarshi yayi yabar cikin school d'in batare da yak'ara duban inda suke ba

Rasheed ne ya k'ara sassautar da muryarshi yace "pls Azraa muje nasaukeki gida koma miye saimuyi solving d'inshi a gida zaifiye mana mutunchi damu tsaya nan muna magana" kaii dubanta tayi gareshi daniyar yab'amai maganar da duk tazo bakinta kasancewar shine yasata a wannan halin.....amma kash saitaga yayi mata kwarjinin da baza iya cimai mutunci ba, tuna alherin iyayenshi garesu yasa tasassauta fuskarta, bugu da k'ari shima Rasheed baiyi k'asa a gwiwa ba wurin ganin yana nuna kulawarshi garesu ita da mahaifiyarta dukda ba'asan ran Umma yake hidinta masu ba don ita macace wanda ta iya hak'uri dasamun da Allah yabata komai k'ankantarshi batare da tayi kwad'ayin nawani ba

Bakin motar taja tunga ta tsaya ganin haka yasa Rasheed saurin bud'e mata motar, tafe suke shuru ba wanda yace komai basuyi nisa da makarantar ba sosai taga motar Mr Aabid yayi parking yatsaya kamar yana jiran wani abu, daidai zasu wuce yak'ara jifanta da wata irin muguwar harara wanda takasa tantace kota micece kawar da kanta tayi tamaida dubanta zuwa ga titi, basuyi nisan rabin kilomita d'aya ba taga ya wuce da wani irin mugun guda kamar wanda ke shirin barin duniyar

Rasheed ne yajuyo yakalleta yace wancan guy fa" tare da d'aure fuska kamar baitab'a dariya ba....

"wake nan?"...... "bansani ba" cigaba yayi da driving d'inshi kamar baisan tana cikin motarba,wanda shurun nashi shiyafi yimata dad'i kan ya isheta da surutunshi marar makama don kwakawlwarta tana da buk'atar nazari kan abubuwa da dama

Tafiyar mitina shabiyar ce takawosu gida, batajira cewarshi ba takama kiciniyar bud'e k'ofar motar amma ina tuni yariga da yayima motar key tadaga wurin mazauninshi, sund'auki kusan minti biyar batare da wani yace wani abuba hasalima kowa da irin tunanin dayake cikin ranshi, shine yakawar da shurun ta hanyar cewa

"mik'e tsakaninki da wancan garan malamin naku" banza tayi mashi don bata da amsar dazata bashi "Azraa dake fa nake" yayi maganar cikin d'aga murya

"miya haka katan bayeshi"........"au haka zaki fad'a"

"kaga malam bude' mani k'ofa inada abinyi" cire motar yayi daga lock, ganin hakan yasa tafice mai amota tashige gida ,girgiza kai yayi yace

" *Azraa* Insha Allahu baki da mijin da yawuce ni don tuni nagano take takenki akaina zanjure duk wani k'alubale dazan fuskanta a kanki" daga kai ayar zancen nasa yaja mota ya wuce gida.......

"Waikai lafiyarka tunda kashigo kake tayima mutane bak'in rai" cewar mahaifiyar Aabid

"Normal Hajiya ba wani abu"....."Allah yasa, ka koje wurin yarinyar da Alhaji yace kuje ku daidaita kanku kuwa?" Take hoton wani abu yafad'o mashi arai "Hajiya zanje zuwa anjima"

"da dai yafi maka don wannan karon baka da wani uzuri dazaka kawoma mutane" tashi yayi ya wuce b'angaranshi batare da ya tofa wata kalma daga bakinshi

Harara takarashi da'ita tace "Aabid Abdallah kenan wannan matarka taga takanta kan d'an banzan miskilancinka" tare da cigaba da abinda take

Shigarshi d'aki yayi kwance kan gado ya lumshe idonshi kamar mai bacci

*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

© *HALIMA MK*

🌈 *KAINUWA WRITERS ASSO*✍🏻

*SADAUKARWA GA*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH* *{KE ALHERI CE}*

*KUSKURE*
*_kamar yadda nace Azrah nakarantar mass com a dan 4dio, Alhali dan 4dio basa course d'in sai Ummaru Ali Shinkafi kadai ne suke course din mass com a sokoto afuwan πŸ‘πŸ» zamu barshi akan tana karanta harshen turanci (english) sannan kuma akwai inda nace Azraa da Rasheed tafiyar mintina shabiyar takawosu daga dan 4dio zuwa mabera to nan ma ina neman afuwa saboda daga dan 4dio zuwa mabera tafiyar takusan sa'a guda ce normal driving dafatan mazauna garin sokoto masu bin labarin zasuyi mani afuwa_*

*PAGE 4*

*Y*afi tsawon 20 minutes a haka idonshi lumshe alhali ba bacci yake ba yanata tunanin zuci, wani b'angare ne na zuciyarshi yake k'ara tunatar dashi to miye na damuwa dan ankirata a waya, ko ko don kaganta da wani ne zaisa kajefa kanka cikin damuwa alhali kasan babu wani abu tsakaninka da'ita hasalima koda kuka had'u wurin bikin MM ba wata magana data shiga tsakaninku balle har kayi tunanin ko akwai wata mahimmiyar magana tsakaninku wanda zaka damu kanka haka, da wannan tunanin ne yasamu kuzarin damar tashi yarage kayan jikinshi, toilet yashiga yasakanma kanshi ruwa, bayan yafito daga wanka saida ya share kusan 15 minute yana lailaye fatarshi da mayuka masu kyau datsada wanda ke k'ara nuna kyawun jikinshi da kuma b'oye shekarunsa

Closet d'inshi ya bud'e wanda take shak'e da kaya nau'o'eh daban daban wanda suka danganci k'ananan kaya, manya riguna, suit, dadai sauran nau'eh kaya namaza kowanensu a tsare yake cikin ma'adani aje kayan

Wani black trouser ne yad'auko da red shirt, bayan yakamalla saka kayan ne wanda bak'aramin amsar fatar jikinshi sukayi ba kasancewarshi fari sannan yabi jikinshi da wani lallausan turare mai sanyi k'amshi, d'aukar key d'in motarshi da wayoyinshi yayi ya fito counpoud d'in gida, motarshi yayi ma key tare da dannama maigadi horn, take ya wangale mashi babba k'ofar, hannu kawai yad'aga mashi ya fice gidan

Unguwar Arkilla yatasanmawa don cika umarnin iyayenshi, bayan ya gaisa da maigadin gidan ne ya umurceshi da yayi mashi sallamah da Saleemah inta nan

Bayan fitowar getman d'in ne yace mashi yashiga palour bak'i tana zuwa, daga haka yakoma bakin aikinshi

Tafiya yake cike da natsuwa har zuwa masaukin bak'in, baiyi zaman mintina goma ba Saleemah tafito cikin ado da yauk'i, zama tayi kujerar dake kallon tashi tace "barka da yammaci"

"barka" cawar Aabid tare dazaro wayarshi daga cikin aljihun wandonshi yakama danne dannane, d'akin ne ya d'auki shuru nakusan mintina shabiyar don kafin lokacinma har angabatar mashi da abin motsa baki wanda ko kallonsu baiba, "inbaki da abincewa nizantafi" Aabid ne yayi furucin tare da mik'ewa yayi hanyar barin palourn

Cikatayi da mamakinshi na wannan wane irin sabon salone yin noma da lauje, ganin dagaske tafiya zai yasa tace "Allah ya kiyaye" daga haka ya ida ficewa daga palourn batare da yajuyo yace mata Ameen ba

Zamata tayi rajaf bisa kujerar tace "oh ni, anya su Daddy ba kuskure suke san yiba akan wannan auren da wancan baud'ad'en mutunan wanda baka gane ina ya dosa, k'ara zurfafa kanta tayi cikin tunani na gano kotana da wani aibu wanda za'ace bata cancanci a sota ba hasalima ita tasan tana dakyau da diri wanda akeson mace dashi kuma tasan bata da wani mugun hali ko kuma rawar kai na 'yan matan wannan k'arnin da za'ace bata cancaci tazama mata gakowane kamilin namiji ba, ganin zataba kanta ciwon kaine yasa ta kwashi halintun jikinta ta wuce cikin gida...........

Koda yabar gidan su Saleemah baizame ko inaba sai Zabira Mall don da akwaI abinda yakeson dubawa a wurin......

Azraa ce zaune ita da Ummarta suna fira kamar kodayaushe, Umma ce takalleta tace "Niko Azraa mikika yanke kan maganarku da Rasheedu don jiya Hajiyarshi tazo tasameni akan maganar yanason ayi mashi iso can tambuwal wurin dangin mahaifinki dan a tsayar masu da Magana"

Nisawa tayi tace "Umma da anbari nan gaba kad'an"......."wane gaba kad'an kuma, ai mutuncin mace d'akin mijinta, kuma ma yayi alk'awarin bazai hanaki karatunki ba to minene nadamuwar kice sai wani lokaci"

"to Umma Allah yazab'a mana abinda yafi zama alkhairi" "ameen, yanzu zantura yaya saminu yaje yafad'a 'Yan uwan mahaifin naki don atsaida masu magana" daga haka suka cigaba da firarsu

Bayan kwana biyu Tafito zata makaranta suka had'u da Rasheed k'ofar gida kallonta yayi yace "morning my princesss"

"morning" cewar Azraa "oyo muje nasaukeki yau Munyi latti"

"kabarshi kawai ka wuce Ofis na hau agwagwa da buje (napep)"

"muje kawai zansaukeki don banason kowa na gane mani fuskar mata don nan gabama nikab zaki rink'a sawa"

Naturally habit d'inta tayi mashi watau yatsina fuska tare da yimashi kallon kanka akeji tayi gaba wurin mota, bud'e mata k'ofar motar yayi sannan yazagaya yashiga mazaunin direba, tafiyar minti hamsince takawosu cikin makarantar, batare da b'ata lokaciba tabud'e k'ofar motar zata fita handbag d'inta ce yayi saurin rik'ewa, ganin hakan yasa tasakarmashi bandir d'in 500 yasa mata ciki, kallonshi tayi tace

"Ya Rasheed kadubi girman Allah kacire kud'in nan wallahi na koma ma Umma dasu Allah kad'ai yasan wane irin abu zaitai mani akansu"

"aibance baki nayi ba ki ajeman Innazo da daddare zan amsa" ganin karsu tsaya jayayya yasa ta amshi jikkatta gashi dama sunriga dasunyi latti, daidai tafiddo k'afarta daga cikin motar ne shikuma Mr Aabid yayi parking d'in tashi kusa datasu, kai kallonshi yayi wurin motar dake pake kusa datashi, ganin wadda ke k'ok'arin fitowa cikin motar yasa yaji gaba d'aya wutarshi ta d'auke jiyake kamar and'auko dutsen kwatarkwashi an azamai a k'irji jin yadda yayi mashi nauyi, kallon dayawatsa matane yasa ta maida k'afafunta cikin motar "yadai" cewar Rasheed dayaga tamaido k'afarta cikin motar

"daidai, akwai abinda zanduba ne" Murmushi yak'e yasaki domin sarai yasan dalilin dayasa tace haka don tunkafin yayi parking ya hango motarshi ta madubi

Tada motar yayi ganin haka takalleshi tace "ya haka kuma"...."na'aza yau kinfasa d'aukar darasi ganin kintsorata da ganin wancan garan saurayin naki don yaganki dani" yak'arasa maganar cike da tsananin kishi

"wallahi ya Rasheed bawani abu dake tsakanina dashi hasalima ko magana bata tab'a shiga tsakanina dashi ba"

"Azraa kenan rufo k'ofar motar" rufewa tayi batare da wata gardama, fisgar motar yayi don har tana buge kanta da dashbord, a 180 yafice daga cikin makarantar

Aza kanshi yayi saman sitiyarin motar a yayinda yaji duniyar gaba d'aya tad'aukemai yadauki sukan miti biyar cikin wannan halin wanda yarasa wai meke shirin faruwa dashi kan wacca kucakar yarinyar wanda baya tunanin tama fara jinin haila gashi zuciyarshi na neman ta haddasa maisa abinda bazai tab'a yuwuwa ba, don ga yadda yake jin kanshi yasan ba k'arar mace zata iya d'aukar lalurarshi, ganin tunanin bamafita ne gareshi ba yasa ya wuce ofis.......

*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

® *HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH {KE ALHERI CE}*

*PAGE 5*

*W*ani irin mugun gudu yake dasu wanda bak'aramin tsorata tayi ba shuru dai kawai tayi tana ta salati cikin ranta dan tariga da ta sadak'as yau kila kwananta sunk'are harta fara tunanin yau zasu had'u da dagus d'inta a k'iyama, wani wawan birki yataka wanda yasa tayi saurin d'aga kanta dake sadde k'asa don har wata siririyar rihi tasaki wanda Allah yaso baijita ba

Ganin inda yakawota ne yasa tai saurin bud'e k'ofar motar tashige gida da sauri batare da tajira maizaice mata ba

Askwane ta d'auki buta sai toilet don gudun da yayi dasu bak'aramin yamutsa mata ciki yayi ba, Umma dake zaune tsakar gida binta kawai tayi da kallo

Bayan tafito ne Umma tace "ya zaki shigo gida basallama gashi kinshugo kamar wadda aka biyo" ajeyi butar tayi inda suke ajewa ta matsa kusa da Umma sosai tace "Umma yau naga tashin hankali"

"tashin hankali kuma Azraa! Meyafaru injin dai bakoroki sukayi daga makarantar ba"

"ko d'aya Umma Rasheed ne yaso yayi dibar karan mahaukaciya dani, daga zai sauke ni makaranta yaga wani malamin mu na hararata shike nan yace ai saurayinane" tsoki Umma tasaki tace

"to shine zaki shigo gida a hargitse, to shimma dakika dawo yau bakwa karatu ne?"

"munayi, shine yamaido ni kuma ya wuce wurin aiki, yanzu haka ma ni kaina ke ciwo zuwa zanyi inkwanta" daga haka ta wuce d'aki

Girgiza kai Umma tayi sannan ta cigaba da girkin da ta d'aura

Jin k'arar shigowar sak'on ne a wayarta yasa ta jawo hand bag d'inta wanda har kud'in da Rasheed yabata suna fad'owa batabi takansuba ta fara duba sak'on kamar haka _Azraa mutunanki Mr Aabid test yake mana ina kika tsaya harkamar yanzu baki k'araso ba_ sak'on da yashigo wayarta kenan daga Maryama

Batare da wani jinkiri ba tamayar mata da amsa kamar haka _kyale bak'in mugu_

Daga haka tarufe wayar gaba d'aya don kar adameta, to sarauniya inkin gama baccin sai ki fito in aikeki gidan hajiyarsu Rasheedu, idon Umma ne yasauka kan kud'in dake zube bisa katifa

"Azraa mai nake gani nan bisa katifarki"

"Umma Rasheed ne yabani na aje masa kafin zuwa anjima yazo yakarb'a" tak'arasa maganar cikin dana sanin barin kud'in har Umma ta gani

"babban fatana Allah yasa Azraa barok'o kika fara ba, don bana fatan kisama ranki son abin duniya dukda kintaso cikin talauci, kina ganin ko wannan hidimar dayake mana nakaiki makaranta da sauransu ba'asan raina yake yinsu ba don dai yacije da abarshi yayi shiyasa nakyaleshi ganin yana da hankali da kame kai yasa nabarshi kuna fita tare wanda duk lokacin dazaku fita nikad'ai nasan yanakeji barin ku danai kun keb'anta"

"Umma bana fata rok'o yashiga cikin al'amurrar rayuwata koda kuwa zamu kwana bamuci ba, bare ga mutumin dayake bakin k'ok'arinshi akanmu"

"nadai gaya maki, kuma kiyi k'ok'ari ki maida mai kud'inshi karki yadda kibashi fuskar dazai ce yabarmaki su kinji nagaya maki, yanzu kitashi kikaiwa Hajiyarshi dambun zogale da nayi"

K'atuwar abayar tace ta d'auko har k'asa wanda dama shigarta kenan tasa abaya har k'asa wanda da wuya ma kaga kalar kayan dake jikinta saboda girman hijabin fitowa tayi tsakar gida tace "Umma dambun ne a cikin wannan cooler?"...." eh kiyi sauri kidawo karki dad'e kigaisheta"

Koda ta bud'e k'aramar k'ofar get d'in gida taga motarshi na nan a parking space cikaitai da mamaki na mai yahanashi zuwa wurin aiki bayan da ya ajeta dazu kuma ma tasan wannan lokacin bai isa ace yatashi daga ofis ba, yatsina fuska tayi ta k'arasa shiga palourn gidan, bayan tayi sallama har sau ukku taji shuru yasa tashiga cikin palourn, kwance ta iskeshi bisa sofa yarufe idonshi, Aisha ce k'anwarshi ta fito d'aya daga cikin d'akunan dake palourn "oyoyo Aunty Azraa" tare da karb'ar cooler dake hannun Azraa cewar Aisha

Murmurshi tayi mata tace "yau ya akayi bakije school ba"

"kedai bari Aunty Azraa natshi da jarabawar ciwon ciki shiyasa Ummi tace karnaje"

Wata tsawa Rasheed yadakama Aisha natabar palourn wanda su a zatonsu sun aza bacci yake ganin idonshi rufe, kama hannun Azraa tayi da zummar su shiga d'aki amma suka tsinci muryashi na cewa

"Azraa kisameni gadern yanzu" tare da mik'ewa yabar palourn, Aisha ce tace "tundazu yake ta wannan fad'an don bana ma tunanin yau ko ofis yaje" Azraa shuru tayi don tasan kwanan zance, hanyar dazata sadata da gadern d'in gidan ta nufa

zaune ta iskeshi bisa plastic chair, "ya Rasheed gani" kujerar dake kusa dashi ya nuna mata alamar ta zauna, batayi zaman mintina ukku ba yace

"tsawon wane lokaci ne kike tare da wancan garan malamin naku"

"banga nake tare dashi ba"......kallon karki d'auke ni sakarai yayi mata yace "Azraa duk wani take takenshi akanki nagane don haka abinda zanyi warning d'inki dashi shine wallahi karki kuskura inganki tare dashi, dan bazai yuwuba shekara da shekaru ina dokon sonki wani shege yazo rana d'aya yashigar mani gona, dan mafi akasarin malaman jami'a mayaudara ne burin su kawai su lalata yaran mutane subarsu"

"wai yaya Rasheed maike damunka, ko zargina kake ne akanshi wanda har rantsuwa nayi maka bakomai tsakani na dashi hasalima ko maganar fatar baki bamu tab'a yiba"

"bance ina zarginki ba, amma yanayin take takenshi ne kebani tsoro"

"ka kwantar da hankalinka Azraa takace har abada"

Wani k'ayatancen murmushi yasaki wanda tunda suke da'ita baitab'a jin wani kalami maidad'i daga gareta ba, wanda ita kuma tanayin maganar ne cikin k'arfin hali don harga Allah Rasheed baya d'aya daga cikin mazan datake so yazama miji gareta badan bashi da kyau ko wani mugun halin da za'ace bai cancanshi asoshi ba domin ko mutunen kirki ne hasali kyautatawarshi ga mabuk'a yasa take k'ara tursasa zuciyarta gareshi

Da haka suka cigaba da firarsu ta masoya wanda Azraa daurewa kawai take tana biye mashi......

_dan Allah kuyi hak'uri da wannan mura nake, naso yafi haka yawa_

*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA :*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEEH ISAH*

_*Alhamdulillah naji sauk'i .......*_



*PAGE 6* to 8

*M*r Aabid ko yinin rana yayi shi cikin wani irin k'unci da damuwa aranshi kuma yarasa miye musabbi abinda ke haddasa mashi shi, dan duk lokacin da wani zairab'eta ji yake kamar ana kwarara mai ruwan zafi a jiki gashi zuciyarshi takasa tantance mashi sone koko yanayin yadda take mu'amala da maza shike sashi cikin damuwa haka...

Bayan sati biyu manema amran Azraa sukaje can tambuwal wurin dangi mahaifinta wanda dama sunsan da maganar tun marigayi mahaifinta nada rai, saida sunce masu su basu lokaci zasu aiko masu duk yanda ake ciki, sunyi hakan ne dan suyi shawara da mahaifiyar yarinyar don suji miye nata tanajin akan bikin kasancewar ba wani k'arfi garesu ba kuma mahaifin nata bawani abu yabari ba sai gidan da sukeci wanda ita Azraa ta gajeshi, da sauran yan gonakin dayake dasu can tambuwal wanda yan uwan nashi suka ci gadonsu saboda suna da gadonshi tunda d'iya mace gareshi bayada namiji

Zaune suke cikin aji ita da Maryama suna firar duniya, Maryama ce takalli Azraa tace

"Amarya bakya laifi" daidai lokacin da Mr Aabid zai wuce tabayan ajinsu, jiyayi kamar murya Maryama ke fad'in wannan maganar, dammmm gabanshi ya fad'i sani cewa Maryama bata da wata k'awa da ta wuce wannan yarinyar 'yar girman kai, jin muryarta yayi data takatse mashi tunani, tana cewa ma Maryama

"anjima zanzo gidanki don akwai maganar da nakeso mutattauna"

"to shikenan sai kunzo, don nasan keda Mr Right d'in naki zaki zo" bata bata amsar abinda tace mata ba saima yatsina fuska tayi kamar koyaushe tace "k'arfe nawa zaki gida, dan yau ni bazan jira ya Rasheed ba sunje zamfara shida wani abokin aikinsu"

"ok bari in MM yazo saimu saukeki, yau banfito da motata ba"

Dakyal yatattaro sauran kuzarinshi yak'arasa wurin da yayi parking motarahi, zuciyarshi kuwa inba ya ga nanatamai kalmar Amarya ba abinda takeyi, yafi k'arfin mintina goma zaune cikin mota kafin yatada ta yafita daga cikin makarantar, wanda yana driving amma hankalinshi kwata kwata baya tare dashi, ikon Allah ne kawai yakawoshi gida

Basu k'ara zaman mintina 30 MM yak'araso suka wuce gida bayan sun aje Azraa gidansu dake mabera


Kallo d'aya Hajiyarsu Aabid tayi mashi tace "waikai Aabid muke damunka kwanan nan dan ina lura dakai wasu lokunta inka dawo daga wurin wannan aikin naka kaita wani b'ata fuska kamar wanda akayi ma bushura da wani mugun abu zaisa meka, gashi kai baka iya gayama mutane damuwarka balle ko shawara abaka saidai kayima mutane dumkum dakai"

"Hajiya nifa ba abinda ke damuna yanayin aikine kawai, kinsa ba abinda yafi caja kan mutum irin d'alibai musamman mata suna bamu matsala wallahi"

"yanzu naganoka kace gamma katar kayi, don bai yuwuwa daga koyama d'alibai sai adawo ana fushi, ni bawan nan ba yakuka k'are da Saleemah d'iyar aminin mahaifinka,kaga cikin satin nan muke saran dawowarshi daga tafiyar nan dayayi zuwa india kuma inyadawo zasu tsaida lokacin auran, gara asan mekuke ciki kai da yarinyar kafin azartar da hukunci"

"Hajiyarmu bansa hayaniya kaina ke ciwo zanje in kwanta inna tashi zamuyi maganar"

"au maganar tawace keda hayaniya, to amshi karaba" tare dayi mashi dakuwa da hannu alamar zagi, murmushi yayi ya wuce part d'inshi don ya ragye gajiyar dayakwaso

duniyar tunani yafad'a tare da k'ara nazarin firar Maryama da k'awarta, yana kuma k'ara maimaita kaimar amarya acikin aranshi, zumbur yatashi yace "its means aure kenan zaitai, baidai wannan zata auraba mai wuya kamar marik'in lema" haka yaciga da suruntunshi kamar wani zautacce, kallon sama yayi kamar mai neman mafita kafin yayi kuta yashige toilet

Azraa ce zaune ita da Ummarta kamar koda yaushe suna tattauna matsalar rayuwarsu da kuma ta wace hanya suke ganin zasu shawo kan matsalolin nasu na rayuwa, dan yanzu wannan zamanin tuni akayi watsi da zumunci, saikana dashi akeyi dakai dazaran wata jaraba tasameka, naka ne farkon wanda zasu gujeka saidai kawai fatan Allah yasa mudace domin muna cikin wani k'arni mai wuyar fassaruwa, Umma ce tace

"Azraa jiya baban ninki sun same ni akan maganar aurenki da Rasheedu na sunason a tsada masu lokacin biki, to ya kike ganin za'a b'uloma wannan al'amari kinga dai bamu ajeba bamu ba wani ajiya ba, kina ganin yadda muketa fad'i tashi kan abinda zamuci dasauran 'yan hidimomin rayuwar don ma Allah yahad'amu da mutanen kirki shiyasa koda yaushe nai sallah nake yima wad'annan bayin naka addu'a Rasheedu da Hajiyarshi dashi kanshi ubangayyar watau Alhaji Musa, Allah yabi wad'annan bayin naka da alkhairi"

"Ameen Umma" shuru ne yaratsa wurin na wasu 'yan dak'ik'ai, Umma ce takatse shurun ta hanyar kallon Azraa tace "kodai gidan nan zamu saida, Allah bashi inyaso bayan biki sai inkoma tambuwal dazama, don shine kad'ai mafita a garemu"

"a'a Umma wannan gidan shine babban rufin asirinmu, kuma ni banso ki koma tambuwal kibarni nan shiyasa tunfarko naso yabari har ingama karatuna nasamu aiki wanda ko yayane zamu samu inda zamu d'ora hannu, dukda dai aikin yazama wahala wannan lokacin sai wayasanka ko wakasani"

"kedai Allah yarufa mana asiri, don kuwa ana rayuwa mai wahala saidai bawa duk yanda ya risk'i kanshi ya godewa mahalilcinmu"

"to Umma Allah yakawo mana mafita ga dukkan al'amuranmu yakuma warwarema kowa matsalolin rayuwa, bari inje inshirya kinsan d'azu nasanar dake zanje gidan Maryama"

"to maza kishirya ga wasu 'yan kayan amfanin gida nan kitai mata dasu" daga haka firartasu tak'are wanda Azraa tashiga d'aki da takintsa yayinda Umma taciga da 'yan hidimominta natsakar gida

"Umma ina sak'on nakintsa" cewar Azraa dake fitowa daga cikin d'aki, bayan takarb'i sak'on ta tafi don samun abin hawa, mai agwagwa da buje (lol) tatsayar sai shiyyar gwiwa lowcost

"Assalamu alaikum" muryar Azraa data karad'e palourn, jin shurun yasa tayima kanta matsu gunni d'aya daga kujerar dake palourn, wayarta tad'auko daga cikin hand bag d'inta jin shugowar sak'o ganin Rasheed ne kesanar da'ita cewar sundawo, wayar tasake maidawa daga cikin jikkar batare data bashi amsa ba

Rungume da juna suka fito daga cikin d'akin baccinsu wanda hannunshi na zagaye da kugunta, ganin Azraa zaune a palourn yasa MM saurin sakin Maryama dake rungume jikinshi

"kice yau babbar aminiyarmu ce a gidan namu" cewar MM dake k'ok'arin kunna tv datayima palourn kawanya

Wani kallo Azraa tayima Maryama na cewar kudai baku da kunya duk abinda kukayi cikin d'aki bai eh shekuba sai kunzo palour ku ida, kafin ta dubu MM tace "aikodai"

"ina mutunan kotare kuke?"

"a'a, sunje wani aiki a zamfara, amma yace mani sunshigo gari yanzu"

"ok Allah yataimaka"...."ameen" Maryama ce tagabatar mata da abun motsa baki sannan suka cigaba da firarsu wanda MM ke samasu baki jefi-jefi, wayarshi ce tayi ringing d'auka yayi yace "Assalamu alaikum" daga can d'ayan b'angaren aka amsa, ok kawai yace yakatse kiran,tare da cema Maryama

"madam minti biyu ina da bak'o waje may be inba sauri yake ba zamu shigo"

"badamuwa mijina sirrina" cewar Maryama tare da jifarshi da wani shu'umin kallo wanda har saida yashafi sandar girmanshi kafin yasa kai ya wuce

"aina aza sai Maryama tahaihu kazo ganin d'a ko d'iya, irin wannan hali naka rashin san shiga cikin jama'a"

"naji fad'i ba'a tambayekaba" cewar Mr Aabid da yamik'a MM hannu don suyi musabaha,bayan sun gaisa ne MM yace mashi

"shiga zakayi ka kwashi girkin amarya, don yau kaida barin gidan nan sai Allah" tare da jan hannunshi suka Shige palourn, koda suka shiga suntarar da su Azraa basa ciki amma sunji motsinsu kitchen, MM ne yabisu cikin madafin sanwar ya umurci Maryama data kaima bak'on nashi ruwa

Faranti mai d'an fad'i ta d'auko tasa ruwan swan da lemun excotic guda da kofunan guda biyu,,,bayan fitatta Azraa ta tsinci kanta da fad'uwar gaba, hakanan taciga da aikin dasu ka fara

Jin kiran da Maryama kema ba kakkautawa yasa tayi saurin fitowa palour dan ko hijabinta bata tsaya d'auka ba

4 eyes sukayi da Mr Aabid wanda suka d'auki minta biyu batare da sun d'auke dubansu ga juna ba, Azraa ce tayi saurin dauke idonta akan nashi, kallon sashen da Maryama take tace

"miye kike mani wannan irin kiran" da hannu ta nuna mata bag d'inta tace "ana calling d'inki tundazu"

Wanda yaba Mr Aabid k'are mata kallo dani kaina mk sarkin rihota, masha Allah abinda baki na yafara furtawa kenan don ko Allah yayi halilta a wurin don bantab'a katari da tacire hijabi ba sai yau dan kullum cikin adana kanta take, Azraa irin kirar coca cola shape ce don Allah ya azurtata da yalwantacen kugu ga boobs d'inta masu d'aukar hankali da tarwatse natsuwar namijin da yayi arba dasu, ga dara-daran idanu abin tubarkalla, zamu iya kiran fatarta da chocolate calour, ga gashi daketa reto bayanta kasancewar Ita bama abociyar daura kallabi ba ce shine yabani damar k'arema gashin nata kallo, komai naji kinta yayi bakarya don in kana kallonta bakasan kadaina,

Sungumar bag d'inta tayi ta wuce kitchen, ganin kallon da Mr Aabid yabita dashi wanda take kallonshi ta gefen idonta, dogon tsoki Mr Aabid yabuga wanda har saida MM yace mashi "Lafiya"........

"hello Ya Rasheed"......"gani nan k'ofar gida inkin gama zancen naje gida Umma tace kina gidan Maryama "

Dafe kirji tayi tazaro ido don tasan yau ko jikin Ya Rasheed kunnuwa ne bazai tab'a yadda bada saninta Mr Aabid yazo gidan nan ba

"baibaki iznin kiyi magana ba shiyasa kikayi mani shuru"

"kayi hak'uri ya Rasheed gani nan fitowa" datsen kiran tayi, saurin sa hijabinta tayi ta d'auki bag d'in tayi hanyar palour, koda ta isa Maryama da MM basa ciki sai Mr Aabid daketa danna remote yana canja channels, ganin tana da niyyar barin palourn ne yasa yayi sauri tarar gabanta har suna shak'ar nunfashin juna, tagefen shi tayi niyyar bi ta wuce,saiji tayi yajawota har tana fad'a kirjinshin,wani irin abu sukaji a lokaci d'aya wanda yakewaye illahirin jikinsu yabi sak'o da lungu da jini ke kwaranya yayin da gangar jikinsu tarink'a amsar sakwani kala kala, sund'auki 4 minutes ahaka kafin yayi k'ok'arin zare jikinta danashi yace

"ban baki iznin tafiya ba" yayi maganar ciki gadara da nuna isa

"ban......ringing d'in wayarta ce ta hanata k'arasa abinda tayi niyyar fad'i

"Ya Rasheeeee.....bakinta ne yad'alla da hannunshi tare da amsar wayar yakashe kiran.................

*MRS ABDUL SULE*

🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS*✍🏻
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*WANNAN SHAFIN NAKU NE MA'ABOTA KARANTA LABARIN AZRAA.....*

*_Azraa Fan's Naji Dad'i Comment D'inku Na Last Page Dukda Real Maryama Usman ce (lol) Zata Ida Maku....._*

*PAGE 7*

*K'*ok'ari amsar wayar tayi daga hannunshi amma takasa, ganin karya k'ara had'a mata wani zafin yasa ta hak'ura takyaleshi, taku biyu tayi da zummar barin palourn taji ya ambaci sunanta " *Azraaaaaa*" wanda tunda take bata tab'ajin wani yafad'i sunanta dai-dai ba kamar yadda Mr Aabid yafad'i ta kumayi mamakin dama yasan sunanta, juyowa tayi tamik'a mashi hannu don a tunaninta ko wayar zaibata, saima gani tayi yasaka wayar cikin aljihu yakoma bisa sofa ya cigaba da kallonshi

Barin palourn tayi da sauri don tasan Rasheed nacan ya cika fam kamar filawar da akayima b'arin yis, yale kuwa don ta iskeshi tsaye bakin mota ya kurama hanyar fitowa daga gidan ido, wani matsiyacin kallo ne ya wurga mata sannan ya bud'e murfin motar yashiga ciki, zaga yowa tayi wurin mazaunin mai zaman banza (gaba) tabude murfin motar tashiga

Zaman kusan 8 minutes sukayi ba wanda yace k'ala, wanda baya ga huci ba abinda Rasheed keyi, ganin inzasu shekara a haka baza tab'a iya fara yimashi magana ba yasa yace

"kingama soyayyar keda saurayin naki mu wuce gida? koko shi zaimaidake don nasan shiya kawo ki nan gidan don kuji dad'in sakewa"

"Ya Rasheed waikai mike damunka kan wancan guy d'in, nafad'a maka bawata alaka tsakani na dashi amma ka kasa fahimtar haka, yakakeso nayi da raina ne"

"ke karki d'auke ni sakarai wanda baisan abinda yake ba, Allah kad'ai yasan tsawon wane lokaci kuke tare dashi bansani ba sai wannan lokacin yasa nasani" shuru tayi don tasan koma mai zatace mashi bazai tab'a fahimta ba don yariga da yayi nisa "wani kallan ukku saura kwata yak'ara maka mata yace

"dole kiyi banza ki kyale ni inta surutuna ni kad'ai dan nasa yariga da yasaye zuciyarki, dan shi bazaki tab'a nuna mashi wannan miskilancin naki tunda sonshi kike"

"ya isa haka ya Rasheed! Ya isa!! ya isa!!! Kadame ni da hayani" tayi maganarne cikin fushi da d'aga sauti

"na dameki!! Ok badamuwa, sauka saikije wanda bazai samaki hayaniya ba yamaidake dama shiya kawoki"

Fitowarsu MM ne yakatse masu tak'addamar da suke

"kice nan kika zagayo kinbar Maryama da cigiyarki" cewar MM da yak'araso bakin motarsu, yayinda goga Mr Aabid yayi hanyar wurin da yayi parking motarshi batare da yakalli inda suke ba dukda zuciyarshi na azalzala mashi da yakalli inda take amma yakasa don yasan ba abinda zaik'aru dashi sai bak'in ciki da tashin hankali ganin tana tare da wani

Murmushi Rasheed yasakarma MM wanda zamu iya cewa na yakene "muna tare da'ita kardai ace batayima Madam bankwana ba, to wurin wa tamak'ale kodama ba wurinta tazo ba?" yayi maganar cike da tabbatar da zarginshi

Tuni MM ya harbo inda zancen nashi ya dosa "a'a Maryama takawo ma ziyara, namayi mamakin daba tare kuke ba saida tace man kaje Zamfara"

"hmmmmm, well bari mu wuce naga bak'on naku ya wuce"

"to Rasheed godiya muke, Azraa sauka lafiya"......"Allah yasa ya MM"

tafe suke cikin mota bawanda yayi magana cikinsu har suka kawo gidansu Azraa, bud'e motar tayi amma tajita a rufe

"meyasa dana kiraki dazu kika kasheman waya bayan bamu gama magana dake ba"

"bankashe ba laifin nertwork ne"....... "lailakam laifin nertwork, naji yanzu bani wayarki akwai abinda nakeson induba" dam gabanta ya fad'i sanin inda tabar wayar "dake nake" yak'ara maimaita mata, hand bag d'inta tafara dubawa kamar gaske nemanta take

"namanta ta gidan Maryama" wayarshi yazaro yayi dialing number tah, tana ringin amma ba'a d'auka ba, layin MM yakira ya tambayeshi ko Azraa tabar wayarta, amma sukace mashi bata bari ba, juyowa yayi yakalleta sosai yace

"har wayarki kika barmashi yayi kyau" bud'e mata k'ofar motar yayi yace "Allah yabamu alkhairi saikije ki cigaba daga inda kuka tsaya"

"insha Allah" abinda kawai tace mai tare da bud'e k'ofar motar ta shige gida, baisan lokacin da wasu siraran hawaye suka zubo mashi ba bayan ta shiga gida

"ya Allah kasauk'ak'a mani son wannan baiwar taka, kan son abinda bani da tabbacin yazama alkhairi gareni, ya Allah kazab'a mani abokiyar rayuwa tagari, Allah in har Azraa alkhairi ce ga rayuwata da addinina Allah ka jarabeta da sona fiye da yadda ka jarabeni danata" addu'ar da yayima kanshi kafin yabar k'ofar gidan ya wuce gida

A b'angaren Aabid ko da kyal yakai kanshi gida jin yadda zuciyarshi take mashi zafi, koda yaga kiran Rasheed bak'aramin hautsina mai tunani yayi ba, dakewa kawai yayi ganin sunan dake yawo na Rasheed kan allon wayarta don yasan shi kad'ai zata sama haka _TO BE_ ganin sunan datasa yak'arajin zuciyarshi kamar za faso kirjinshi ta fito don tashin hankali

Bayan faruwar abun kullum Rasheed zaizo yakaita makaranta wanda baya ga gaisuwa ba abinda ke shiga tsakaninsu, dukda shikad'ai yasan ya yakeji game da'ita narashin share juna dasukeyi, kuma har yanzu Mr Aabid baibata wayarta ba asalima bata k'ara sashi ido ba tunranan da abin yafaru

Mr Aabid Abdallah haifefen garin sokoto ne iyaye da kakanni shine d'a na biyu ga mahaifansa akwai khadijah, Aabid, Aminatu, sai Auta Ummu Aymana, mahaifinshi hamshak'in d'an kasuwa ne wanda yadad'e yana nema kuma yatara yana sahun gaba-gaba na masu kud'in jiharsu ko ma muce k'asa baki d'aya, yakuma tsaya tsayin daka ganin ya inganta iyalenshi wurin ganin yabasu tarbiya, ilmi da abinda zasu dogara da kansu, a yayinda khadijah ke auran wani k'usa a gwamnati suna zaune garin Abuja, sai Aminatu dake aure garin katsina wanda yanzu yarage daga Aabid sai Aymana basuyi aure ba

Aabid matashin saurayine da baigaza shekara 33 ba kyakkyawane nasahun gaba domin kuwa komai yahad'a wanda akeson namiji dashi,gashi farine tas kamar ba indiye don sautari wasu abokanshi nakiranshi da sharukhan d'in Naija saboda yanayin kama dasuke dashi wanda kyawun nashi na dilmiyar da wasu 'yan mata kan wutar sonshi.........

Maryama da Azraa ne zaune wurin shak'atawa na cikin makarantar suna hutawa kasancewar sun samu d'an hutun rabin sa'a kafin su cigaba da darasi, Maryama tace

"Azraa waimeke damunki kwana biyu naganki kin k'ara zama so silent haka what is goig on" yatsina fuska tayi tace

"Normal Maryama"....... "banyadda ba kigaya man mekefaru don ba haka kike ba"

"Nida ya Rasheed ne, tun ranan danaje gidanki yaga motar Mr Aabid shikenan yabi yatada mana hankali nidashi, wai yafuskanci soyayya muke nida Mr Aabid,shiyasa kwana biyun nan sai wani sharewa yake"

"Ya Rasheed kishinshi yayi over, baisan ma bakwa shiri da wanda yake tada jijiyar wuya kanshi ba, koda yake nima fa nafara zargin Mr Aabid duba da irin kallon daya biki dashi ranan gidana dakika zo d'aukar wayarki da aka kiraki"

"niba ma wannan ba wayana tana wurinshi tun ranan baidawo man dashi ba"....."ya akai wayarki taje wurinshi?"

"Maryama tashi mukoma aji bani da time na amsa maki wannan tambayar,kinga harmun k'ara mintina biyar kan yadda aka bamu nashiga wani darasin"

"aida yake na hannun damarkine kida periot d'in may be yamarmu mushiga koda mun sab'a lokaci" tak'arsa maganar cikin zolaya, "kanki akeji nikinga nayi gaba inkin gama hayaniyar kin k'araso ajin"

Tatsaya suna gaisawa da wani course mate d'insu wanda har Maryama ta wuceta tashiga aji, shigar Maryama aji dakusan mintina 2 biyu Mr Aabid yashigo wanda su Azraa basu hangi shigar shi ba,wanda shi ya hangeta da wani tsaye suna magana, saida wasu d'alibai 'yan ajin nasu suke fad'in munyi missing lecturer Mr Aabid yarigamu shiga, ganin yabarsun sunshiga yasa Azraa da wannan saurayi yasa suma suka gwada sa'arsu kozaibarsu sushiga

"out" abida kawai yace masu, juyawa sukayi batare da gardama ba suka nemi wurin zama kafin yagama

Bayan yagama basu darasin ne yace ma Maryama tace ma Azraa tasameshi ofis yanzu

"Azraa Mr Aabid na nemaki" cewar Maryama daki isarmata da sak'on "mezanmashi"....."kunfi kusa saiki k'arasa kiji, iyakata isar da sak'o nasanar nafitaπŸ™…πŸ»‍♀"

Knocking! Knocking!! Knocking!!! "yes coming" cewar Mr Aabid dake zaune cikin ofis "Assalamu alaikum".... "ameen waalaiki salam, have a seat" cewar Mr Aabid, zama tayi kafin tace "ance kana nemana" kwalin wayar Ipad sabuwardal yamik'o mata "gashi wannan wancan bansan inda nasashi ba"

"kabarshi kawai, inkaga wanca kowane lokaci ne kabani" tare da mik'awa zatabar ofis d'in, saurin sama k'ofar key yayi ya matso gaban kujerarta ya'azamata saman cinyarta

"gashi nan inkinfita kiyarda ko kiba maiso, inkuma damuwarki kar saurayinki yagani wannan matsalarku ce"

"thanks, bud'eman zantafi muna da darasi yanzu"....."na'aza badarasi kikazo ba don naganki dazu da wani wanda har yahanaki shiga darasin da yagabata"

"darasi nazo d'azuma kuskure aka samu" Baza yayi da'ita yakoma bisa kujerarshi ya cigaba da cike wasu takardu, ganin har lokacin tashi yayi baice mata komai ba yasa ta kalleshi tace " kabud'e man time d'in tashi yayi zanje gida"

Agogon hannunshi yakala yaga time yaja sosai yasa yabud'e mata k'ofar, koda tafito gaban ofis d'inshi sukayi 4 eyes da...............gata rungume da kwalin waya

*MRS ABDUL SULE*🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA :*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*



*PAGE 8*

*_Juma'atu kareem..........._*

*D*a Maryama dake k'ok'arin bud'e k'ofar ofis d'in ta shiga suka had'a ido "haba Azraa yau kina cikin hankalinki ki kuwa, tund'azu kinbar ni inata yawon nemanki duk inda nasan kina zuwa naje amma banganki ba, dan banyi tunanin har yanzu kina wurin Mr Aabid ba duba da irin yadda lokaci yaja"

"Maryama bazaki gane ba, bansan abinda Mr Aabid yake nufi dani ba"


"me kuma yafaru?, koda yake sauri nake yanzu MM yakirani yana jirana bakin get zamu wuce gida, kema d'an anacen naki sarkin kishi gayacan yana haukan nemanki, dukda nima fushin naki yashafeni dan gaisuwa kawai ta had'amu dashi, gashi kuma oga Aabid yayi kyauta" tare da nuna wayar dake hannun Azraa

"Maryama bari nabaki wayar nan kije dashi gida zuwa gobe saimu san yadda zamuyi dashi"

"kitafi dashi kawai zaifi, yakamata kirage jin wannan tsoron nashi tunda ko auranshi ke kanki iyakarta kenan, balle ba'a riga da anzargaba balle yanuna ikon mallaka kanki"

"ni bashi bane damuwata ba, Ummace damuwata yanzu nakoma mata da wannan wayar nashiga ukku da fad'anta k'arshema tace rok'o nayi aka bani, kuma ya Rasheed tsab zaice bashi yasiya man ba"

"dukda haka kije dashi sakiyima Umma bayanin dakika ce yayi maki"

"ya Rasheed fa ya zance mashi kinsa bazai fahimta ba"

"wannan kuma tsakaninku,kinga tafiyata kema yanacan yana jiranki"

"ok, sai gobe inbaki ganni gobe ba Umma tayi lugude dani kan wannan wayar, dabatama ko birge ni ba" tak'arasa maganar tana yatsina fuska

Murmushi Maryama tayi tak'ara gaba tare da waving hand d'inta ga Azraa, Azraa kuwa gwiwa sab'ule tak'arasa inda Rasheed yayi parking

"Assalamu alaikum" ...Waalaiki salam" tare da sauke idanunshi kan wayar dake hannunta "ya Rasheed barka da rana".... "barka" bayan sunshiga cikin motar yaja suka tafi

Tafe suke kamar kurame ba maicewa komai, dan kowa da irin tunanin dayake cikin ranshi, Azraa ce takawar da shurun ta hanyar cewa "ya Rasheed inason muyi magana dakai in kana da time ko zuwa anjima ne"

"yanzuma kina iya maganarki, dan bansan ko zuwa anjima ba kina da ajanda da wani ganin irin tsaleliyar wayar da ya damk'a maki may be zai biyo sahunki ki anjima ki k'ara mashi godiya"

"oh my god! Ya Rasheed dan Allah ka fahimce ni mana"...... "bawata fahimta dazan maki Azraa" daga haka basu k'ara cewa junansu komai ba saima speed d'in motar da yak'ara ga wak'ar sani sabulu dake tashi cikin redion motar

"thank's yaya Rasheed"..... "for what?"....... "for everthing" kad'a kanshi kawai yayi yaja motar ya wuce gida, koda yashiga cikin palourn hajiyarsu nazaune bisa sofa tana karatun al'qur'ani maigirma, saida takai aya sannan ta amsa mashi sallamar da yayi kafin ta rufe qur'anin ta kalleshi da kyau tace

"lafiya Rasheed kwana biyun nan naga duk kazama wani sukuku dakai, kardai maganar rashin tsayar da bikin nan ke damunka, dan nasan halinka da kwallafa rai da abu"

"ko d'aya Hajiyarmu kawai yanayi ne na yau da gobe wanda bata barin d'an adam ya zauna lafiya"

"to aidama rayuwa sai hak'uri domin duk inda d'an adam yake cikin jarabin rayuwa yake maikyau ko akasin haka, fatadai kamik'a lamurranka ga Allah saika ga kasamu dacewa daga wurin rabbil izzati"

"Allah yasa mudace".... "ameen Rasheed, har yanzu fa gidansu Azraa muke saurare muji wane lokaci suka tsayar"

"badamuwa Hajiya duk lokacin da suka aiko dai-dai ne, bari inshiga, inaso in d'an kwanta kafin lokacin sallah yayi" daga haka ya wuce part d'inshi





"Azraa, Rasheed waya ya canja maki ne naga ba waccan bace, kwana biyu ma nadaina ganin kina amfani da waccan ko lalacewa tayi" kirjin tane yafara luguden markad'e nasanin amsar dazata bata kan wayar

"kinyi shuru, ko Rasheedu kika rok'a ya canja maki, kwana biyu ma nadai na ganinshi ko lafiya"

"Umma lafiya lau yana nan ai kullum shike kaini makaranta yakuma d'auko ni"........"ganin banga yana shigowa ba yasa nace ko baya gari, ita kuma wannan wayar yaushe ya canja maki ita?"

"Umma bashi yasai mani ba"...... "to wayabaki?" bayani tayi ma Ummma tundaga randa taje gidan Maryama da kuma yadda Rasheed yakasa fahimtarta

"Azraa! Azraa!! "Azraa!!! ki kiyayi duniya da abinda ke cikinta, kinga muna zaune cikin rufin asiri kijawo mana abinda yafi k'arfinmu, dukda ba alk'awari aure ke tsakaninki da Rasheedu amma mahaifinki shiya bashi iznin neman aurenki, in har kun aminta da junanku, kuma ba wannan tunin shi zaibaki damar wofintar dashi ba kizab'i waninshi nagaya maki, don matsawar ina da nunfashi baki da mjin da ya wuce Rasheedu kinji nagaya maki dan haka maza ki maiyarma wanda yabaki wannan shirmen tunkafi wanki hula yakaiki ga dare"

"Umma Allah ya huci zuciyarki insha Allah zanmayarmai da kayanshi"..... "dayafi maki" cewar Umma da ta tashi daga zaman firar da suke

Washe gari tunkafin su shiga darasi ta nufi ofis d'inshi dan tamayar mai da wayarshi, kwankwasa k'ofar ofis d'inshi tayi kafin yabata iznin shigowa, bayan sun gaisa ne tamik'amai kwalin wayar "gashi"........"saboda mai zank'arba bayan mallakinkice" cewar Mr Aabid

"Ummata ce ta umurceni da in maido maka dashi, wancan data b'ata anyafe maka"

"karkiyima Umma k'arya, kedai fad'i gaskiyar waya ce kidawo dashi?" a zamashi tayi bisa table d'in ofis nashi batare data bashi amsar tambayar da yayi mata ba ta juya zatabar ofis d'in "Azraaaaaaah, dawo ki d'auki wayar nan" cigaba tayi da tafiyarta, takowa yayi ya cimmata tare da juyo da fuskarta suna fuskantar juna

K'urama juna ido sukai har zuwa na dak'ik'a kad'an, kafin Azraa tayi saurin sadda kanta k'asa, hannunta yakama har zuwa gaban table d'in ya damk'a mata wayar a hannunta, tare da kama d'ayan yana murzamata cike da mugunta alamar horo, wanda yana murzawa shikad'ai yasan abinda ke mashi yawo cikin kwanyar kai

"washhh Sir karka karyaman yatsu"....... "gobe in ank'ara maki kyauta ki k'ara mayarwa" yasaki hannun tare da sakin wata siririyar ajiyar zuciya

"kiyi saurin shiga aji kafin infito don in na rigaki bazan bari kishiga ba" kallan kasaba yin haka tayi mashi kafin tabar ofis d'in

Batafi minti biyar da zamaba ya shigo suka cigaba da d'aukar darasi

Bayan tadawo daga skull ne tayi ma Ummarta bayanin yak'i karb'ar wayar wanda saida tasha fad'a sosai kafin Umma tayarje mata amfani da'ita da sharad'i inhar Rasheed yace baisan tayi amfani da wayar to dole ta ajiyeta

Shirye- Shiryen dawowar Alhaji Abdallah suke mahaifin Aabid wanda gidan ya kacame da girke-girke kala kala don tarbar maigida ran gida, Aabid ne yafito cikin shirinshi na d'auko mahaifin nashi daga Airport, sanye yake cikin shadda bower fara sal tasha aiki da brown d'in zare, wanda yabashi damar sa brown d'in takalmi da hula, sai ogogon d'anyar azurfa dake d'aure a tsintsiyar hannunshi, Momy ce dake hakimci bisa sofa yakalleta cikin zolaya yace "Momy duk kwaliyar tarbar maigidance haka"

"Aabid matar ubanka, kaga ja'irin yaro ni sa'ar kace"..... "Momy na sorry πŸ‘πŸ» kin kintsa muje taroshi"....... "a'a kaida Aymana zaku inkuma ta tsaya kwalliya saikaje ka kyaleta don baifi 25 minutes ba jirginsu yayi landing"

Fitowar Aymana ce yasa suka wuce batare da suntsaya b'ata lokaci ba, wanda itama shigar datayi bak'aramin ansa fatar jikinta ta tayi ba

Azraa zaune tana yankar farce (akaifa) Rasheed yayi sallama yashigo, Umma ce dake bakin murhu ta amsa mashi sallamar

"lale marhabin da Rasheedu wucceke, ke Azraa tashi d'auko ma yayanki kujera kikai zaune kina kallon mutane" tashi tayi da d'auko mai plastic chair wanda saida yagaida Umma kafin ya zauna

"ya Rasheed ina wuni".... "lafiya" amsar kawai da yaba Azraa kenan data gaisheshi

"anjima ko nake cewa inje bikon d'ana kwana biyu nadaina ganinka"........"lafiya lau Ummma wasu 'yan aiyuka ne sukasha kaina, amma komai yaza normal insha Allah"...."Allah yataimaka"..."ameen Umma" da haka suka cigaba da hirarshi da Umma wanda tana lura dashi da yakalli sashen da Azraa take sai ya harareta

Wayar Azraa dake gefenta ce tafara ringing,mamaki ne yakamata sanin bawanda yasanta da layin dan ko Maryama bata ba number data gani cikin wayar ba, k'ara kiranta akai karo na biyu don wancan da yariga dayazama miscall sanin batasan maikiranba yasa yakatse bata d'auka ba

"ba wayarki ake kiraba?, koko ta Rasheedu ce"

"a'a Umma wannan wayar manya ce batawa bace" wanda yayi maganar har saida Umma tagane cikin zafin kishi yayita, sanin halinshi yasa tak'i d'auka, ganin haka yasa Umma tabarmasu filin tsakar gidan tashige d'aki tasaki labule

"ki d'auki wayar aikinsan maikiranki".... "Ya Rasheed ba wanda naba wannan layin dan haka nibansan waye yakira niba"

"wanda yabaki wayar shike kiranki kin kuma sani"....shuru yaratsa wurin na mintina biyu kafin wayar tak'ara ringing

Takowa yayi har kusa da'ita ya d'aga kiran yasa handspeak yaji muryar namiji yana sallama, saurin datse kiran yayi batare da yayi magana

"kince baki san kowaye ba, amma yanzu kingane muryar kowaye ai?"

Abayarta tad'auka dake rataye bisa igiyar shanya tace "ya Rasheed muje soro (zaure) inason muyi magana dakai" baimusu mata ba ya wuce tabi bayanshi

Suna shiga zauren sak'o na shigowa ta wayar Azraa kamar haka wanda Rasheed ne yabud'e yagani _kuna tare shiyasa bakya iya d'aukar waya in an kiraki_


Mik'a mata wayar yayi yace "gashi yana jiran amsarki" amsar wayar tayi tace "ya.... "dakata Azraa banson jin komai daga gareki tuni na fuskanci inda kika dosa"

"ya Rasheed wallahi bansan mai number ba hasalima bantab'a amsawa waya da'ita ba" takowa yayi ya amshi wayar yayi dialing number da aka kira da'ita,handspeak yasa wayar yana fara ringing yamik'a mata, muryar Mr Aabid ce ta doki dodonan kunnanta inda yake mata sallama, nuni Rasheed yayi mata da ido na datayi magana

"aminchin Allah ya tabbata garemu"........ "kisa meni gidan MM akwai maganar dana kesomuyi" kashe kiran yayi batare da yaji amsartaba

Innalillahi wa inna ilahi raju'un abinda Rashee ke nanatawa cikin ranshi kawai kenan, saida yaji sauk'in abinda ke mai yawo cikin kirji sannan ya rab'e ta gefenta zai wuce

"ya Rasheed nasan bani da kalmar dazance maka saida nace don girman Allah kayi hak'uri"

"inyi hak'uri inkyaleki kibashi damar gabatan dakanshi wurin magabatanki, aiko baki ce ba dama zanbarki! Azraa zanbarki!! zanbarki!!!" tare da buga kanshi gabango, ganin baida alamar denawa yasata rik'emai hannu tabaya "ya Rasheed stop that"

"kirabu dani Azraa kitafi kije yana jiranki" tare da fizge hannunshi daga nata, bata daddara tak'ata kamo hannushi wanda jiyake kamar ya rungumeta ko yasamu sauk'in da zuciyarshi kemashi

"Azraa sakarman hannu".... "Ya Rasheed bazan sake ba, saika mani alk'awari bazaka k'ara buga kanka a bangoba" bakinta kawai yatsurama ido ganin yadda take magana, baisan lokacin da ya had'e bakinshi danata yahau tsotsa, ringing d'in wayarta ce daya karad'e soron gidan wanda yadawo dasu daga duniyar da suke son sutafi

"ki d'auka" yayi maganar cikin wata irin kasalalar murya, daga haka yafice daga gidan.........

*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKRWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*SISTOO ASIYA MK WANNAN CHAPPY NAKI NE KIYI DAMA-DAMA DASHI, DAMARKI CE*

*PAGE 9* to 11

*K*oda yafito gidan cikin motarshi yashiga ya had'a kai da sitiyarin mota, zuciyarshi namashi wani irin k'una

30 minutes yad'auka yana jiranta k'ofar gidan MM yaga ta ina zata b'ullo, amma shuru ba labarinta,layin MM yakira yace mashi yana k'ofar gidansa, iso yayi mashi da yashigo palour, bayan sun gaisane, Mr Aabid yake tambayar ina madam "kotayi maka nisan kiwo na ganka kai kad'ai" cewar Mr Aabid "tana can tana shiri zuwa gidansu Azraa" hamdallah yayi cikin ranshi yace lallai fad'uwa tazo dai-dai da zama, Maryama ce tafito cikin shirinta, bayansun gaisa da Mr Aabid, takalli MM tace "honey bari kawai nayi driving naje tunda kanada visitors" Aabid ne yayi saurin cewa ba matsala Hajiya Maryama bari munyi dropping d'inki dama akwai inda nakeson yaraka ni"

Daga haka suka wuce gidansu Azraa wanda har lokacin Rasheed baibar k'ofar gidan ba, koda Aabid yaga motar Rasheed bak'aramin tashin hankali yaji ba dakewa kawai yayi, kamar ance ya d'ago idonshi, yaga motar Mr Aabid tayi parking kusa da tashi, lokaci d'aya wata zufa taketo mashi bai ida shan mamaki ba saida yaga MM da Maryama dasuka fito daga motar Aabid, Maryama ce tashiga cikin gidansu Azraa yayinda MM ya nufoshi,hannu yamik'a mashi suka gaisa, Aabid ko zamanshi yayi cikin mota bashida niyyar fitowa saima dane-dane da yake da waya

"oyoyo Mrs MM" cewar Azraa data fito daga d'aki jin sallamar Maryama datayi a tsakar gida

"ke nifa ba wurinki nazo ba wurin Ummata nazo,ehhhhe" Umma ce itama tafito daga d'aki tace Maryama kece a gidan namu"...... "eh Umma, an wuni lafiya" "lafiya lau, ya maigidan?" "tarema muke dashi da wani abokinshi yana son yashigo ya gaisheki"

"ai badamuwa Maryama kice su shigo" waya kawai ta d'auka ta kirashi tace Umma tace su shigo, wanda Azraa kwata-kwata bata kawo cewar Mr Aabid bane abokin MM dasuka zo tare

Kallon ikon Allah ya tsaya gani, ganin MM da wancan guy d'in sunshige gidan Umma, take zuciyarshi taci gaba da tafarfasa kamar zata kama da wuta don jin zafin abinda su Azraa ke shirin yimashi

Sanye take cikin english wears duguwar riga mai hannu best wanda ta matseta sosai wurin boobs d'inta da kuma k'ugunta, tun shigowarta daga wurin Rasheed tacanza atamphar datasa dazu zuwa doguwar rigar wanda bak'aramin amsarta rigar tayi ba, kanta ko bako kallabi kasancewarta bata cika sashi ba sai zata shiga makewayi ko kuma in Umma taimata fad'an d'aura kallabi


"Umma barka da yamma" cewar MM tare da durkusawa alamar girmamawa, shima Aabid durk'usawa yayi yana kwasar gaisuwa, yayinda Azraa tayi mutuwar tsaye dan batayi tsanmani tare suke ba dan koda tana gayama Umma lokacin tashiga d'ayan d'akin ta d'auko masu tabarma su shinfid'a

"Azraa kawowa su Muhammadu ruwa mana kikayi zaune" kunyace ta hanata tashi sanin kayan dake jikinta gashi ba abaya kusa da'ita balle tajawo tasa, "bada ke nake ba kikayi zaune" tashi tayi cike da kunya, Aabid kuwa wata harara yabita dashi, bayan ta'aje masu ruwan taja Maryama suka fita daga d'akin

"yanzu naga motar ya Rasheed k'ofar gida ga dukkan alamu kamar yana cikin wani yanayi nab'acin rai" fitowar su MM yahanata yimata maganar datayi niyya "Hajiya Azraa ba gaisuwa"

"yaya MM barka da yau"......"barka ya makaranta"...... "Alhamdulillah"

kallonta takai inda Aabid yake tsaye, "Sir barka da yamma" "barka"

"madam bayan sallar isha'e zandawo saiki kinmtsa kafin lokacin da nan masallacin Sidi Attahiru zanyi sallah"......."ok yaya Allah yakaimu" daga haka suka wuce

Koda suka fita sun iske Rasheed nata feta salansar motarshi da wani kwali "Rasheed lafiya meyesamu salansar motar?"

"MM zafi take shiyasa nake fetawa" tuni suka gano bakin zaran nashi watau kishi yake ganin Aabid ko wurin Azraa yazo, abinda MM kawai ya ayyana aranshi kenan

"amma katadata bata tashi bane koyaya?"....... "MM kuje kawai nasan zata tashi yanzu" daga haka yashiga motar ya fizgeta ya kyalesu nan tsaye

Murmushi kawai Aabid yayi suka shiga tasu motar sukabar k'ofar gidan

Text ne ya shigo wayar Azraa daga number da aka kirata d'azu _"ki kasance koda yaushe kina da suturar kirki jikinki ba mai nuna tsaraici ba"_

"Maryama, Mr Aabid na neman haddasa mani fitina tsakanina da ya Rasheed"

"mekuma yafaru?" gayama Maryama tashiga yi tun farkon kiranta da yayi da kuma text d'in da yayi mata na su had'u gidanta

"no wonder naga ya Rasheed cikin wannan halin, kuma yanzu zarginshi zai tabbata bare yaga munzo dashi Mr Aabid d'in, wanda haka zak'ara tabbatar da cewa tare kuke dashi"

"ni wallahi Maryama lamarin ya Rasheed yafara damuna, gashi Umma tace banda mijin da ya wuceshi"

"kiyita addu'a Allah yazab'a maki mijin dayafi alkhairi, amma kishi ya Rasheed yayi over"

_kuyi hak'uri da wannan ana fama da rashin wuta........_

*MRS ABDUL SULE*
[3/5, 4:16 PM] ‪+234 803 588 5385‬: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUW*
*BIEBEE ISAH*

*Batul Adam Jtko*
*Aunty Fauza*
*Muneerah*
*Khadijah Kt*
*Nappy Saulawa*
*Aisha Ali Garkuwa*
*Aisha Machika*
*Aisha Sada Machika*
*Zubaida Aliyu*
*Jiddah Cool*
*Jiddah Saudiyya*
*Mrs Mansoor*
*Sa'adat Alk'ali*
*Ummy Ontop*
*Maryam Ahmed*
*Maimouna Nijar*
*Jiddah Samusa*
*Ummy Abduol*
*Aysha Hamzart*
*Natural*
*Noor*
*Maryerhm Ishaq*
*Miss Ayusha*
*Amira Aliyu*
*Fauxia MB*
*Fareeda Saraki*
*Nafisa Isah Shehu*
*Beebhaloh*
*Maryam Shitu Gozaki*
*Little Miss*
*Miss J*
*Aysha Ehman*
*Ummien Fauza*
*Ummu Nabil*
*Mum Jay*
*Mom Hanan*
*Meenat yakasai*
*Maryam Maishanu*
*Maman Twince*
*Maman Arfat*

*Damarkuce πŸ‘πŸ»*

*PAGE 10*

*"M*r Aabid niko inason nayi maka wata tambaya, wai maike tsakaninka da Azraa ne, don nakula datake-takenka akanta tun lokacin bikina da Maryama"

"wacece haka?".... "bansani ba" cewar MM

"sorry abin baikai na bak'arar magana ba" dariya MM yayi yace "intayi wari dai maji" "bama wani wari da zatayi balle kuji, yarinyar da ko al'ada bata fara ba, balle kace zata d'auki lalurar d'anshekara 33"

"amma Aabid ba d'an iska irinka, Azraa ce bata fara haila ba" kallon raini yayi mashi yace

"inma tafara baiwuce wata d'aya da ya wuce ba"

"kaini ba wannan ba, yanzu ina muka nufa? kace zan rakaka wani wuri"

"gidansu Saleemah naso zuwa amma nafasa sai wani lokacin, kasan Daddy yarik'e wuta wannan karan aure bafashi, gashi ni ban shiryama hakan yanzu ba"..... "Ai haka da Daddy yayi maka shine dai-dai"

"au haka zakace, nifa ba Saleemah ke banso ba auren 'ya'yan masu kud'i ne basa burgeni nafison auren 'ya'yan talaka, amma shi Daddy yafison kwarya tabi kwarya"

"Allah yazab'a tagari shine fata domin kowace da halinta take zama, domin zaka samu 'ya'yan masu kudin da halin kirki 'ya'yan talakar kuma sab'anin haka, addu'a dai Allah yabamu abokan rayuwa nagari da zuri'a d'ayyiban, shine fata" daga haka sukaci gaba da firarsu wanda yashafe al'amurrar rayuwarsu

*

Alhaji Abdallah mahaifin Aabid ne zaune suna tautana yadda bikin Aabid zaikasance shida Hajiya Asiya mahaifiyar Aabid, saboda sunriga da suntsayar da lokacin bikin shida mahaifin Saleemah nan da wata biyu masu zuwa, Mr Aabid ne yayi sallama yashigo palourn yatarar da mahaifannasa suna tattauna maganar data shafi bikinshi da Saleemah, gaishesu yayi, yayi yunk'urun barin palourn mahaifin nashi ne ya katse mashi hanzarin barin palourn da yayi niyyar yi ta hanyar cewa

"Aabid abinda nakeso dakai kayi k'ok'arin kammala gidanka kafin nan da sati 6, dan munriga da munyanke shawarar nan da wata biyu masu zuwa ne lokacin bikinka" dammm yaji gabanshi ya fad'i, nisawa yayi yace

"Daddy danaso ak'ara mani lokaci don akwai shirye-shiryen danake sonyi gashi lokacin da kukasa bana tunanin na kammala kafin lokacin"

"what! mekake cewa Aabid a k'ara maka lokaci?, to bari kaji ingaya maka wannan karan baka isa katsallake umarnina ba, wacen karan na kyaleka saboda wasu dalilai da na bincika yarinyar nadasu, amma wannan kasani kamar anyi angama don ba fashi,kaji nagaya maka"

"Alhaji kodai a k'ara mashi lokacin tunda bamusan uzurinsa ba" cewar Hajiya Asiya

"dama keke d'aure mai gindi yayi ma mutane yadda yaga dama, to tsaya kiji daga ke harshi baku isaba a d'aga ba, don ko k'ark'ashin ikona kuke"

"Allah ya huci zuciyarka Daddy yadda kace haka za'ayi" daga haka yamik'e yabar palourn

"zancen banza zance wofi, yanzu haka wata d'iyar talaka yalik'emawa suka shanye kurwarsa yakeyima mutane yadda yaga dama, duk lokacin da aka tuntub'eshi da maganar aure"

"Alhaji, talakama ai mutum ne, kaida muyima 'ya'yanmu samun abokan rayuwa nagari, bawai zab'in ranmu ba"

tsaki yasaki yace "nidai nagaya maki babu talakka cikin tsarin rayuwata"

*

"Azraa latsoman number Hajiyar Rasheedu kice mata ina nan zuwa don jiya danaje bansameta ba"

"Umma bani da number ta a wannan wayar, a waccan wayar nake dashi"

"to Rasheedun fa, koshima baki da'ita, sai wanda yabaki waya kike da layinshi"

"Umma ni bani da number kowa a ciki"

"to aishikenan kinyi dai-dai" daga haka suka cigaba da tautaunawa kan lamarin rayuwar yau da gobe

***

Fitowarta kenan daga gida tana sauri taje gidan Maryama don akwai handout data keson amsowa wurinta , gashi suna da gwaji na course d'in

Turus tayi ta tsaya ganin Rasheed zaune cikin moto k'ofar gidansu, kallonta yayi kamar bazai magana ba kasancewar haryanzu yana fushi da'ita tun ranan da Aabid yazo, d'aurewa yayi cikin muryar da zaka fahimci sonta na wahalar dashi yace "Wifely sai ina da yammacin nan haka?"

"ya Rasheed barka da yamma"..... "baki bani amsar tambayata ba"

"ya Rasheed zanje gidan Maryama amso handout"

"a'a fad'i gaskiya, zakidai zance wurin malaminku"

"dan Allah kabar maganar nan tunda anriga da anwuce wurin"

"a wurinki ba, any way muje na ajeki inhar in yaganni bazai damu ba" tare da yarfa hannuwanshi

"kabarshi kawai nagode"....... "kina gudun b'acin ranshi ko?"

"ya Rasheed badamuwa muje aka ajeni tunda har yau baka yadda dani ba" daga haka tabud'e gaban mota tashiga yaja suka tafi

"niko Azraa haryanzu Umma batace komai kan maganar bikinmu ba"

"eh" shuru ya ziyarci motar na d'an wani lokaci kafin Rasheed yace "miye dalilin dayasa har yau batayi wata magana akan haka ba"

"bata fad'a mani komai akan haka ba" cikin rantako cewa take kayan d'aki ne matsalarmu, kallonta yayi yace "Azraa kodai kincanza ra'ayi akai nane?"

"a'a ya Rasheed akwai dai dalilin dayasa batace komai ba"

"wane dalili ne dazaisa bazaku iya sanar dani ba, na d'auka d'a ta d'auke ni ba suruki ba balle har a b'oye mani wani abu" ta bud'e baki da niyyar tayi magana taga Prado a bakin get d'in gidan Maryama wanda ba tantama motar Aabid ce don yatab'a zuwa da'ita d'anfodiyo, harara Rasheed ya watsa mata yace

"aiga dalili can da yahana kuce wani abu, saki sauka kije yana jiranki" wanda a b'angaran Mr Aabid yazo ne MM yarakashi gidan da yake ginawa saboda wasu kayan da za'a sauke mashi

"Azraa ki saukar man a mota zantafi inada abinyi" yayi maganar cike da hasala

"muje kawai nafasa"... "baki isa ba, saukar mani a mota kije can wurinshi" bud'e k'ofar motar tayi tafita batare data cemai komai ba

Tana shiga gidan ya bud'e motar yafito ya zauna saman motar bayan yahad'e fuskarshi da no respect (gilashin ido)

Ganin haka Aabid shima yafito daga tashi motar ya bud'e k'aramar k'ofar gidan yashige yabar Rasheed nan zaune yana hura hanci yana huci kamar mayunwacin zaki

Dai-dai harabar gidan sukayi arangama da MM dake niyyar fita ya sameshi waje "au kace tare kuke da mutuniyar taka"

Murmuahin yak'e yayi yace "tare dai suke da saurayinta sarki zafin kishi, wanda baya iya b'oye hakan"

"ai Rasheed k'arshe wurin kishi"...... "hmmmmm" abinda Aabid yace kawai "to muwuce kaga lokaci naja banason nakai har bayan isha'e batare da nadawo wurin iyalina ba gudun kar inshiga hakk'inta, domin kuwa nayi rok'o da wannan koyin na ma'aiki S.A.W na duk in wani uzuri zaifitar dashi daga gidanshi irin wannan lokacin sai ya nemi iznin matanshi"

"laila kayi rik'o da babban koyi, mushi ga mugaisa da madam"

"bawani kugaisa da madam, kace dai mahad'a kukai da Azraa kake wani yima mutane basaja" duka yakaimai ga kafad'a yace "kaini inzakiyi mani iso kayi mani inkuma bakayi nakama gabana"

"banyi, baridai naturo maka wanda kazo wurinta" daga haka ya wuce yabarshi nan tsaye

Rasheed kuwa tunda yaga Aabid yashiga gidan yaji kamar zuciyarshi zata kama da wuta dan wani irin zugi datake mashi, baitab'a tunanin Azraa sakarai ta d'auke shiba sai yau watau shizata rainama wayo tace mashi handout zata karb'o alhali wurin wani k'aton banza tazo wanda Allah kad'ai yasan maisuke aikatawa dashi, kwafa yayi ganin wannan bashine mafita gareshi ba yasa yashige cikin motar yabar k'ofar gidan cike da jin zafin Azraa da Maryama dayake ganin itace take turata akan tarabudashi

"Azraa, Mr Aabid yana nemanki yana bakin get yana jiranki".... "ya MM ni kuma?"

"yeesssss abinda yace man kenan" alama Maryama tayi mata da ido natadaje, mik'ewa tayi cike da sanyi jiki ta fita

Zaune ta iskeshi bisa wasu milk colour d'in chairs da akayima harabar gidan k'awanya dasu

"kisa meni a mota daga haka yawuce yabar harabar gidan "insameka a mota abinda" tayi ta nanatawa kenan a ranta, wani sashe na zuciyarta ne ya umurceta dataje tayi mashi warning kan yafita harkarta, wani tunani ne yadarsu a zuciyarta na infa ya Rrasheed na k'ofar gidan tace mashi me kenan, da wannan tunanin ne ta yanke hukuncin ta kyaleshi kartaje inyagaji dazaman jira yasan inda dare yayi mashi, har tajuya zata koma ciki sak'o yashigo wayarta _"wanda kike tunani baya nan ina jiranki karki b'ataman lokaci"_

Cika tayi da mamakinshi na nuna isa da iko, yasa ta maida mashi amsa a karon farko tun lokacin da yafara tura mata sak'o _"sauka lafiya"_ k'arar bud'e get taji yasa ta waiga, takowa yai har inda Take yaje hannunta batare da yace mata komai ba, kiciniyar kwatar kanta tayi amma tagaza saboda barik'on wasa yayi mata ba,janta yayi kamar rak'umi da akala har inda yayi parking car d'inshi, bud'e mata yayi yace tashiga batayi musu ba tashiga, zagayowa yayi shima yashiga mazaunin driver, kallonta yayi wanda itama lokacin ta d'ago ido da niyyar tayi mashi maganar yafita harkarta idanuwansu suka sark'e dana juna, sunshare ak'alla mintina biyar suna isarma da junansu sak'on wanda sukansu basu fahimci hakanba domin kuwa tuni zuciyoyunsu suka aminta da juna yayinda gangar jikinsu tak'i k'arb'ar haka, d'auke kanshi yayi saurin yi domin ko shikad'a yasan abinda kallonta ke haddasa mashi

Kamo hannunta yayi yace "karna sake ganinki da wancan guy bama shikad'aiba duk wani wanda ya amsa sunan namiji kinji nagaya maki" tare da k'ara murza 'yan yatsunta cike da horo

Rasa maizata ce mashi tayi na wannan ikon mallaka nashi, ganin bazatayi magana a yatada mota yaja suka tafi...........

_*Kuyi hak'uri najin shuru na kwana biyu, jiki da jini*_

*MRS ABDUL SULE*
[3/5, 5:17 PM] ‪+234 803 588 5385‬: 🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITES ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*Wannan shafin sadaukarwa ne gareku, group na Aisha Ali Garkuwa, Garkuwan Fulani Group naji dad'in comment d'inku na last page, amma dan Allah zuciyarku ta daina zafi (lol), tare da TABITAl PUlAAKI Group wannan shafin damarkuce*

*PAGE 11*

*S*huru ne yaratsa cikin motar ba wanda kecewa komi don ko kowa da irin tunanin da yake cikin ranshi, baizame ko ina da'ita ba sai shiyyar gawan nama inda yake ginin gidanshi, kallon inda yakawota tayi tace "Sir bud'eman k'ofa zanwuce gida" banza yayi da'ita saima wayarshi da yazaro cikin aljihu yashiga amsa kiran da akai mashi, sallama yayi ma wanda yakirashi, bayan an amsa sallamar, maikiran yaciga da ce mashi

"wai kai Aabid wane irin d'an iska ne, ina kaje da yarinyar mutane" cewar MM da yakirashi a waya yanzu, wanda saida yafito waje yaga basa k'ofar gidan sannan yakirashi

"kasa meni gawan nama" abinda kawai Mr Aabid yace mashi kenan, daga can b'angaren banji abinda MM yace mashi ba saima kiran da naga Aabid ya yanke.

Rasheed koda yatada mota kasa tafiya yayi saima wuri da yasamu yayi mab'oye yana kallon duk wani motsi da suke, har zuwa lokacin da yaga yarik'o hannunta yasata mota suka tafi duk akan idonshi yafaru

Ganin sunja mota suntafi yasa hankalinshi yatashi, baisan lokacin da yarink'a buga kanshi ga sitiyarin mota ba yana cewa "kaicona Azraa bantab'a tunanin haka daga gareki ba, dan nasan ba irin wannan turbar Umma ta d'auraki akai ba, wai yau Azraa kece wani d'a namiji yake rik'e maki hannu wanda ba muharraminki ba, wanda tunda nake dake bantab'a nuna maki soyayya gurbatacciya ta shan minti na samarin wannan zamani, natsare maki mutunchin kanki da nawa har lokacin da zamuyi aure, amma kingaza hak'uri kin biyema samarin *Zamani* masu *Sabon Salon Yaudara*, kaicona Azraa dana aminta dake Allah kad'ai yasan wane kalan soyayya kuke dashi"

Haka Rasheed ya cigaba da zantukanshi tamkar Azraa ce agabanshi, fizgar motar yayi yabar wurin ya wuce gidansu Azraa.

Dan ya k'udirti niyyar yima Umma magana akan sani miye matsayar zancenshi, dan baizai yuwuba ace yarinyar datake shirin zama uwar 'ya'yan ka kana barinta as how kowane gara najanta inda yaga dama, saidai kash koda ya isa gidansu Azraa yayi rashin sa'a baitar da Umma gidan ba domin padlock da yagani gark'ame a k'ofar gidan, kwafa yayi ya wuce wuri wani mai tireda yayi parking ya zauna zaman jiran yaga ta ina Azraa da Ummata zasu fito

Zaman kurame ya cigaba da wanzu cikin motar, wanda bamai cewa da d'an uwansa k'ala, ganin zata k'arama kanta laifi biyu wurin Rasheed da kuma Umma intaga tajima bata dawoba yasa tace mashi

"dan Allah Sir *Aabiiiiiiid* kabud'e man natafi gida kar Umma tayi mani fad'a" wanda kiran sunan nashi datayi bak'aramin jefashi cikin wani yanayi yayi, don saida yaji tsikar jikinshi tashi, dakyar yatsaida natsuwarshi yace

"kardai saurayinki yayi zargin wani wuri kika tafi, tunda Umma tasan inda kikaje"

"naji, koma miye zakace kabud'e man natafi" jaridarshi dake bayan mota yamik'a hannu yajawo ya cigaba da karatu batare da yace mata wani abuba, jitayi kamar ta zunduma ihu ganin yadda yawofintar da'ita ya cigaba da safgar gabanshi, wanda takasa sanin dalilin da yasa yake mata wani iko saikace mijinta, ko kuma wanda yake shirin zama miji gareta

Wayarshi ce tashiga kukan neman agaji ga mai'ita, d'auka yayi yace "ok" sannan ya kalleta yace mata "just 5 minutes for me" daga haka yabud'e motar yafita, jingina yayi jikin motar yayinda MM yak'araso inda yake

"Aabid ina yarinyar mutane?" kasancewar gilashin motar tintac ne baka ganin naciki yasa baiga Azraa dake zaune gaban motar ba "nacinyeta, kozaka kiraman hukuma"

"ko d'aya, amma abinda kayi baka kyauta ba, yarinyar nanfa an tsayar mata da miji baikamata ace a gabanshi kaja mota ku tafi da'ita ba, zai iya haddasa mata zargi a tsakaninsu, tunda kai kasan bawani abu ke tsakaninku ba shiko bazai fahimci haka ba, dan haka ka kyale masu yarinyar kaje kaji da hidimar dake gabanka"

"dakata! Malam inji dai ba auran aka d'aura ba balle kace na sato matar mutane har yanzu Azraa ta mai raboce, don haka daga yau nidashi muzuba mugani"

"ni yanzu banda lokacin wasu surutai naka na rashin kan gado, fiddo yarinyar mutane na maisheta gida, bawai dogon surutu ba"

"baka isaba don ko bakai kakawota nanba, don haka sai naga damar mayar da ita zanmayar"

"haka kace, yayi maka kyau, ni bari na wuce tunda ba amfanin kira dakayi mani" daga haka ya juya wurin motarshi, Aabid ne yace mashi "jimana Malam" juyowa yayi yawatsa mai harara yayi gaba abinshi, bud'e motar yayi yaciga da karatun jaridarshi wanda a zahirin gaskiya bakaratun yake ba, illama kanshi da yajefa cikin duniyar tunani, ba abinda yake k'ara d'agamai hankali illa wai antsayar mata da miji, dukda yaji firarsu da Maryama kwanakin baya.

"dan Allah kabud'e man k'ofa natafi gida, kaga a k'alla munshafe kusan sa'a guda anan, wanda banga dalilin hakan ba" cewar Azraa datayi maganar kamar zaita kuka

"kece baki ga dalili ba amma nikam naganshi" banza tayi mashi tacigaba da wasa da zoben dake hannunta, lura da abinda take ne yasa yakama d'an yatsan dake da zoben yashiga kiciniyar cireshi. "dan Allah meye haka kadena banaso" baibi takanta ya cigaba da k'ok'arin cire zoben, saida yarabata da zobe sannan ya kyaleta, batason lokacin da wasu siraran hawaye ya zubomata ba, kama fuskarta yayi ya shiga lashematasu batare da yayi magana, yayinda tacika da mamakinshi na meyasa yake mata haka ba, wanda tunda take da ya Rasheed baitab'a kai hannunshi ga jikinta balle har yayi mata irin haka

Ganin abin nashi na neman wuce makad'i da rawa yasata kwace jikinta dakyal, ajiyar zuciya ya sauke tare da kamo hannunta ya cigaba da wasa dashi har idonshi na lumshewa "zakaso ace k'anwarkace tare da wanda ba muharraminta a haka? koko ace wanda take shirin zama matarka tare da wani namiji haka?" jin maganganunta yayi kamar a sama, tabbas batayi k'arya ba bazaiso ace k'anwarshi ko mai shirin zama iyalinshi a irin wannan hali, to amma yakasa controlling kanshi duk lokacin da yake tare da'ita, jiyake wani irin maganad'iso na fizgarshi akanta wanda baitab'a jinshi akan kowace mace ba, haka inyaga wani yarab'eta jiyake kamar ya burmama kanshi wuk'a ya hutu irin yadda yakejin k'irjinshi namashi zafi.

Hannunta yasaki, yatada motar suka tafi, baizame ko ina da'ita ba sai k'ofar gidansu wanda har lokaci Rasheed na nan zaune wurin mai tireda, ita kuma Umma bata dawo ba.

"dalilina yafara aiki" tare da kai kallonshi inda Rasheed yake zaune, itama dubanta takai inda yake kallo taga Rasheed zaune yak'urama motarsu ido, motar yabud'e mata yace "sauka lafiya" batace komai ba tasa hannu tad'auke zobenta da aje wurin giyabos, saurin kai hannunshi yayi wurin ya d'auke zoben "wannan ring d'in yagama zama hannunki, saidai wanda yasai maki yasake saimaki wani"

"bani zobena banajin wannan karon zan iya yadda ka salwantarman da abu mai mahimmaci gareni kamar na wancan lokacin" wanda babban tashin hankalinta ace Rasheed ya fuskanci zoben bai wurinta don shine ya mallaka matashi

"indai damuwarki sa zobe, karki damu zankawo maki wani, amma wannan kedashi har abada"

"dan Allah kabarni da zobena don koshine muradina ba wanda zaka kawo ba" kallon kwayar idonta yayi yace "kina k'arama kanki laifi, wurin wancan mai idanun kamar na mayu da yazuba mutane su kamar saban kamun hauka, yakamata kije kiji dashi don wannan zoben ba bakishi zanba, saida kuma inbaki kagaji da ganina ba muciga dazama a haka"

Jiki sanyaye ta bud'e k'ofar motar tafita, hannunta ya damk'o yasa mata wayar data barmashi bisa seat d'in mota, ganin in bata amsaba Rasheed na iya hango hannuta da yarik'e yasa ta amsa, don tayi niyyar barmashi ita, "zankiraki anjima, salan kik'i d'agawa" daga haka yaja motar ya wuce, tagaban Rasheed ya wuce wanda yana zuwa saitin da yake yarage glass yad'aga mashi ✌🏻 ya wuce, wanda bak'aramin k'ara k'ullada Rasheed yayi ba

Ganin k'ofar gidan rufe yasa tagane Umma bata nan, tunani takamayi na ina Umma tashiga har kusan magrib bata dawo gida ba, wanda a k'a'idarta da wuya tayi magariba wani waje sai dole, hangota datayi yasa tasaki murmushi don a rayuwarta tanason mahaifiyyarta, tanason taga ta kyautatama rayuwarta, hangota da Rasheed yayi yasa yanufi inda take, amsar kayan dake hannunta yayi, ita kuma Azraa makulli ta amsa tayi gaba ta bud'e masu k'ofar gidan don lokacin har anfara kiran sallah magariba, "sannu da k'ok'ari Rasheed saikayi haramar alwala atafi masallaci".... "to Umma" buta yad'auka yafara alwala, itama Azraa butar dake kusa dashi tamatsa zata d'auka, saiji tayi yace "kidai tabbatar da kin wanke k'ura da kikasha waje kafin ki fuskanci ubangijinki" wanda yayi maganar slowly ita kad'ai taji miyace

Kallanshi tayi ta girgiza kai tashiga toilet don sarai tagane inda zancensa yanufa, baki kawai yatab'e ya cigada alwala, bayan yagama yace ma Umma inyadawo akwai maganar da yakeso suyi daga haka ya wuce masallaci.


*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*Innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Allah ya amshi bak'unchinki Hajiya Asma'u Garba Baraya Annabi Rahama yasan da zuwanki, uwa mabada Mama 😭😭😭😭😭😭* *R.I.P Firdaus*

*PAGE 12* and 13

*S*aida yayi sallar isha'e sannan yabaro masallacin, bayan yashigo gidan yatarar da Umma itama tayi tata sallar don ko sallayar bata nad'e ba, "Rasheedu kadawo?"... "eh, Umma Allah ya yarda".... "to Allah yakarb'a"... "ameen", shuru ne yaratsa wurin na 'yan wasu dak'ik'a, kafin Umma ta nunfasa tace

"Rasheedu kace akwai maganar dakakeso kayi dani, amma kayi shuru, Allah yasa dai lafiya" sunk'uyar da kai k'asa yayi yana mai k'arajin nauyin maganar da yakeso ya gayamata

"Rasheedu kayi shuru kabud'e baki kagayaman miye damuwarka indai kasan har cikin ranka ka d'aukeni a matsayin uwa"

"Umma dama ba wani abu bane, Illah kan maganarmu da Azraa" ya k'arasa maganar cike da nauyi da jin kunya

"kad'an k'ara hak'uri wata 'yar matsalace, insha Allah ankusa warwareta" take yafara tunanin ba wata matsala da ta wuce wannan malamin nasu Azraa, amma dan ya tabbatar yace ma Umma

"wace irin matsalace ta taso wanda har kuka shiga damuwa haka bansani ba"

"bawata matsala bace sosai, kadai k'ara hak'uri insha Azraa bata da mijin da ya wuce kai" ajiyar zuciya ya saki yace

"bakomai Umma, Allah ya shige mana gaba"... "ameen".... "Umma zankoma sai Allah yakaimu".. "Allah yatashemu lafiya" daga haka yayi hanyar zaure, jin muryar Umma da yayi tana kiran Azraa dataje ta rufe masu gida yasashi dakatawa cikin zauran, jin takun tafiyarta yasashi saurin b'oyewa bayan k'ofa, kamawa tayi da niyyar tura k'ofar ta rufe taji nunfashin mutum kasancewar zauren ba wuta, bata wani firgita ba sanin Rasheed ne saboda k'amshin turarenshi da ya fallasashi, sakin k'ofar tayi taja baya kad'an, shima ya fito ya jingina da k'ofar, wayarshi ce ya d'auko ya kunna fitila ya haska fuskarta, kallon kusan mintina biyar yayi mata don har saida ta kare fuskarta da tafin hannunta, hannunta yajanye daga fuskartata sannan yace

"Azraa bayan fitarku daga gidan Maryama ina kukaje, wanda har yad'aukeku awa d'aya da rabin sa'a?". Shuru tayi don tasan bata da amsar bashi "dake fa nake, in baki da lokacin bani amsa ink'ara gaba, kar in tsaya inb'atama kaina lokaci"

"ya Rasheed kabari zuwa gobe kazo akwai maganar da nakeso muyi dakai ta fahimta".... "uhmmm, Allah yakaimu" daga haka yasakai zaifita, ita kuma takai hannunta ga k'ofar mistakly hannuwansu suka sark'e dana juna, don har wayarshi na k'ok'arin fad'uwa, hannunshi dake rik'e da wayar yasa yakashe fitilar wayar yamayar cikin aljihu, d'ayan kuma na rik'e da hannun Azraa, kallonta yayi dukda duhu ya gauraye zauran ba sosai yake iya ganin kwayar idonta ba, ajiyar zuciya yaja yace

"ya akai ya rik'e maki hannu?, kuma kan wane dalili zaki keb'abta dashi alhali ba muharraminkiba? Shin dakukabar gidan Maryama ina kukaje?, koko dama kun saba fita irin haka?, tsawan wane lokaci kuke mu'amulla dashi?, yanzu nikeson ki amsaman basai gobe ba"

"ya Rasheed kayi hak'uri bazan iya amsa maka ko d'aya ba dare yayi, kuma Umma zataga daga rufe gida naje na zauna"

"good, bazaki iya amsawa ba ko?, kar Umma taga kindad'e, yayi kyau" daga haka yasaki hannunta, jin kamar bawani abu a hannunta yasa shi saurin kamo hannunta duka biyun, yatsunta hannunta yashiga murzawa yaji ba zoben da yabata, wanda ko d'azu yaganshi ga hannunta, a fusace yace

"Azraa!! zoben dana baki shine kika bashi?". "gidan Maryama namantashi"

"wallahi Azraa k'arya kike! k'arya kike wallahi!!, yadai rabaki dashi don yafuskanci kowa yabaki shi, kamar yadda yarabaki da wayar da yake tunani nina mallaka maki ita" daga haka yasaki hannunta ya banko mata k'ofar gidan ya wuce wanda badan tayi saurin ja baya ba sai k'ofar tayi mata rauni.

"wayyo Allah gani gareka, anya kuwa ya Rasheed zan iya rayuwar aure dakai, kishinka yayi yawa wanda har zargi na neman shigowa, wayyo ni Azraa Allah kakawo mani mafita" a can b'angaren Umma kuma jin shurun yasa tabiyo Azraa zauran, jin zantuntukan datake ne yasata dakatawa, saida tabari takai k'arshen surutun nata yasa tashiga cikin zauren

"dama halin dakike k'ok'arin jefa Rasheedu kenan?, shiyasa duk kawaici irin nashi har saida takai ya bud'i baki yayi mani magana, to nasan matakin dazan d'auka a kanki" daga haka taje ta rufe gidan tabar Azraa tsaye kamar wadda aka dasa, ganin tsawuyar bazaita mata yasata barin wurin tashigo cikin gidan

Zaune tasamu Umma tarafka tagumi, kallonta tayi cike da tausai don a rayuwarta batason taga Ummarta cikin hali na damuwa koya take, kallanta tayi cikin murya irin ta nadama in harkasan ka aikata laifi da baidace ba

"Umma kiyi hak'uri bani da wani nufi akan ya Rasheed, rashin fahimta ne yashiga tsakaninmu wanda har yakeson yadasa zargi tsakanina dashi"

"banason jin komai daga bakinki nariga dana gama yanke hukunci akanki, abinda nake umartarki dashi daga yau baki bak'ara zuwa makaranta har saina gama yanke hukunci"

"to Umma bazan k'ara zuwa ba harsai radda kika bani umarnin cigaba da zuwa" bazan tayi da'ita saima d'aki datashige tabarta nan zaune

Washe gari kamar koyaushe, Rasheed ne yayi parking k'ofar gidansu Azraa, yaro yasamu yaturo don yakira mashi ita, koda yaron isar da sak'onshi tare suka fito dashi, sallama tayi mashi bayan ya rage glass d'in motar, ya amsa

"ya Rasheed barka da safiya"... "barka, kishigo mu wuce koya hanaki shiga motata kamar yadda yarabaki da komai daya shafeni"

"ya Rasheed, Umma tadakatar da zuwa makarantata har zuwa wani lokaci"

"akan wane dalili?"... "bata gayaman ba" fitowa yayi daga motar batare da yak'ara cemata komi ba yashiga gidan, itama tabi bayanshi suka shiga tare, sallama yayi, Umma ta amsa tabashi iznin shigowa, bayan ya gaisheta yanemi dalilin miyasa ta hana Azraa zuwa makaranta, kallanshi tayi cikin tausayawa tace "Rasheedu, na dakatar da karatun Azraa har zuwa lokacin da zata zama mallakinki, albashi inyaso tak'arasa d'akinta, shine kawai abinda na yanke, don haka katashi katafi wurin aikinka karka makara" kasa tashi yayi saima langab'ar da kai yayi kamar k'aramin yaro yace

"Umma don Allah kibarta ta cigaba da zuwa makarantarta, karki ce zaki dakatarmata da karatunta, don Allah Umma badan halinmu ba"

"to shikenan naji, amma badai yau ba, katashi katafi wurin aikinka".... "to Umma sai yaushe zataje kenan?".... "Rasheedu tashi katafi wurin aikinka ranan da na shirya barinta ta sanar dakai" daga haka tashige d'aki tabarsu nan

"ya Rasheed katafi kawai bazata bari ba don yanzu, sai zuwa wani lokacin" da hannu yayi mata nuni data biyoshi waje, bin bayanshi tayi, isarsu zauren yace mata

"Azraa kan wane dalili Umma tahanaki zuwa makaranta, don nasan haka kawai bazatace bazaki ba"

"taji firar damukayi dakai jiya shine dalilin dayasa ta hanani zuwa"... "ok, in nadawo zamuyi magana"

"badamuwa, Allah yabada sa'a"....... "ameen" daga haka yatafi wurin bid'a

Maryama ce zaune cikin aji tanata tunanin miya hana Azraa zuwa har yanzu, nisawa tayi ta k'udura aranta dasun tashi daga makaranta zata wuce can gidansu Azraa danji miya hanata zuwa.......

Shiryen-Shiryen biki suka shigayi duka b'angarorin biyu, watau gidan su Aabid da Saleemah.......

*MRS ABDUL SULE*

🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*PAGE 13*

*K*wana biyu kenan rabon da yaga tazo makaranta, gashi kwata-kwata yakasa kiranta, saboda matsanan ciyar damuwar da yashiga ta sanadin auren Saleemah da ake shirin k'ak'abamai, yan zunma zaune yake cikin ofis d'inshi duk abin duniya yadameshi, kasa hak'uri yayi ya d'auki wayarshi dake saman table yashiga kiran layin Azraa, jin wayar a rufe ya k'ara jefashi cikin damuwa don yasan tabbas ba lafiya ba, kamar wanda aka tsikara ya mik'e yazari makullan motarshi yayin hanyar barin ofis d'in.

Gidansu Azraa yatasamawa cike mamakin kanshi, akan wace hujja zaije, ko-ko zaice yaga tadena zuwa makaranta shine dalilin dayasa yazo wurinta dan yaji ko lafiya, da ire-ire wannan tunanin ne harya iso k'ofar gidan nasu Azraa, parking yayi yafito ya jingina ga jikin mota, tunani ya cigaba dayi naya aika akira mashi ita ko-ko ya zaiyi, kamar daga sama ya hangi wani yaro zaishiga gidan, magana yayi mashi, yakira mashi Azraa in tana nan, koda yaron yafito yace mashi tace wanene, k'ara tura yaron yayi yace mata Malaminsu ne, gane kowaye datayi yasa tace ace mashi batanan, sallamar yaron yayi da naira d'ari biyu yace yaje ya gode

Tunani ya shigayi, donmi zata aiko tace waye daga baya kuma tace batanan, kodai tagane shine, dalilin da zaisa tace batanan.

Ganin baida wata mafita yashiga motar da zumar barin k'ofar gidan kamar daga sama yaga Maryama sunfito tare da Azraa wanda bai lura kwata-kwata da motar Maryama dake parke nesa datashi.

Maryama ce ta tab'o Azraa tace "ashe Mr Aabid ne ya aiko kiranki, shine kika ce baki nan dan rashin m. naki"

"Maryama yanzun kika gayaman shirye-shiryen bikinshi ake, don mi nizai rink'a haddasa mani fitina da wanda yake shirin zama miji gareni, alhali bawata alak'a ke tsakanina dashi"

"a'a Azraa ko kema kishinshi kike don kinji ya kusa angwancewa" tayi maganar cikin zolaya "kishi kuma Maryama?, na'aza abinda kakeso ne kawai kake kishi, amma nida bawata dangantaka tsakani na dashi kishin me zan tsayayi akanshi, sai kace wani mijina"

"kundai gama munafinci soyayyar taku kufito fili kowa yasani, ahahhh"

"keni kin isheni da hayaniya yakamata kije kiyima mijinki girki, yafi maki akan kitsaya kina wannan surutun"...... "kedai kice intafi in baku wuri kuji dad'in soyewa" banza tayi mata saima gida datayi k'ok'arin komawa, kamo hannunta Maryama tayi tace "sorry amaryar ya Rasheed, k'arasa ladarki ki rakani bakin mota mana, sannan ki gaisa da Malamin naku ki kuma yimashi Allah yasa alkhairi na auren dazaiyi nan da sati biyu"

"dan Allah muje suda sarkin surutu, wallahi ya MM na hak'uri da surutunki" murmurshi Maryama tayi tai gaba, bata zame ko ina ba sai wurin Mr Aabid, gaisheshi tayi cike da mutuntawa da kame kanta a matsayinta na matar aure kamar ko yaushe in har irin haka ta had'asu, shima cike da girmamata ya amsa sanin darajar auren dake kanta, sallama tayima Azraa ta wuce batare data saurari cewarta ba tayi gaba abinta, tabarsu nan tare da Mr Aabid, wani shu'umin kallo yajefeta dashi wanda batasan lokacin da tasadda kanta k'asa ba, don kallon ba k'aramin jefata yayi cikin wani irin shauk'i, wanda masoya kanshiga batare da sun fargaba.

"baki iya gaisuwa ba?" da kamar bazatace komai ba, saidai wata zuciyarta natason tabiye mashi taji dame yazo da har zai aika a kirata alhali ba wata hujja.

"barka da yau" abinda kawai tace mashi kenan, banza yaida ita, kafin daga bisani yace mata "bud'e mota kishigo inason magana dake"

"bazan iya shiga motarka ba"...... "ko donmi?".... "wannan ra'ayi nane" tunani yashiga yayi na kardai ace yarinyar nan tago abinda ke cikin zuciyarshu, sharewa yayi yace "to shikenan kisa mamana wurin zama inaso magana dake ne"

Gaba kawai tayi zuwa zauren gidan nasu, hakan yagane mita ke nufi yasa yafito daga cikin motarshi yabi bayanta, koda suka isa cikin zauren sun kusa shafe fiye da mintina biyar ba wanda yace komai, ganin shike nema yasa yace "wane dalili ne yasa kika dena zuwa makaranta bayan kunkusa fara jarabawa?"

"Umma ce ta hana hakan".... "kan wace hujja"...... "Sir wannan ba huruminka bane"

"ba hurumina bane?, niko nake da hurumi kansani wane dalili zaisa ki dakatar da zuwa makaranta" gani gwanda kawai ta gayamashi gaskiya shine kawai abinda zaisa ya fita hanyarta, yasa tace "aure zanyi nan da sati hud'u masu zuwa, don haka umarnin cigaba da zuwa makaranta ta yanaga hannun mijin dazan aura, inyaso zanciga, in kuma baiso ma zanbar karatun inciga da bautar Allah yadda yakamata".

Jin maganar yayi kamar zubar ruwan sama na watan Augusta, lailai tabbas in baki baisan abinda zai fad'a ba tabbas baisan mai za'a mayar mashi ba, wata irin zufa tashi keto mashi ta kowane sassa na jikinshi jin kalmar aure zatai daga bakinta, dakyar ya saita kanshi yace

*Azraaaaaaaaaaa*, *Azraaaaaaaaaaa*,
*Azraaaaaaaaaaa*, kinsan Allah komawa zaki aura zaki wahalar da zuciyarki ne kawai, domin kuwa mutum d'aya ne mallakinta, kin kuma kasa gane hakan"

"zuciyata mallakin yaya Rasheed ce don tuni muka aminta da juna, don haka banason wani dogon sharhi kan hakan"

Matsowa yayi cikin huci har yana had'ata da bango, kamo hab'arta yayi yace "ni kike gayama zuciyarkita ta Rasheed ce"...... "kai kaso kasan hakan shiyasa na fad'a" bakinta ya had'a da nashi suka zama abu guda, bakinta yashiga tsotsa cike da mugunta, jin yana neman cire mata laben, gashi yayi mata wani irin rik'o data kasa kwatar kanta ko tasaki ihun neman taimako yasa ta gantsara mashi cizo ga harshe, jin zafin cizon baisa ya sarara mata ba saima hannunshi d'aya da yasaka cikin hijabinta ya shiga murza mata mazaunanta cike da wata kalar muguntar, dakyal tayi nasarar kwatar bakinta daga nashi wanda har lab'enta sun kumbura, nunfashi ya shiga maidawa tare da k'ara murza mata mazaunanta wanda har had'awa yake da tsinkuli.

Cikin muryarta data dushe kan azabar da Aabid ke gana mata tace "kasake ni, banaso irin haka, miyasa baka d'auki abinda ba halalinka a bakin komi ba!, meyasa ka ke da sha'awar tab'a mace haka?, zakaso ace matar da zaka aura nan da sati biyu a haka tare da wani" kamar ma wanda take k'ara mashi busa, saima salon abinda yake yak'ara, ganin baida niyyar daina abinda yakeyi yasa ta tureshi cicin k'arfinta ta shige gida, tana maijamai Allah yasaka mata cikin ranta, inda Allah yataimaketa Umma batanan tayi sammakon zuwa tambuwal kan maganar aurenta da ya Rasheed nan da sati hud'u masu zuwa, d'aki ta afka harda sa sakata don karya biyota.

Dakyar Aabid ya iya jan k'afarshi yabar cikin zauran, don ba k'aramin kasalace ta taso mashi ba kan yadda yayi wasa da mazaunan Azraa, wanda laushinsu makawai abin tada hankali ne ga duk wani lafiyayyen namiji.

Sau biyu yana wuce wa tak'ofar gidansu Azraa yana ganin motar Malamin nasu Azraa, gudun karya shiga yaga abinda zaisa zuciyarshi bugawa yasa yake ta zarya, ganin yanayin da yafito ne yasa gaba d'aya hankalinshi yatashi

4 eyes sukai tsakanin Aabid da Rasheed, take Aabid yasa karmai murmushin mugunta yayi gaba abinshi, kasa d'aurewa yayi yafito daga cikin motar yafad'a gidansu Azraa...........



*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*Innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Allah ya amshi bak'unchinki Hajiya Asma'u Garba Baraya Annabi Rahama yasan da zuwanki, uwa mabada Mama 😭😭😭😭😭😭* *R.I.P Firdaus*

*PAGE 12*to14

*S*aida yayi sallar isha'e sannan yabaro masallacin, bayan yashigo gidan yatarar da Umma itama tayi tata sallar don ko sallayar bata nad'e ba, "Rasheedu kadawo?"... "eh, Umma Allah ya yarda".... "to Allah yakarb'a"... "ameen", shuru ne yaratsa wurin na 'yan wasu dak'ik'a, kafin Umma ta nunfasa tace

"Rasheedu kace akwai maganar dakakeso kayi dani, amma kayi shuru, Allah yasa dai lafiya" sunk'uyar da kai k'asa yayi yana mai k'arajin nauyin maganar da yakeso ya gayamata

"Rasheedu kayi shuru kabud'e baki kagayaman miye damuwarka indai kasan har cikin ranka ka d'aukeni a matsayin uwa"

"Umma dama ba wani abu bane, Illah kan maganarmu da Azraa" ya k'arasa maganar cike da nauyi da jin kunya

"kad'an k'ara hak'uri wata 'yar matsalace, insha Allah ankusa warwareta" take yafara tunanin ba wata matsala da ta wuce wannan malamin nasu Azraa, amma dan ya tabbatar yace ma Umma

"wace irin matsalace ta taso wanda har kuka shiga damuwa haka bansani ba"

"bawata matsala bace sosai, kadai k'ara hak'uri insha Azraa bata da mijin da ya wuce kai" ajiyar zuciya ya saki yace

"bakomai Umma, Allah ya shige mana gaba"... "ameen".... "Umma zankoma sai Allah yakaimu".. "Allah yatashemu lafiya" daga haka yayi hanyar zaure, jin muryar Umma da yayi tana kiran Azraa dataje ta rufe masu gida yasashi dakatawa cikin zauran, jin takun tafiyarta yasashi saurin b'oyewa bayan k'ofa, kamawa tayi da niyyar tura k'ofar ta rufe taji nunfashin mutum kasancewar zauren ba wuta, bata wani firgita ba sanin Rasheed ne saboda k'amshin turarenshi da ya fallasashi, sakin k'ofar tayi taja baya kad'an, shima ya fito ya jingina da k'ofar, wayarshi ce ya d'auko ya kunna fitila ya haska fuskarta, kallon kusan mintina biyar yayi mata don har saida ta kare fuskarta da tafin hannunta, hannunta yajanye daga fuskartata sannan yace

"Azraa bayan fitarku daga gidan Maryama ina kukaje, wanda har yad'aukeku awa d'aya da rabin sa'a?". Shuru tayi don tasan bata da amsar bashi "dake fa nake, in baki da lokacin bani amsa ink'ara gaba, kar in tsaya inb'atama kaina lokaci"

"ya Rasheed kabari zuwa gobe kazo akwai maganar da nakeso muyi dakai ta fahimta".... "uhmmm, Allah yakaimu" daga haka yasakai zaifita, ita kuma takai hannunta ga k'ofar mistakly hannuwansu suka sark'e dana juna, don har wayarshi na k'ok'arin fad'uwa, hannunshi dake rik'e da wayar yasa yakashe fitilar wayar yamayar cikin aljihu, d'ayan kuma na rik'e da hannun Azraa, kallonta yayi dukda duhu ya gauraye zauran ba sosai yake iya ganin kwayar idonta ba, ajiyar zuciya yaja yace

"ya akai ya rik'e maki hannu?, kuma kan wane dalili zaki keb'abta dashi alhali ba muharraminkiba? Shin dakukabar gidan Maryama ina kukaje?, koko dama kun saba fita irin haka?, tsawan wane lokaci kuke mu'amulla dashi?, yanzu nikeson ki amsaman basai gobe ba"

"ya Rasheed kayi hak'uri bazan iya amsa maka ko d'aya ba dare yayi, kuma Umma zataga daga rufe gida naje na zauna"

"good, bazaki iya amsawa ba ko?, kar Umma taga kindad'e, yayi kyau" daga haka yasaki hannunta, jin kamar bawani abu a hannunta yasa shi saurin kamo hannunta duka biyun, yatsunta hannunta yashiga murzawa yaji ba zoben da yabata, wanda ko d'azu yaganshi ga hannunta, a fusace yace

"Azraa!! zoben dana baki shine kika bashi?". "gidan Maryama namantashi"

"wallahi Azraa k'arya kike! k'arya kike wallahi!!, yadai rabaki dashi don yafuskanci kowa yabaki shi, kamar yadda yarabaki da wayar da yake tunani nina mallaka maki ita" daga haka yasaki hannunta ya banko mata k'ofar gidan ya wuce wanda badan tayi saurin ja baya ba sai k'ofar tayi mata rauni.

"wayyo Allah gani gareka, anya kuwa ya Rasheed zan iya rayuwar aure dakai, kishinka yayi yawa wanda har zargi na neman shigowa, wayyo ni Azraa Allah kakawo mani mafita" a can b'angaren Umma kuma jin shurun yasa tabiyo Azraa zauran, jin zantuntukan datake ne yasata dakatawa, saida tabari takai k'arshen surutun nata yasa tashiga cikin zauren

"dama halin dakike k'ok'arin jefa Rasheedu kenan?, shiyasa duk kawaici irin nashi har saida takai ya bud'i baki yayi mani magana, to nasan matakin dazan d'auka a kanki" daga haka taje ta rufe gidan tabar Azraa tsaye kamar wadda aka dasa, ganin tsawuyar bazaita mata yasata barin wurin tashigo cikin gidan

Zaune tasamu Umma tarafka tagumi, kallonta tayi cike da tausai don a rayuwarta batason taga Ummarta cikin hali na damuwa koya take, kallanta tayi cikin murya irin ta nadama in harkasan ka aikata laifi da baidace ba

"Umma kiyi hak'uri bani da wani nufi akan ya Rasheed, rashin fahimta ne yashiga tsakaninmu wanda har yakeson yadasa zargi tsakanina dashi"

"banason jin komai daga bakinki nariga dana gama yanke hukunci akanki, abinda nake umartarki dashi daga yau baki bak'ara zuwa makaranta har saina gama yanke hukunci"

"to Umma bazan k'ara zuwa ba harsai radda kika bani umarnin cigaba da zuwa" bazan tayi da'ita saima d'aki datashige tabarta nan zaune

Washe gari kamar koyaushe, Rasheed ne yayi parking k'ofar gidansu Azraa, yaro yasamu yaturo don yakira mashi ita, koda yaron isar da sak'onshi tare suka fito dashi, sallama tayi mashi bayan ya rage glass d'in motar, ya amsa

"ya Rasheed barka da safiya"... "barka, kishigo mu wuce koya hanaki shiga motata kamar yadda yarabaki da komai daya shafeni"

"ya Rasheed, Umma tadakatar da zuwa makarantata har zuwa wani lokaci"

"akan wane dalili?"... "bata gayaman ba" fitowa yayi daga motar batare da yak'ara cemata komi ba yashiga gidan, itama tabi bayanshi suka shiga tare, sallama yayi, Umma ta amsa tabashi iznin shigowa, bayan ya gaisheta yanemi dalilin miyasa ta hana Azraa zuwa makaranta, kallanshi tayi cikin tausayawa tace "Rasheedu, na dakatar da karatun Azraa har zuwa lokacin da zata zama mallakinki, albashi inyaso tak'arasa d'akinta, shine kawai abinda na yanke, don haka katashi katafi wurin aikinka karka makara" kasa tashi yayi saima langab'ar da kai yayi kamar k'aramin yaro yace

"Umma don Allah kibarta ta cigaba da zuwa makarantarta, karki ce zaki dakatarmata da karatunta, don Allah Umma badan halinmu ba"

"to shikenan naji, amma badai yau ba, katashi katafi wurin aikinka".... "to Umma sai yaushe zataje kenan?".... "Rasheedu tashi katafi wurin aikinka ranan da na shirya barinta ta sanar dakai" daga haka tashige d'aki tabarsu nan

"ya Rasheed katafi kawai bazata bari ba don yanzu, sai zuwa wani lokacin" da hannu yayi mata nuni data biyoshi waje, bin bayanshi tayi, isarsu zauren yace mata

"Azraa kan wane dalili Umma tahanaki zuwa makaranta, don nasan haka kawai bazatace bazaki ba"

"taji firar damukayi dakai jiya shine dalilin dayasa ta hanani zuwa"... "ok, in nadawo zamuyi magana"

"badamuwa, Allah yabada sa'a"....... "ameen" daga haka yatafi wurin bid'a

Maryama ce zaune cikin aji tanata tunanin miya hana Azraa zuwa har yanzu, nisawa tayi ta k'udura aranta dasun tashi daga makaranta zata wuce can gidansu Azraa danji miya hanata zuwa.......

Shiryen-Shiryen biki suka shigayi duka b'angarorin biyu, watau gidan su Aabid da Saleemah.......

*MRS ABDUL SULE*

🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*PAGE 13*

*K*wana biyu kenan rabon da yaga tazo makaranta, gashi kwata-kwata yakasa kiranta, saboda matsanan ciyar damuwar da yashiga ta sanadin auren Saleemah da ake shirin k'ak'abamai, yan zunma zaune yake cikin ofis d'inshi duk abin duniya yadameshi, kasa hak'uri yayi ya d'auki wayarshi dake saman table yashiga kiran layin Azraa, jin wayar a rufe ya k'ara jefashi cikin damuwa don yasan tabbas ba lafiya ba, kamar wanda aka tsikara ya mik'e yazari makullan motarshi yayin hanyar barin ofis d'in.

Gidansu Azraa yatasamawa cike mamakin kanshi, akan wace hujja zaije, ko-ko zaice yaga tadena zuwa makaranta shine dalilin dayasa yazo wurinta dan yaji ko lafiya, da ire-ire wannan tunanin ne harya iso k'ofar gidan nasu Azraa, parking yayi yafito ya jingina ga jikin mota, tunani ya cigaba dayi naya aika akira mashi ita ko-ko ya zaiyi, kamar daga sama ya hangi wani yaro zaishiga gidan, magana yayi mashi, yakira mashi Azraa in tana nan, koda yaron yafito yace mashi tace wanene, k'ara tura yaron yayi yace mata Malaminsu ne, gane kowaye datayi yasa tace ace mashi batanan, sallamar yaron yayi da naira d'ari biyu yace yaje ya gode

Tunani ya shigayi, donmi zata aiko tace waye daga baya kuma tace batanan, kodai tagane shine, dalilin da zaisa tace batanan.

Ganin baida wata mafita yashiga motar da zumar barin k'ofar gidan kamar daga sama yaga Maryama sunfito tare da Azraa wanda bai lura kwata-kwata da motar Maryama dake parke nesa datashi.

Maryama ce ta tab'o Azraa tace "ashe Mr Aabid ne ya aiko kiranki, shine kika ce baki nan dan rashin m. naki"

"Maryama yanzun kika gayaman shirye-shiryen bikinshi ake, don mi nizai rink'a haddasa mani fitina da wanda yake shirin zama miji gareni, alhali bawata alak'a ke tsakanina dashi"

"a'a Azraa ko kema kishinshi kike don kinji ya kusa angwancewa" tayi maganar cikin zolaya "kishi kuma Maryama?, na'aza abinda kakeso ne kawai kake kishi, amma nida bawata dangantaka tsakani na dashi kishin me zan tsayayi akanshi, sai kace wani mijina"

"kundai gama munafinci soyayyar taku kufito fili kowa yasani, ahahhh"

"keni kin isheni da hayaniya yakamata kije kiyima mijinki girki, yafi maki akan kitsaya kina wannan surutun"...... "kedai kice intafi in baku wuri kuji dad'in soyewa" banza tayi mata saima gida datayi k'ok'arin komawa, kamo hannunta Maryama tayi tace "sorry amaryar ya Rasheed, k'arasa ladarki ki rakani bakin mota mana, sannan ki gaisa da Malamin naku ki kuma yimashi Allah yasa alkhairi na auren dazaiyi nan da sati biyu"

"dan Allah muje suda sarkin surutu, wallahi ya MM na hak'uri da surutunki" murmurshi Maryama tayi tai gaba, bata zame ko ina ba sai wurin Mr Aabid, gaisheshi tayi cike da mutuntawa da kame kanta a matsayinta na matar aure kamar ko yaushe in har irin haka ta had'asu, shima cike da girmamata ya amsa sanin darajar auren dake kanta, sallama tayima Azraa ta wuce batare data saurari cewarta ba tayi gaba abinta, tabarsu nan tare da Mr Aabid, wani shu'umin kallo yajefeta dashi wanda batasan lokacin da tasadda kanta k'asa ba, don kallon ba k'aramin jefata yayi cikin wani irin shauk'i, wanda masoya kanshiga batare da sun fargaba.

"baki iya gaisuwa ba?" da kamar bazatace komai ba, saidai wata zuciyarta natason tabiye mashi taji dame yazo da har zai aika a kirata alhali ba wata hujja.

"barka da yau" abinda kawai tace mashi kenan, banza yaida ita, kafin daga bisani yace mata "bud'e mota kishigo inason magana dake"

"bazan iya shiga motarka ba"...... "ko donmi?".... "wannan ra'ayi nane" tunani yashiga yayi na kardai ace yarinyar nan tago abinda ke cikin zuciyarshu, sharewa yayi yace "to shikenan kisa mamana wurin zama inaso magana dake ne"

Gaba kawai tayi zuwa zauren gidan nasu, hakan yagane mita ke nufi yasa yafito daga cikin motarshi yabi bayanta, koda suka isa cikin zauren sun kusa shafe fiye da mintina biyar ba wanda yace komai, ganin shike nema yasa yace "wane dalili ne yasa kika dena zuwa makaranta bayan kunkusa fara jarabawa?"

"Umma ce ta hana hakan".... "kan wace hujja"...... "Sir wannan ba huruminka bane"

"ba hurumina bane?, niko nake da hurumi kansani wane dalili zaisa ki dakatar da zuwa makaranta" gani gwanda kawai ta gayamashi gaskiya shine kawai abinda zaisa ya fita hanyarta, yasa tace "aure zanyi nan da sati hud'u masu zuwa, don haka umarnin cigaba da zuwa makaranta ta yanaga hannun mijin dazan aura, inyaso zanciga, in kuma baiso ma zanbar karatun inciga da bautar Allah yadda yakamata".

Jin maganar yayi kamar zubar ruwan sama na watan Augusta, lailai tabbas in baki baisan abinda zai fad'a ba tabbas baisan mai za'a mayar mashi ba, wata irin zufa tashi keto mashi ta kowane sassa na jikinshi jin kalmar aure zatai daga bakinta, dakyar ya saita kanshi yace

*Azraaaaaaaaaaa*, *Azraaaaaaaaaaa*,
*Azraaaaaaaaaaa*, kinsan Allah komawa zaki aura zaki wahalar da zuciyarki ne kawai, domin kuwa mutum d'aya ne mallakinta, kin kuma kasa gane hakan"

"zuciyata mallakin yaya Rasheed ce don tuni muka aminta da juna, don haka banason wani dogon sharhi kan hakan"

Matsowa yayi cikin huci har yana had'ata da bango, kamo hab'arta yayi yace "ni kike gayama zuciyarkita ta Rasheed ce"...... "kai kaso kasan hakan shiyasa na fad'a" bakinta ya had'a da nashi suka zama abu guda, bakinta yashiga tsotsa cike da mugunta, jin yana neman cire mata laben, gashi yayi mata wani irin rik'o data kasa kwatar kanta ko tasaki ihun neman taimako yasa ta gantsara mashi cizo ga harshe, jin zafin cizon baisa ya sarara mata ba saima hannunshi d'aya da yasaka cikin hijabinta ya shiga murza mata mazaunanta cike da wata kalar muguntar, dakyal tayi nasarar kwatar bakinta daga nashi wanda har lab'enta sun kumbura, nunfashi ya shiga maidawa tare da k'ara murza mata mazaunanta wanda har had'awa yake da tsinkuli.

Cikin muryarta data dushe kan azabar da Aabid ke gana mata tace "kasake ni, banaso irin haka, miyasa baka d'auki abinda ba halalinka a bakin komi ba!, meyasa ka ke da sha'awar tab'a mace haka?, zakaso ace matar da zaka aura nan da sati biyu a haka tare da wani" kamar ma wanda take k'ara mashi busa, saima salon abinda yake yak'ara, ganin baida niyyar daina abinda yakeyi yasa ta tureshi cicin k'arfinta ta shige gida, tana maijamai Allah yasaka mata cikin ranta, inda Allah yataimaketa Umma batanan tayi sammakon zuwa tambuwal kan maganar aurenta da ya Rasheed nan da sati hud'u masu zuwa, d'aki ta afka harda sa sakata don karya biyota.

Dakyar Aabid ya iya jan k'afarshi yabar cikin zauran, don ba k'aramin kasalace ta taso mashi ba kan yadda yayi wasa da mazaunan Azraa, wanda laushinsu makawai abin tada hankali ne ga duk wani lafiyayyen namiji.

Sau biyu yana wuce wa tak'ofar gidansu Azraa yana ganin motar Malamin nasu Azraa, gudun karya shiga yaga abinda zaisa zuciyarshi bugawa yasa yake ta zarya, ganin yanayin da yafito ne yasa gaba d'aya hankalinshi yatashi

4 eyes sukai tsakanin Aabid da Rasheed, take Aabid yasa karmai murmushin mugunta yayi gaba abinshi, kasa d'aurewa yayi yafito daga cikin motar yafad'a gidansu Azraa...........



*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*PAGE 14*

*K*ada yashiga gidan ya iske tarufe k'ofar d'akin, bugawa yayi batare da yayi magana ba sanin Umma yau bata gidan, don tunjiya ta sanardashi zata tambuwal, jin bata bud'e k'ofar ba yasa ya cigaba da bugawa ba k'auk'autawa, wanda ita kuma Azraa a tunaninta ko Mr Aabid ne, banza tayi dashi ta kyaleshi, ganin bazai daina bugawa ba yasa tayi niyyar bud'ewa, gudun kar hankalin mok'ota yadawo kansu, jin yadda ake buga k'ofar da k'arfi.

Bud'ewarta kenan taga ya Rasheed tsaye, fuskar nan tashi kamar baitab'a dariya ba, kallanta yayi shek'ek'e yace "menene dalilin dazaisa ki rufe k'ofa, da rana k'iri-k'iri?"

"haka nan na rufe" kallonshi yakai ga bakinta dake furta haka nan, "me kuma ya kumbura maki leb'e haka?" kwallo idanuwa tayi tace "d'azu ne na buge da bango" dariyar rainin wayo yayi mata wanda zamu iya kiranta data yak'e, yace "ko kuma bak'onki da yafita yanzu ya bugeki ba" kasa ce mashi komi tayi saima d'akin data koma, girgiza kai yayi yabar gidan don yasan komai zai'iya faruwa inya matsa mata jin sanin miye musabbabin kumburin bakin nata.

***

Bayan kwana ukku, Alhaji Abdallah ne zaune cikin k'ayataccen palournshi, da yaji kayan alatu na more rayuwar duniya, yana amsa wayar aminin nashi, watau mahaifin Saleemah, daga can b'angaran mahaifin na Saleemah ke k'ara tunasar mashi da lailai Aabid zaibar Saleemah tacigaba da karatunta bayan sunyi aure, data keyi a k'asar bangaladash, wanda dama da wannan yarjejeniya ce mahaifin Aabid ya aminta da auren had'in da yake sonyi, wanda shi Alhaji Abdallah baiyi shawara da d'an nashi ba ko jin menene ra'ayinshi kan cigaban karatun matarshi zuwa wata k'asa, ko shawara da mahaifiyar Aabid kafin ya zartar da hukunci, nisawa yayi yace

"gaskiya bariga dana sanarda Aabid d'in ba kan cigaban karatun nata, ganin samarin zamani sunfi son auren mace wayayya shiyasa na dogara da hakan, insha Allah nasan bazai bamu wata matsala ba"

"ka sanardashi d'in nada kyau, don kasan yaran yanzu ka haifesune baka haifi halinsu ba, kar daga baya a d'aura aure yazo yace baisan zancen ba, wanda ni kuma bazan laminci hakan ba"

Nisawa yayi yace "zan sanardashi"..... "to dadai yafi" haka suka k'arasa wayar ba cikin jindad'i ba

Azraa zaune tana gyarama Ummartata zogale, yayin da Umma ke gyara tsakin masarar da zasuyi dambun dashi, Umma ce takallo sashen da Azraa ke aiki tace "dangin mahaifinki sunyi rawar gani, akan hidimar auren nan naki domin ku suntara maki kud'i ki mani naira dubu d'ari da hamsin, wanda zamuyi hidimar bikin dashi, haka nima na saida wata gonata akan naira dubu d'ari, kinga in an had'a da kud'in wurin dangin mahaifin naki da nawa sun zama dubu d'ari biyu da hamsin kenan, wanfa nasan zamu sayi abubuwa masu mahimmanci dasu"

"to Umma masha, Allah yasa masu albarka"

"ameen Azraa, yanzu abinda nakeso dake kiyima Maryama magana kuje kasuwa kunemi kaya masu rangwamen sauk'i kusaya, tunda da wuya musamu kud'i nan gaba masu yawa kamar wa in nan"

"to Umma kamar me zamu saya".... "kusayi gado da labiyaye sai 'yan kayan kitchen da dai sauran kayan buk'ata na yau da kullum"

"shikenan Umma zuwa anjima zanje gidan Maryama don muji yadda za'ayi" daga haka suka cigaba da shirye-shiryen, d'aura dambun masarar nasu.

Zaune Aabid yake gaban mahaifin nashi yana mashi bayani akan bayan aurenshi da Saleemah zaibarta ta cigaba da karatunta data keyi a k'asar bangaladash,

"Daddy, dan Allah kayi hak'uri bazan iya barin iyalina ta tafi wata k'asa da sunan karatu"

"Aabid kallan ni dakyau, umarni nake baka bawai neman shawara, kaji nagaya ma"

"to shikenan Daddy Allah yabata sa'ar karatu" daga haka ya fita yabar gidan, zuciyarshi cike da damuwa, na yama za'ai ace kai kana nan matarka na wata uwa duniya daban da sunan tana karatu, duk makarantun dake fad'in Najeriya ace bazata samu d'aya tayi ba.

wayarshi ya d'auka ya shiga kiran layin Azraa domin ita kawai zaigani ko yaji muryarta yaji sauk'in damuwar da yake ciki, sallamarta tace da doki dodon kunnanshi, saida ya lumshe idanu nawani sakannin kafin ya bud'e, amsa sallamar datayi yayi ya cigaba da cewa

"kina ina ne nakejin hayaniya haka?".... "badamuwarka bace" murmushi yayi kamar tana ganinshi yace "Azraa kin rainani da yawa, amma na kusa maganin wannan rashin kunyar taki very soon"

"miye damuwarka da kake kirana, irin wannan lokacin"

"Azraa kina ina?"..... "kasuwa"....... "miye kikaje saye" dariya tasaki kafin tace "kayan aurena nida *Habibi Da'iman* d'ina" yaji haushin habibi da'iman data kira, dan yasan Rasheed take nufi ba kowa ba, dakewa kawai yayi yace "amma kinsan tsarin kalolin da nakeso a gidana yakasance dashi" wayar tacire daga kunnenta dan ta k'ara tantance waya kirata "kinji abinda nace ko saina k'ara maimai tamaki" kashe wayar kawai tayi gaba d'aya tajefa jikka, don bata da lokacinshi yanzu.

Maryama ce tace "Mr Aabid ne ko?".... "kamar kinsani" daga haka ta cigaba da jawo wasu food warmers don ta shiriritar da maganar don kwata-kwata al'amurran Mr Aabid na bata tsoro.

Ganin Azraa ta share da maganar yasa Maryama tasama bakin salatin nata kwad'o suka cigaba da hudimar data kawosu.

Jin takashe wayar gaba d'aya ya k'ara tunzurashi, donmi zata kashe mai waya don tana sayen kayan aurenta da wani banza, kwafa yayi ya ayyana aranshi shi kad'ai yasan abinda zaimata in har suka had'e.

Tunda suka fita wajejen k'arfe sha biyu basu dawo ba sai wuraren biyar da wani abu, dakaya nik'i-nik'i dasuka sawo daga kasuwa, Maryama bata wani zauna ba tayima Umma sallama ta tafi gida, da niyyar gobe zata dawo kan suyima Umma bayanin duk abinda suka sawo.

Bayan yayi sallar issha'eh ya wuce gidansu Azraa, kiran wayarta yayi yajita akashe, yaro ya tura yakira mashi ita, bayan kamar mintina bakwai sai gata tafito, zaure wannan karanma ya bita suka shiga don yasan halinta na bata shiga cikin mota da sunan zance bare yanzu da duhu yafara, bayan sun gaisane yace mata

"Azraa inason ki k'ara maimaita mani abinda kika ce dazu" yayi maganar cike da rashin son wasa "meko nace, cewa nayi naje sayayyan kayan aurena, koda wani abu baya ga haka"

Fisgota yayi tafad'o jikinshi, wata irin runguma yayi mata yana k'ok'arin cire mata abayar dake sanye jikinta, jin takun tafiyar mutum zaishigo ne yasa yayi saurin ida cire mata abayar, bakinshi ya had'e danata yashiga tsotsa kamar yasamu sweet, kallo d'aya Rasheed yayi masu ya kauda fuskarshi, wanda Aabid yana halkance da yanayin da Rasheed ya shiga, gashin kanta yashiga yamutsawa kasancewar ba kallabi kanta kuma gashi bakitso ne akanta ba shine yabashi damar tura hannunshi cikin gashin kanta yana wasa dashi yadda yakeso, baisan lokacin da wasu zafafan hawaye suka shiga zuboma Rasheed ba, dafe saitin da zuciyarshi yake yafita, wulgawar mutum kawai tagani yafita, kuma tana da tabbacin Rasheed ne domin irin wannan time d'in ne lokacin zuwanshi.

Ganin yafita dafe da zuciyarshi yasashi sakin Azraa, abayarta da ya yadda yasa mata, d'ago idanunta tayi da sukai jawur kamar garwashin wuta don b'acin rai, tace

"burinka ya cika, kuma sai Allah yasaka man kan zargin da kake ta k'ok'arin kaga ka haddasashi tsakanina da ya Rasheed"

"zargi ni bawani zargi danake haddasawa a tsakaninku, illa ina nuna mashi daya kyale matar daba tashiba, dafatan kin fahimta"

"niko na fahimta, tunda kana k'ok'arin wargaza soyayyar da aka gina kan turba maikyau, kana neman haddasa zargi maik'arfi a tsakani"

"ni banga wani zargi anan ba,kuma Azraa k'arya kike kice bakisan halin da zuciyoyinmu suke ciki ba, yakamata mudaina wasan b'uyen nan haka nan kinji mufito fili mu nemama kanmu mafita, domin daga ni har ke muna cikin damuwa"

"wasan b'uya fa kace! kaidawa kuke wasan b'uyan? ina fata badai dani Azraa ba, balle har kayi tunanin ina cikin damuwa, damuwata d'aya yanzu ya Rasheed yace yafasa aure na kan wannan abun daya gani toshine babba tashin hankalina, dan Allah kad'ai yasan wane hali zanshiga kan rashinshi"

Murmushi yasaki yace "kar in k'arajin sunan Rasheed a bakinki daga yau" tare da had'e hannunwata waje d'aya yanaja da k'arfi

Ringing d'in wayarshi ne yasa yasaki hannuwan nata ya d'auki wayar, a handsfree yasa wayar kasancewar baisan mai number barba, da dafarko ma kamar bazai d'auka ba, amma wata zuciyar tace ya d'auka komai kiran yanason wani taimakon gaggawa gareshi, murya mace yaji tana rangad'amai "Mijina uban 'ya'ya barka da yau" tabbas ya gane murya Saleemah ce, amma dukda haka yace

"bangane wake magana ba"... "Saleemah ce" abinda ta sanar dashi kenan. "ok, Saleemah yakike"

"lafiya lau, dama nakira in shaida maka cewa zuwa gobe inason ganinka akwai wani shirye-shirye dana keson mutsara dakai"

"badamuwa" daga haka kawai yadatse kiran, ganin yagama wayar yasata nufar cikin gida, cike da mamakin rainin wayon irin na Aabid, nadan mi zairabata da masoyinta, shi kuma yana nashishirye-shiryen aure, jitayi ya juyo da hab'arta suna kallon juna, "baisan lameki ba danmi zaki taf"

"Sir Aabid ka fita harkata kaji, kaje kaji da hidimar dake gabanka, nima inji datawa" daga haka ta fizge ta shige gida.

Rasheed ko ikon Allah ne kawai yakaishi gida, yana zuwa dai-dai k'ofar palourn gidan ya....

*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*PAGE 15*

*MARYAM MK*
*RUKAYYA ALIYU(BOSHOSHUWA)*
*HUSSY AHMED DIKKO*
πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»

*"A*zraa na amince maki da cigaban karatunki, tunda anriga da an tsaida ranan bikin, alabarshi sai kiyi taka tsan-tsan da rayuwarki ki kuma sa tsoron Allah cikin lamurranki, kinji na gaya maki"

"to Umma insha Allah zan kiyaye" daga haka suka cigaba da hidimominsu na yau da kullum

Washe gari tunda safe tayi shirinta na zuwa makaranta, bayan tasaka k'atuwar abayarta takawo nik'ab tasa, sanin Rasheed baisan Umma tabarta ta cigaba da zuwa makaranta ba yasa bata tsaya jiranshi ba ta nufi bakin titi tasamu abun hawa (taxi)

Tun ranan da yabar gidansu Azraa yakamu da wani irin ciwon kai da jiri, wanda ko wurin aiki yadaina zuwa, tunda yasanar dasu bashi da lafiya, wanda ita Hajiyarshi yakasa sanarmata halin da yake ciki, bayanshi a ranshi ya k'udirti niyyar in har Azraa ce autar mata ya hak'ura da'ita koda son da yake mata shine ajalinshi ya hak'ura da'ita, dan bazai iya auren macen da tarabarma guys kanta a waje ba.

Koda tashiga makarantar da motar Maryama tafara cikin karo a bakin get, glass d'in motar Maryama tasauke tace "Hajiyar nik'ab shigo in k'arasa dake" wanda duba d'aya Maryama tayima Azraa tagane cewar itace ganin yanayin natsuwarta da kuma tafiyarta, batayi musu ba ta bud'e gaban motar tashiga

"ya akai kika gane ni duk basajar danai" cewar Azraa bayan tashiga motar

"yanayin tafiyar yasa nagane, kice Umma tabari ki cigaba da zuwa makarantar kenan?"

"eh, jiya muna zaune tace na shirya na cigaba da zuwa makaranta ta, tunda an tsaida ranan bikin"

Daga haka suka k'arasa parking lot d'in cikin makarantar.

Maryama ce takai dubanta ga Azraa tace "yau ko a sa'a kika shigo makarantar nan danko mutunenki shine wanda zaifara bamu darasin yau"

Yatsina fuska tayi tace "ina abinda yadame ni dashi".... "mudai namu ido" cewar Maryama da suka k'arasa shiga aji, basuyi wani dogon zama ba Mr Aabid ya shigo, kallanshi yakai inda mai nik'ab take zaune, ya gane cewar Azraa ce, darasinshi ya cigaba dayi, wanda Azraa ko in banda harara ba abinda take banka mai tacikin nik'ab.

Bayan ya fita daga ajin nasu yakira layin Azraa tana ringing amma bata d'auka ba, sak'o ya turama mata ta sameshi ofis d'inshi, tura mashi amsa tayi da batazo school ba, k'ara kiranta yayi still bata d'auka ba, k'ara dialling number yayi a karo na biyar.


Jin zaidameta ne yasa tad'aga kiran "hello" abinda kawai tace mashi tayi shuru "nasan kinzo makaranta, komi kike ki sameni ofis right now" tare da datse kiran

Jinjina iko irin na Aabid tayi tace "Aiko yau zanshayar dakai ruwan mamaki, dan baka isa kasani zuwa ba dan bakai ka kawo ni makarantar ba" wanda tayi maganar ne a fili har Maryama na jiyota

"Mr Aabid, ko?" cewar Maryama "shimana ya hanama rayuwata sak'at, duk wani motsi na akan idonshi, dalilinshi ne yasa nasa nik'ab amma dukda haka bantsira ba"

Bayan kamar mintina goma baiga tazo ba yasake kiran layin nata "Azraa bakiji menace maki ba"..... "ba haka yakawo ni makarantar ba" tare da kashe wayar baki d'aya danma karya k'ara kiranta, kwafa yayi bayan yasake kira yaji kashe yace "zamu had'une"

Shuru-shuru ba Rasheed ba labarinsa, Umma duk tabi tadamu, takuma rasa dalilin dayasa yadaina zuwa, itama Azraa bak'aramin tada mata hankali rashin zuwanshi yayi ba musamman sanin musabbabin abinda ya hanashi zuwa, kasa daurewa Umma tayi tace ma Azraa "lafiya, Rasheedu kwana biyu baizo ba, ko wata tsiyar kika k'ara haddasa mai wanda har yayi fushi haka?"

"Umma bawani abu da naimashi k'ila hidimomine sukasha kanshi kila shine dalilin da ya hanashi zuwa" cikintako in baya ga k'ulululululu ba abinda yakeyi dan tana jin tsoro Umma tagano wani abu ya k'ara had'asu.

"to Allah yasa da gaske kike dan ni yanzu lamurranki tsoro suke bani"

Umma na gama sallar ishsha'eh ko Abayar bata cireba tace ma Azraa tayi gidansu Hajiya Rasheedu, addu'a tashiga yi na kar Allah yasa Umma ta iske ya Rasheed gida, wanda a fili tace "Umma ko inzo in rakaki?".... "kiyi zamanki nima ba dad'ewa zanba" bayan fitar Umma dakamar mintina goma yaro yayi sallama yace ana kiran Azraa waje, duk a zatonta ya Rasheed ne ya aiko kiranta ganin Umma na gidansu yasa yak'i shigowa cikin gidan, "kace ina zuwa" tagayama yaron.

K'amshin turaren hot ne ya gwauraye zauren, take tagane ba Rasheed bane don ko ba irin turarenshi bane, saurin juyawa tayi da niyyar shigewa gida, ganin tana shirin guduwa yasa ya rik'e mata abaya ta baya.

Jin yashak'eta da abayar yasa tayi saurin cirewa, kama hannunta yayi yadawo da ita cikin zauren, "sakanman hannu"

Wasa yashiga yi da yatsun hannun nata, saurin fizge hannun nata tayi tace "ina garga d'inka da babba murya kada ka kuskura hannunka ya k'ara kaiwa ga jikina" murmushi kawai yayi yace "i promise bazan sake kai hannuna ga jikinkiba, saidai in naga abinda zai cutar mani dake shine bazan iya hak'ura ba sai jikina yakai ganaki" shuru ne ya ratsa wurin, kafin daga bisa ni Aabid yace "nakira d'azu kik'i zuwa, komi yasa?"

"saboda ba abinda yakaini makarantar ba kenan".... "nasan da haka da saikizo kiji miye uzuri na"

"ai yanzu gashi uzurin naka yakawo ka, sai kafad'a inji" murmushi yayi yace "Azraa meye mafita?"

"mafita ka ke nema, ko yaya?" matsowa yak'arayi yace "miyasa kike son a zabtar da ruhinmu, why!, bayan kinsa halin da muke ciki"

"kaga Sir Aabid ka rabu dani kaje kaji da abinda ke gabanka, bawai ka tsaya b'atama kanka lokaci, kaga shigewata inada abinyi" fizgota yayi ta fad'a bisa fad'add'en k'irjinshi, wata sanyaryar ajiyar zuciya suka saki lokaci d'aya, sunkusa shafe mintina ukku a haka, kafin ta raba jikinta danashi, jingina yayi da bango ya k'ura mata ido "Azraa sonki na a zabtar da ruhina bantab'a son wani abu kamar yadda nake sonki, inkika d'ebe Allah da manzonsa, da kuma mahaifana, kece wadda ke rufa masu baya cikin zuciyatah"

Dai-dai lokaci da Rasheed ya sako kai zai shigo gidan, yaji maganar cikin dodon kunnenshi, Umma ko da yarako mutuwar tsaye ce takamata jin furucin da Aabid yayi alhali ta tsayarma da 'yarta miji.

Sallamar k'arfin hali Rasheed yayi, Umma ko kasa cewa komi tayi ta rab'e ta gefensu zata wuce, "Umma ina wuni" cewar Aabid juyowa tayi ta kalleshi na d'an wani dak'ik'a, kwarji yayi mata sosai wanda yahata kasa amsa gaisuwar dayayi mata, amsa tayi tashige gida, Rasheed na biye a bayanta.

"Umma tunda nakawoki gida bari na wuce, dare na k'arayi"....... "Rasheedu kayi hak'uri da abinda kagani, d'an yau ne ka haifeshine baka haifi halinshi ba, saboda haka yasa kwanaki baya na hanata zuwa makaranta"

"Umma ba komi, bari inkoma sai Allah yakaimu".... "Allah yakaimu Rasheedu, Allah yayi maka albarka".... "ameen Umma" daga haka yatashi ya nufi zaure, lokacin Azraa in baya ga kukan zuci ba abinda takeyi.

Wuce kawai yayi batare da ya ko kalli inda suke ba, don shi kad'ai yasan abinda yakeji cikin ranshi, yayinda kunnuwanshi ke amsa kuwar k'arajin furucin Aabid cikinsu.

"Sir Aabid burinka ya cika yau karabani da mutane mafi daraja gareni" murmushin gefen baki yasaki yace "Azraa ki rubuta ki aje baki da mijin da ya wuce ni Aabid, any way zakiji shuru na kwana biyu saboda shirye-shiryen da suka sakoni gaba, in komi yazama normal zakiji ni, but inaso yakasance koda yaushe wayarki a kunne, nabarki lafiya *My Heart Con*". yana kai k'arshen zanceshi ya fuce yabar gidan.
yabarta nan tsaye kamar wadda aka dasa.

"Allah ka kawo mani mafita" cewar Azraa tare da rufe gidan, tunanin yadda zasu k'are da Umma ta shigayi, don tasan mai rabata da'ita sai Allah, dakyar ta taimakon innalillahi tayi namijin k'ok'arin shiga gidan, bata tarar da Umma tsakar gidan yasa ta d'auki buta sai makewayi dan bak'aramin hautsinawa cikinta yayi ba..........

*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*```KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*```
®
*```HALIMA MK*```

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*```PAGE 16*```

*K*oda ta fito daga makewayi, k'in shiga d'akin tai, tsayuwar tayi nan waje kamar wata munafuka, "kishigo magana zanyi dake in kingama tsayuwar munafuncin taki" cewar Umma datayi maganar daga cikin d'aki.

K'undun balar mazuru tayi tashiga cikin d'akin, kallan banza Umma ta bita dashi kafin ta rufeta da fad'a tana cewa "dama shegantakar da kike shukama Rasheedu kenan, ko dan kinga Allah ya jarabeshi da sonki yasa kike mashi wannan iskanci, yaushe ne yaro yana dakon sonki shekara da shekaru yana bauta maki, amma rana d'aya wani ya ganki da hak'oranki talatin ba d'aya yace yana sonki har ki yarda ki aminta dashi dan sakarci irin naku na yaran zamani wanda basa gane masoya na gaskiya"

Nunfasawa Umma tayi domin har haki take kan b'ab'atun fad'a, bayanta nisa ta cigaba da cewa "yanzu na ganoki ashe shiyasa kika kori Rasheedu dan kinga wanda yafishi ko gaki ke sarauniyar kyau wadda maza ke rubibi, to kibud'e kunnanki da kyau ki saurare ni sati mai zuwa za'a d'aura aurenki da Rasheedu kowama ya huta" haka Umma ta cigaba da yimata fad'a, ga bakinta dake kunfa kamar ta ari baki, don masifa, shuru dai Azraa tayi saida ta tabbatar data gaji don kanta sannan ta bud'e baki tace

"Umma Allah yabaki hak'uri, abinda kike tunani ba haka bane, rashin fahimta ce kawai irin ta yaya Rasheed da kuma kishi dayasa ma ranshi, wanda har zargina yake muna wata mu'amullar banza da wanda kukazo kuka tarar damu tare"

Kalmar zargi data ambata Rasheed namata kwata-kwata Umma bataji dad'in taba, donko ko auren mutum kayi yana zarginka to haramun ne auran naku, balle ace baka riga da kashiga gidan ba, amma dan karta bata damar da zata kafa hujja akan gujema auren Rasheedun, dukda tasan bawai dan ya kwanta ma Azraa arai bane, yasa tace mata

"kunyi abinda zaisa ya zargeku ne shiyasa, in ba dan haka ba bazaice yana zarginku da wata mu'amala marar kyau ba"

"Umma wallahi ni ba wata mu'amalar banza data tab'a shiga tsakanina dashi, bamashi kad'ai ba duk wani d'a namiji dake fad'in duniyar nan"

"wannan kuma rayuwarki, don kowai nagari dan kanshi, aure bafashi sati mai zuwa, koda kayan d'aki ko babu sai anyishi, kintafi da abinda ya sauwak'a gareki, kuma sannan duk randa na k'ara ganin wannan shegen yaron gidan nan dagake harshi saina fasa maku k'auri, don mabugi zansa na jemeku"

"Umma Allah ya huci zuciyarki"... "sai shegen dad'in baki kamar matar na tuba" sadda kanta k'asa Azraa tayi don tasan bak'aramin bata ran Umma tayi ba, ga damuwarta kar hawan jinin Umma nata yatashi, shiyasa duk abinda tace take binta da to, don ta kwantar mata da hankali.

Washe gari dukda zuciyarshi na cike da tsanar abinda Azraa tayi mashi baisa yafasa zuwa kaita makaranta tunda Umma ta sanar dashi, bayan ya shiga sun gaisa da Umma take k'ara bashi hak'uri kan sha'anin yaro, da kuma yimashi albishir sati mai zuwa ne d'aurin aure, tare da shaida mashi sadaki kawai takeso daga gareshi, sadda kai k'asa yayi yace

"Umma a daibarshi harzuwa lokacin da akasa" jinjina maganar Umma tayi tace "Allah yakaimu" daga haka Rasheed ya kalli Azraa yace "in kinshirya zuwa makaranta muje na saukeki" sallama tayima Umma suka tafi, wanda Umma jikinta yayi sanyi kan wannan lamarin dake neman kunno mata kai, tare da hasashen kodai dagaske ne Azraa maza take bi a waje wanda harya haddasa k'in amincewar aurenta da Rasheedu ya kesonyi, saurin istigifari tayi tace "ka kyautata kyakykyawan zato ga kowa" daga haka ta tashi ta cigaba da safgoginta

Koda suka baro gidan Umma ba wanda yace k'ala, wani tunani ne ya darsu a ranshi yasa yace mata

"Uncle Abullahi (k'anene ga mahaifinshi) suna san suje tambuwal, kan janye maganar aurena dake danayi, dan haka ki sanar da Umma"

Wasu hawaye ne suka zubo mata, wanda bata shiryama zuwansu ba, kallon mamaki tayi mashi tace "ya Rasheed kajanye maganar aure na dakai!?"

"eh, hakan ne maslaha tsakani na dake" kuka ta cigaba dayi marar sauti, ajiyar zuciya tasaki tace "Allah yasa haka yazame mana alkhairi, ya kuma baka matar da tafini komai, har abada bazan tab'a manta alkhairinka gareni ba" tana maganar tana kuka haik'an

Shima hawayen ya shiga sharewa, dukda yasan rabuwa da Azraa ba abune mai sauk'i gareshi ba, amma yana ganin hakan ne mafita gareshi dan tun farko ta nuna bata ra'ayinshi, biyayya ce kawai yasa take kulashi.

Ajiyar zuciya ce kawai take saki lokaci-lokaci, da tunanin wane irin hukunci Umma zata yanke akan aurenta da ya Rasheed yake shirin gujemawa.

Koda suka iso, har tabud'e k'ofar motar zata fita yace mata "Karki d'auka nadena sonki yasa nai maki haka, a'a nayi ne dan bazan iya tarayyar aure tsakani na dake ba koda munyi aure, saboda wasu hujjoji dana gani daga gareki keda Malaminku"

"na fahimceka yaya Rasheed, nasan kanayi mani kallon wanda take hudd'a da maza a waje, saboda kishi daya rufe maka ido, bakomi Allah shine shaidata, ina maka fatan Allah yabaka mace tagari kamillaliya wanda ba irina ba wanda kakema kallon mutuniyar banza, kuma bazan gaji da k'ara gode maka kan kulawar dakake bamu nida mahaifiya ta Allah ya biyaka da alkhairansa, bissalam" tana kai nan wani irin kuka ne yazoma ta, bud'e k'ofar motar ta nufi hanyar barin makarantar dan tasan kota zauna ba wani abin kirki da zata tsinanama kanta, ganin tayi hanyar barin makarantar yasa yafito daga cikin motar shima.

"ina zaki ne?"... "zankoma gida" daga haka tayi tafiyarta tabarshi nan sake da baki.

*

"Ango Saleemah bada kanka a sare kaje gida kace ya fad'i" cewar MM da suke zaune palourn gidan MM d'in

"kaini ba wannan bace damuwata, Azraa ce damuwata narasa taya zan b'ulloma wannan lamarin"

"hak'uri shine kawai abinda zakai, domin ko ko giyar wake kasha bazaka tunkari Daddy da wannan maganar ba, musamman na sanin ak'idarshi na baison had'a jini da talaka"

"ak'idar banza, dai kawai tunda ba fad'ar ```Allah``` da ```Manzosa``` bace kawai ra'ayi ne irin nashi, wanda ba inda akace maikud'i karya auri talaka"

"kuma kaima banda abinka Aabid yarinyar nan takusa aure, baikamata ace kayi neman aure cikin nema ba, wannan haramun ne" murmushi gefen baki Aabid yasaki yace

"ka rubuta ka'aje Azraa bata da mijin da ya wuce ni Aabid, dan na k'afa hujojin da sai sakaran namiji zai'iya aurenta, balle wannan sarkin mahaukacin kishi wanda baya iya b'oyeshi sai yafidda k'arara kowa ya gane weak point d'inshi"

"Aabid badai yarinyar mutane ka farka ba!?" MM yayi maganar cikin k'araji, dariya Aabid yayi yace "meye na wani razana, abinda kake tunani bane nayimata"

"to mekayi mata?"..... "sirrine" tare da kashe mai ido d'aya ya mik'e, sallama yayi mashi ya tafi

*

Fushi sosai Umma tashiga yi da Azraa, tun lokacin da Rasheed ya janye maganar aurensu, wanda bak'aramin tadama Azraa hankali yayi ba, duk tabi tayi wani iri da'ita, gashi wanda hakan tafaru dominshi yana can yana shirye-shiryen nashi auran ita kuma yabarta cikin tashi hankali.

As usual yau ma yazo kaita makaranta, bayan ta gaisheshi, daga haka suka cigaba da zaman kurame, bayan sunyi parking, Aabid yayi parking tashi don har yana blocking motar Rasheed ta bayadda za'ai ya wuce batare da Aabid ya cire tashi ba, shikuwa sauri ne yake ya d'auko wani abu a ofis d'inshi shine dalilin dayasa bai kula da yanayi parking da yayi

Fitowa Rasheed yayi daga cikin motarshi, wanda har Mr Aabid ya wuce dan bai kula dasu Rasheed d'in ba, kallan Azraa yayi da shanyanyun idonshi yace "saurayinki yayi blocking d'ina, yake nan gashi ina sauri zan wuce ofis kozaki taimaka ki kirashi ya janye in wuce" shuru tayi ta kyaleshi kamar bada ita yake ba.

"Azraa maganafa nake kinajina kinyi shuru"... "ya Rasheed mekakeson nace maka"

"sonake kije ki kirashi" dawowar Mr Aabid ne yasa Rasheed komawa cikin mota, Azraa ko gaba kawai ta k'ara.

Harara Aabid ya bankama mota Rasheed yaja tashi yayi gaba..............

*```MRS ABDUL SULE*```
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊





©
KAINUWA WRITERS ASS✍🏻
®
*HALIMA MK*






*WHERE ARE YOU,*
*FIDDOH SODANGI*
*WANNAN SHAFIN DAMARKI CE, MK NA GODIYA, ALLAH YABARMU TARE, 'YAR MUTAM KATSINAWA*






*PAGE 17*





*K*oda Mr Aabid ya janye motarshi, Rasheed yafin k'arfin mintina biyar zaune cikin mota, kafin daga bisani yaja motarshi yabar cikin makarantar.






Driving yake, amma hankalinshi naga Rasheed da yasauke Azraa, ji yake kamar zuciyarshi ta faso k'irjinshi ta fito, ganin yadda har yanzu Rasheed ya kasa rabuwa da Azraa duk irin abubuwan dayake mata a gabanshi wanda zai haddasa masu zargi a tsakaninsu, amma sun gaza rabuwa, k'uta yayi ya ayyana wani abu a ranshi wanda yake ganin tabbas ya aiwatar dashi to lailai ba Azraa ba Rasheed, danko yasan saisun rabu, rabuwa ta har abada, irin yadda ya fuskanci kishin Rasheed bamai sauk'i bane ta haka kawai zaisa ya rabasu cikin ruwan sanyi, ringing d'in wayarshi ce takatse mashi nazarin da yake.







Innalillahi ce kawai yake maimaitawa bayan ya d'aga kiran da akayi mashi, parking yayi a gefen titi ya sadda kanshi kan sitiyarin motar yana tunanin rayuwa ba'a bakin komi take ga bawa, saida yasamu natsuwa na wasu mintoci kafin yaja motar zuwa Usman D'anfodiyo Teaching Hospital, bayan ya isa yazaro wayarshi yayi dialing number Daddyn nashi, sanar dashi yayi inda zaisamesu.




Yanayin yadda yaga mahaifin nashi da mahaifin Saleemah yai matuk'ar d'aga mashi hankali, dakyar yaja gwiwarshi datayi mashi sanyi har inda suke, isarshi wurin yayi dai-dai da fitowar likita daga d'akin da Saleemah take ciki, rufama likitan baya sukayi har zuwa ofis d'inshi.




Nazarinsu yayi gaba d'aya kafin ya bud'e baki yace "gaskiya yarinkarku tana cikin wani ma wuyacin hali, wanda accident d'in data samu bak'aramin haddasa mata matsala yayi ba, infact mawuyacin abune ta tashi tangaram batare da tasamu wani nakaso ajikinta ba"






Zabura mahaifin na Saleemah yayi yace "wace irin matsala ce tasamu wanda har zata kawo wani nakaso daga jikinta!?"





"sabbeni, kwantar da hankalinka mubi abin a hankali domin waware matsalar, dan ko tasamu rauni a k'ashin bayanta" cewar likitan dayake kwantarma da mahaifin na Saleemah hankali




Shidai Mr Aabid shuru kawai yayi yana jin sarauta ta ubangiji, wanda yanzu suka rabu da'ita Saleemahr kan zaije ya d'auko mata iv card da yamanta dasu ofis, ita kuma tace mashi tanason taje Jiddah plaza, k'ara jinjina lamarin ubangiji yayi na bawa ba'a bakin komai yake ba matsawar ya k'adarta wani abu a kanshi.





D'akin datake suka shiga kwance suka isketa kamar gawa dan kwata-kwata ta fita kamanninta, Umminta in baya ga kuka babu abunda take, take tsoron Allah ya k'ara mamaye duk wanda yayi tozali da halin da Saleemah take ciki.




Matsawa yayi gaban gadonta, ya k'uramata ido, baisan lokacin da hawaye shuka shiga zubo mashi ba, ganin bazai iya jurar ganin halin da take ciki ba yasa ya fice yabar d'akin.




Maryama ce ke amsar wayar da MM yayi mata, inda yake sanar da'ita matar da Mr Aabid zai aura tasamu accident.




"Azraa, kinji matar da Mr Aabid zai aure tasamu accident, yanzu ya MM ke sanardani"




yatsina fuska tayi tace "Allah shi kyauta" daga hakama ta d'auko wani jotting book ta cigaba da nazari kan abinda ta rubuta.




"Azraa ya ina maki magana, shine zaki jawo wani abu kinayi, maimakon kitashi kiraka ni naje na dubata tunda ya MM yace inje yanzu"





"sorry Maryama, wannan damuwarku ce batawa ba, inkin ga dama kije, amma nikam ba inda zani, abinda Umma ta turoni shi zanyi bawai dubiyar matan malaman makaranta ba"



Kallon mamaki Maryama tayi mata, dukda taji zafin maganganunta amma dan ta tusa mata bak'in ciki yasa tace "kice dai kishi kike kawai, shiyasa bakyasan zuwa"




Banza tayi da'ita ta cigaba da abinda take, "tunda banda arzik'in a rakani ni natafi, sai zuwa gobe dan in nadubo ta zan wuce gida"... "Allah yakaimu" daga haka Maryama ta d'auki bag d'inta ta wuce




K'arfe 5:00pm dai-dai Rasheed yayi parking car d'inshi makarantar su Azraa, bata wani d'auki lokaci ba suka wuce kasancewar tun 4 sunyi covering lactures d'insu na ranan.





"Alhaji ina ganin a d'aura auren nan kawai gobe, kaga sai mijinta ya cigaba da jinyarta"




"haba Alhaji Abdallah wace irin maganar banza ce kake fad'i haka! yarinyar dabatasan inda kanta yake ba kake cewa a d'aura mata aure" wanda dama tun ba yau ba yasan manufar auren da Alhaji Abdallah yakeson ayi tsakanin Aabida da Saleemah




Gudun kar yagano bakin zaren nashi yasa yace "gani nai zai hibata kulawa sosai fiye damu iyayenta"




"wannan maganar ba mai yuwuwa bace kabarta kawai, ka kyaleni inji da matsalar dake damun d'iyata" lakwas Alhaji Abdallah yayi baik'ara cewa komai ba.









```Bayan sati d'aya```



Rasheed ne zaune gaban Hajiyarshi ta tusashi gaba lailai sai ya gayamata dalilin dayasa ya janye auren Azraa, wanda bai shawara da'ita ba saida ya aiwarta da abinda yayi niyya sannan yasanar da'ita




"Hajiyarmu dan kuyi hak'uri, nasan bankyauta ba da nasa Uncle Abdallah yaje yace na janye maganar dake tsakanina Azraa, nayi haka ne saboda wani dalili nawa wanda nabarma kaina sirrin hakan"





"Sirrin banza sirrin wofi!, ainaji duk abinda yake faruwa dan ko mahaifiyarta ta sanardani komai" sunk'uyar dakai yayi yace "Hajiyarm..... "bansanjin komai daga bakinka tunda kaga hakan ne mafita gareka, ita kuma Azraa Allah yafiddo mata da mijin dayafika, ba irinka mai kishin mahaukata ba" shidai hak'uri ya cigaba dabata, saida yaga tafara sakkowa sanya yabar palourn yatafi part d'inshi.




A b'angaren Saleemah ko ciwo yak'ici-yak'icin yewa, dole saida aka fita da'ita k'asar india domin bincikar lafiyarta yadda yakamata, dukda k'ok'arin da mahaifin Aabid yayi ganin an d'aura auren kafin a fita da'ita, amma abin baiyuwu ba.




Azraa ce zaune gaban motar Rasheed, kallanshi tayi tace "ya Rasheed gidan Maryama zaka kaini, yau bamu da aji sai zuwa k'arfe biyu saimu wuce da'ita"




"kidaice inkaiki gidan Maryama zaki zance, bawai kice baki da aji ba sai k'arfe biyu" yayi maganar cikin b'acin rai, shuru kawai tayi don tasan fitinar ya Rasheed bamai k'arewa bace dukda ikirarin dayai ya rabu da'ita, speed d'in motar yak'ara, bai sauketa ko ina ba sai gwiwa lowcost, suna isa motar Mr Aabid na isa shima, kallonshi Rasheed ya juwo kan Azraa yace "kince baki da aji sai k'arfe biyu!, uhmm kodama kina nufin nakawoki nan dan yak'arasa dake zuwa school, shiyasa kika fad'i haka"




"ya Rasheed nasan bazan tab'a fita daga zarginka ba, saboda kasama ranka hakan tunfarkin ganinka dashi, wanda nace maka bawata alak'a tsakanina dashi amma ka kasa fahimtar hakan k'arshe ka janye maganar dake tsakanina dakai kan abinda baka da tabbacinshi"




"niko nake da tabbacin hakan, saunawa nake kamaku a cikin yanayi marar kyawun gani"




"to shikenan ya Rasheed abar maganar kawai, Allah ya had'a kowa da rabonsa"




"ke kam ya had'aki da rabonki, sauka kije yana jiranki kar ranshi yab'aci"




Mr Aabid kau yaci ka fam kamar fulawar da akayima b'arin yis, zufa kawai yake gogewa lokaci-lokaci yana dubansu ta site mirrow, ganin basu da niyyar rabuwa yasa ya tura mata sak'o _"ke nake jira kinsan akwai inda zamu_"




Shigowar sak'on yasa tayi saurin tura wayar cikin jikka dan tasan Mr Aabid ne yaturo mata, bata lura ba saidai ganin jikkarta tayi hannun Rasheed, wayar ya zaro, ganin batasa security ba yasa ya duba sak'on da yashigo




"Azraa kince badanshi kika zoba?, amma gashi yace ke yake jira akwai inda zaku, anyway sauka kije ni zanwuce ofis"



"ya Ra....... "sauka kawai sauri nake" yayi saurin katseta, fita tayi tare dayi mashi fatan sauka lafiya bayan ta d'auki bag d'inta da wayarta da ya aje mata saman seat, baiko amsa taba yaja motar da k'arfi kamar zaitashi sama.



Wurgama motar Mr Aabid tayi harara tashige gidan Maryama, ganin tashiga yasa shima yafito yabi bayanta tunda dama sunyi waya da MM kan wani issue nasu da zasu tattauna.




Kafin azo ya bud'e mata k'ofar falourn Mr Aabid yacinmata bakin k'ofar, "sai yanzu kika ga damar fitowa cikin motar tashi" kamar Allah baiyi ruwanshi a wurin ba tayi banza dashi takyale, hannunta yaja yayi waje da'ita duk turjewar datake, "wallahi inbaki natsuba zan d'aukeki dan nasan bawani nauyi ne dake ba" ganin zai aikata abinda yafi haka yasa tace "malam sake man hannu"..... "zan sakeki amma saikin shige munje wurin mota inba haka ba bazan sakeki ba"




Hannunta takwace tayi gaba don batason su Maryama suzo suga yanayinda suke ciki.




Mab'oyar da yake b'oyewa duk lokacin da ya ajeta gidan Maryama, yauma nan ya fake, ganin sunfito sunshiga mota yasa yabi bayansu, Mr Aabid na lura da motar Rasheed dake bin bayansu wanda kwata-kwata Azraa bata lura da'ita ba, alak'ar motartashi yakarkata zuwa d'ank'ani hotel, ganin inda suka shigane yasa Rasheed jin wata mummunan fad'uwar gaba don baiyi tunanin iskancin nasu yakai har zuwa hotel ba




Ganin sak'on da yakeson isarwa ya isa inda yadace ya isa, yasashi sakin murmushin gefe baki, ganin yana murmushi batare da wani abuba yasata ta kalli direction d'in da yake kallo, kwalo ido tayi ganin motar Rasheed ta wuce, yasa takalli inda yakawota dan tunda suka taho ta sadda kanta k'asa saida yai parking yasa ta d'ago taga yanana wannan murmushin.




Hawaye tashiga sharewa ganin gadar zaren da yak'ara kulla mata wurin ya Rasheed...........






*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊







©

*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*

®

*HALIMA MK*





*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*






*PAGE 21*







*K*oda suka shiga motar shuru ne yaratsa na wani 'yan mintoci kafin daga bisani Aabid ya kawar da shurun ta hanyar cewa "ina zaki haka?, dan me yasa kika dawo da wayar dana baki?, inason kigaya mani kwakwaran dalilin dayasa kike kuje mani, wanda hakan ke neman halaka rayuwata"



Shuru tayi tashareshi saima k'ok'arin bud'e motar tayi ta fita, ganin abinda take shirin yine yasa yayi ma motar key bayan yarufeta yadda bazata iya bud'eta ta b'angaranta tafita ba.



Gudu kawai yake shararawa dasu kamar masu barin garin, ganin gudun nashi yayi over domin yana ta had'a go slow a titi yasa tace mashi "Malam wai lafiyarka kake neman halakamu" cigaba yayi da kwasar motar yadda yake so, baizame ko ina da'ita ba sai by pass ta hanyar barin garin na sokoto zuwa katsina dan har sunyi nisa da sokoto rima verse, parking yayi yana maida nunfashi kamar wanda yayi tseren dawaki, bakajin k'arar komai sai na'urar sanyaya mota (Ac), kanshi ya'aza saman sitiyari yana sauke wata ajiyar zuciya, yafi k'arfin mintina goma a haka kafin ya d'ago rinannun idonshi ya sauke kan Azraa datayi tagumi tana kallon tsirar da Allah ya halilta bisa doron k'asa, wanda a zahiri kallonsu kawai take amma hankalinta kwata-kwata baya garesu yatafi wata duniyar ta daban.




Juyo da fuskarta yayi suna fuskantar juna, "Azraaaa meye mafita, mafita nake neman musamu dan wallahi bazan tab'a barin wani ya mallakeki ba alhali ina nunfashi koda hakan zaisa rayuka su b'aci, dan bazan zuba ido wane ya aureki alhali kinsan ke kayana ce bata wani ba"





"Sir Aabid mu hak'ura da juna, danko bazan tab'a gujema umarnin mahaifiyata inbi zab'in raina ba koda umarnin nata zaizama silar rasa farin cikina, dan haka ka kyakeni da zab'in mahaifiyata kuma zab'in raina"




"k'arya kike! kice Rasheed ne zab'in ranki, k'arya kike!! Azraa" yayi maganar ne cikin d'aga sauti, wanda yanayinshi bak'aramin tsorata Azraa yayi ba, maida nunfashi yake yana huci, saurin fizge fuskarta tayi daga rik'on da yayi mata ta juyar da fuskarta gefe d'aya, k'ara juyowa yayi da'ita suka cigaba da fuskantar juna, shanyayun idanunshi ya zubamata masu kama da maijin bacci, wani irin mik'i takeji duk lokacin da yazuba matasu dan bak'aramin rikita mata lissafi suke ba, sun kusa minti biyar a haka kafin tak'ara k'ok'arin janyewa daga gareshi, hannunta yayima wani irin rik'o, k'arar wahala tasaki jin irin rik'on da yayimata





"ki natsu ko kuma yanzu zanyi maki abinda bakyaso" murgud'a mashi baki tayi tafara gun-guni tana yatsina fuska, ganin yadda take murgud'a baki ba k'aramin burgeshi hakan yayi ba, jin wani abu na neman yimashi yawo a kwakwalwar kai yasa yace mata "ina zaki"... "tambuwal" sakarmata fuskar yayi yatashi motar, "Sir Aabid ka saukeni banasan rakiyarka"




"kinji nace zanrakaki ne" daga haka ya juwo da motar zuwa cikin garin na birnin Shehu, drop d'in mota ya d'aukar mata harzuwa tambuwal.





Koda ta'isa gidan kakanin nata tasamu kyankyawan tarba, danko an wadatata da abinci danasha maikyau, bayan komai yalafa taje cen gidan kakanin nata na wurin uba, inda wani d'an uwan Malam Hasheemu ya rufe Azraa da fad'an danmi zata kori Rasheedu, Alhali duk irin hallacin da yayi masu amma tasaka mashi da wanga shegantaka, "amma koda shike nasan maganinki dama d'an gidan sarkin tambuwal yayi mani magana tun wancan lokacin da kukazo keda Hauwa'u ganin kinfitar da miji yasa nabashi hank'uri, amma tunda haka tafaru zanbashi iznin ya turo da magaba tanshi"



Dam k'irjinta ya buga, wannan shine ana wata ga wata, ba'a rabu da bukarba anhaifi abu, haka yagama fad'anshi yabar gidan.




Kwanan ta biyu tambuwal tadawo sokoto, lokacin har yanzu Umma bata sakarmata fuska sosai ba kamar da danko fushi take da'ita sosai kan maganar Mr Aabid.






Alhamdulillah jikin Saleemah yayi sauk'i sosai saboda irin kulawar da likitoci suke bata, da kuma taimakon addu'o'e da'a kemata, wanda ake saran cikin satin nan za'a sallamosu, yayinda a kabar bikinta da Mr Aabid sati biyar masu zuwa.






Sauri take taga tagama shiryawa, kar ya Rasheed yazo bata shirya ba, ganin har tara tayi, jin salamarshi tayi tace a ranta a dai-dai, danko tarigadata gama kintsawa jikkarta tajawo tayima Umma sallama suka tafi.





Suna isa Sir Aabid na isa shima, kallon-kallo akai tsakanin Rasheed da Aabid, d'auke fuskarshi Rasheed yayi, wani irin mugun kallo Mr Aabid yajefi Azraa dashi kafin ya wuce ofis, a gurguje Rasheed yayi sallama da Azraa yawuce wurin nashi aikin.





```Bayan sati ukku```


Umma tak'i aminta da zancen Mr Aabid duk irin nacin da turo mutane dayake, amma tayi burus da zancen nashi, kuma duk wani hali da Azraa tashiga kan k'in amana datayi akan zance tana lura da'ita.




Rasheed ne zaune suna fira da Umma, inda yake mata bayanin wurin aikinshi sunturashi wani tryning garin legas (Rasheed yana aiki a ma'aikatar bada wuta nepa, watau kadco, yana rik'e da matsayin BM), fatan alkhairi tayi mashi da cigaban samun nasara mai d'aurewa, kallashi Azraa tayi tace "ya Rasheed Allah yabada sa'a, yaushe ne tafiyar taka?"




"cikin satin nan My wif...." wani tunani yayi ya hanashi k'arasawa abinda yayi niyyar fad'i, jin bai ida abinda yayi niyyar fad'a ba yasata sakin murmushi, ido d'aya yakashe mata ya cigaba da firarshi da Umma, ganin dare yayi sosai yasa yayi masu sallama yatafi.




***




"Azraa, kinkosan gobe ne d'aurin auren Mr Aabid da Saleemah" wutartace gaba d'aya ta d'auke danjin maganar kamar saukar aradu aka, "Azraa bakiji mainace ba"cewar Maryama "to Maryama konaji mai zance maki, Allah yabasu zaman lafiya" amma a zuciyarta ita kadai tasan yatakeji kan zancen auran nashi, jin kanta na neman juya mata yasa tayima Maryama sallama ta wuce gida dukda suna da sauran darasin da zasuyi, fitowarta bakin get d'in taga motar Aabid na shirin shigowa, ganin irin gudun da yake yasa tafad'i aranta dole kayi tunda ango kake, sauran kawar da kanta tayi daga wurin da yake duk irin horn d'in dayake mata, tayi gaba.



Parking yayi yafito yasha gabanta, wani irin kyau taga yak'ara mata gawani kyalle da fuskarshi taga tanayi, murmushin gefen baki yayi mata, "ina zaki?, dan nasan baku isa tashi ba" harara ta bankamai, tabi ta gefenshi zata wuce, tsabagen kishi ne ya hango kan fuskarta, ganin tana niyyar yimashi nisa yasa ya damk'o hannunta sai cikin mota.





Riverse yayi yafita da motar yafasa shiga cikin makarantar, wani keb'antancen wuri yasamu, ya parker motar, ji take kamar tayi kuka kotasamu sauk'in abinda takeji cikin ranta, k'are mata kallo yayi sannan yace "Azraa nayi maki laifi, amma ina neman afuwa daga gareki" hawayen datake k'ok'arin rik'ewa ne suka sauko kan kyankyawar fuskarta, saurin jawota yayi jikinshi yasa halshe yana lashe matasu hawayen dake zuba daga idanunta, kasa hanashi tayi danko tanasan tafi kowa buk'atar lallashinshi, kamar yadda bata gaji da kukan ba haka shima baigaji da lashe hawayen dake sauka kan fuskarta ba, saida taji damuwar datake d'auke da'ita ta ragu, sannan tatsa gaita kukan, janyeta yayi daga jikinshi, kwantar da jikinshi yayi jikin seat d'in motar yana maida nunfashi.



Ringing d'in wayarshi ne yakatse mashi tunanin dayake, ganin sunan Saleemah b'aro-b'aro akan screen d'in wayarshi ne yasashi kallon sashen da Azraa take zaune, zura mashi ido tayi tagani kozai d'aga kiran da akayi mashi, ganin takasa hak'ura da kiran datake mashi dukda k'in daukar da baiba har kusan karo hudu yasashi d'aga wayar




"on my way" kawai yace mata yadatse kiran, bud'e k'ofar tayi zata fita yasashi saurin damk'o hannunta, "sake mani hannu, kaje matarka najiranka" daga haka ta fizge hannunta tafita, bakin titi ta nufa ta tari abin hawa...........

















*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA DUK WATA MARUBUCIYA DAKE BIBIYAR LABARIN AZRAA, NAGODE KWARAI DA KULAWAR DA KUKABANI*

*MAMAN AYSHA HAUSA NOVELS, NAJI DAD'IN KARRAMAWARKU GARENI 😘😘😘😘*

*PAGE 18*and 19

*D'*agowa tayi da rinannun idanuwanta tace "bud'e man k'ofa natafi, tunda kagama b'ataman suna wurin mafi soyuwa a raina, amma kasani wallahi sai Allah yasakaman kan duk abinda kake yima" d'elle mata baki yayi yace "waye mafi soyuwa aran naki?".... "Rasheeeeeeeed" kallanta yayi shek'ek'e yace "ke da Rasheed har abada"

"tunda kaine ubana sai karabamu, kaini bud'e man k'ofa intafi banda lokaci ka!" tayi maganar cikin daga murya

Seat d'inshi ya kwantar ya rufe ido kamar mai bacci, hannunta takai da niyyar ta bud'e k'ofar saboda central lock yasa, caraf ya rik'e mata hannu, murza hannun ya shigayi yana wasa dashi "Sir Aabid waikai wane irin mutum ne wanda baka d'auki sab'on Allah a bakin komai ba, ya za'ai karink'a tab'ani kamar wata matarka" cigaba yayi da abinda yake kamar badashi take ba, ganin ba sakar mata hannun zaiyi ba yasa tasamu dai-dai tsintsiyar hannunshi ta gantsaramai cizo dama gashi idanshi a rufe yake, zafin cizon ne yasashi bude ido amma yakasa sakarmata hannu "hakan dakikai shizaisa na kyaleki, uhmmm yarinyar kin makaro" dukda yaji zafin cizon dataimashi amma baisa yasaki hannun ba

Wani irin tuk'uk'ine ya turni k'eta jitake kamar tayi ta bugunshi ko kuma tayi tamashi masifa har sai ya kyaleta, amma bata iyawa danko ita bamaison yawan magana bace balle tashin hankali, kyaleshi tayi taba banza ajiyarshi, saida yaji yana neman saka kanshi cikin wani yanayi yasa yasakarmata hannun, kallon agogwanshi yayi sannan yatada motar suka fita daga cikin hotel d'in.

"miya hanaki dubo matata asibiti kafin subar k'asar, alhali Maryama ta sanar dake"... "bani da hudd'a dakai bare ita ballantana naje dubata" murmushi yasaki yak'ara maida hankali kan driving d'inshi

Ganin lokaci yaja yasa ya wuce da'ita makaranta, koda taje Maryama bata kai da isowa ba.

Wani irin jirine ke dibarshi tunda yaga Mr Aabid ya shiga da Azraa hotel, ikon Allah ne kawai yakawoshi ofis, dakyar yasamu yafito daga cikin mota zuwa ofis nashi, yana zuwa dai-dai bakin k'ofar ofis d'in ya yanke jiki ya fad'i sakamakon wata irin hajijiya data d'aukeshi, masinja ofis d'in nashi ne ya lura da fad'uwar da Rasheed yayi take ya nufi inda yake, saurin kiran wani abokin Rasheed yayi Umar wanda ofis d'inshi na kusa dana Rasheed, kasancewar duk fad'in ma'aikatar bashi da abokin da ya wuce Umar

Ciccib'arshi sukayi sai Saraki specialist hospital, bayan komai ya lafa likitan kema Umar bayanin damuwace tayi mashi yawa wanda take neman haddasa mai hawan jini, sannan likitan ya cigaba da cema Umar lallai ne ayi k'ok'arin ganin ankawar mai da duk abinda zasashi damuwa, godiya Umar yayima likitan ya wuce d'akin da akaba Rasheed gado dan yasamu bedrest.

Kwance ya iske Rasheed duk yayi wani iri dashi, sannu Umar yayi mashi kafin ya cigaba da cewa "Rasheed mekasama ranka haka wanda yake neman illata rayuwarka?"

Nisawa Rasheed yayi sannan yace "Azraa ce damuwata, Azraa na neman haddasa man fitina a rayuwata Umar, narasa yadda zanyi na yakiceta in hutu da kuncin datake haddasa mani"

"na'aza kagama shafe maganar Azraa a rayuwarka ganin kajanye maganar auren dake tsakaninku"...... "nadai fad'a ne amma har abada bazan iya shafe Azraa a cikin babin rayuwata ba"

"to naji yanzu kuma miye had'aka da'ita?"..... "Umar mubar zancen nan kawai dan shine kwanciyar hankali gareni"

"to Rasheed nabarshi, Allah yazab'a maka abinda yafi zama alkhairi".... "ameen nagode".

"Rasheed garin ya hakan tafaru"... Hajiyarmu haka kawai nafara jin juwa, sai ganinai na fad'i" cewar Rasheed da suke waya da Hajiyarshi

"ban yadda ba koma miye gani nan zuwa asibitin" kashe wayarta tayi takira Aysha k'anwarshi suka tafi, har zasu shiga mota saiga Umma ta shigo kamar wadda aka kira, bayani Hajiyarsu Rasheed tayi mata, d'unguma sukayi su duka sai Asibitin Saraki

Kallo d'aya Umma tayi mashi tasan yana cikin matsanan ciyar damuwa, wanda tafi alak'anta damuwar kan Azraa ce ta haddasa mai, dukda ikirarinshi nace yafasa aurenta.

"sannu ya Rasheed" cewar Aysha da tamatsa gaban gadonshi, Hajiyarsa ko kasa cewa komai tayi saima idanu data zubamai ganin duk yabi yarame.

"sannu Rasheedu Allah yabaka lafiya"... "ameen Umma" shuru ne yaratsa d'akin donko kowa da irin tunanin da yake cikin ranshi.

"Hajiya bari inje gida zandawo zuwa anjima, indai ba'a sallameku ba"... "to Umma nagode Allah yabar zumunci" Umma tayi hakan ne dan tabasu damar sakewa.

Koda Umma ta tafi gida tunani ne ya addabeta na kan rashin lafiyar Rasheedu, a can b'angaran su Rasheed Hajiya ce ta tusashi gaba lallai sai yagaya mata abinda yasa aranshi wanda yake neman haddasa mai hawan jini

"Hajiya ni ba abinda ke damuna, kawai zuwan abune"

"k'arya kake Abdul-Rasheedu, bawani abu dakasa aranka sai wannan yarinyar Azraa, kasan zakasa kanka cikin wani hali mizaisa ka kasa hak'ura da halinta ka aureta a haka, sai yanzu daga baya kazo kasama ranka wata damuwa ta marar dalili"

"nifa Hajiya ba'a kan Azraa hakan tafaru ba"... "kaidai kasani, ko akan wa hakan tafaru" shuru yayi baisake magana ba saima idonshi da yarufe alamar yanason yayi bacci.

Azraa ce tayi sallamah, ta iske Umma zaune tayi tagumi, take gabanta ya fad'i tuna abinda yafaru da safe tsakaninta da ya Rasheed

"Umma barka da gida"..... "kinyi dai-dai kan sakayyar dakikaima Rasheedu dukda irin hallacin da yayi maki, inkin kashe masu yaro Allah bazai barki danko sai kinga sakayya a kan haka".... "Umma miyace nayi mashi kuma?"...... "zoki shak'eni sai inji dad'in gaya maki abinda kikai mashi, mutuniyar banza da wofi"

"Umma, kiyi hak'uri"..... "kije saraki inkina da lokaci ki ganoshi in kuma alhazan birni sun hure maki kunne shikenan saiki sha zamanki"

Bayan awa biyu, Azraa tafito cikin shirinta na zuwa gano Rasheed, "Umma natafi" banza tayi ta kyaleta, gajiya tayi da tsayuwar ta tafi.

Koda ta'isa, bata iske kowa d'akin ba sai shi kad'ai kwance dan Hajiya da Aysha sundawo gida, "kinzo ne nan ma ki k'arasani, dan haka bana buk'atarki kifice kibani wuri"

"ya Rasheed Allah ya huci zuciyarka, amma bani da wata manufa a kanka"

Tunda mai napep ya ajeta yake bin ta a baya har yaga d'akin da tashiga, saida yagama abinda yakawoshi, sannan yatura k'ofar d'akin yashiga, sallama yayi masu suka juyo ita da Rasheed, tashin hankali ne ya baiyyana k'arara akan fuskar Azraa ganin Mr Aabid, murmushin gefen baki yayi mata ya kashe mata ido d'aya, hannunshi ya mik'ama Rasheed don suyi musabaha, amma k'ememe Rasheed yak'i mik'a mashi nashi hannun, ganin baida niyyar mik'owa yasa yace "Rasheed barka dai, ya k'arfin jiki"..... "Alhamdulillah" daga haka ya juya masu baya yana kallon jikin bango, ambaton Allah kawai yake domin shikad'ai yasa wane hali yashiga ganin Aabid.

Azraa ko innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Allahumma ajirni fi masibati wa kallifini khairan minha, kawai take fad'i cikin zuciyarta dan ko Mr Aabid na neman zame mata annoba, shurune ya wadaci d'akin, nisawa Mr Aabid yayi yace "mu wuce ko, dan naga ga dukkan alamu Rasheed yasamu bacci"

"aiba kaika kawoni ba kana iya tafiya" harara ya wurga mata ta k'asan ido, tare da gargad'in zata sani.

Ganin zasu dameshi da surutu yasa yace "Azraa kibishi kawai nagode da ziyara"... "ya Rasheed ba yanzu zantafi ba tunda batare mukazo dashi ba"

"naji, kibishi kawai zaifi maki sauk'in tafiya" k'intashi tayi, ganin fuska Rasheed har yanzu tana dubin bango yasa Aabid ya kamo hannun Azraa, ganin zai'iya yimata abinda yafi haka kuma batasan Rasheed yaga hannunta da yarik'o yasa takwace hannunta, wayarta ta shiga dannawa, sak'o ta turama Mr Aabid, ganin abinda ta turo yasashi yima Rasheed sallama yatafi, duk a tunanin Rasheed ya d'auka suntafi tare da Azraa, juyo da fuskarshi yayi idanuwanshi cike da kwalla, tozali yayi da Azraa data sadda kanta k'asa

"miya hanaki binshi alhali kinsa tare kuke?"..... "wallahi ya Rasheed bansan zaizo ba"....... "to ya akai yasan ina nan, inba ke kika fad'a mai ba?"

"ya Rasheed ni bani nagaya mashi ba" banza yayi da'ita ya cigaba da jinyar zuciyarshi danko ba k'aramin tashin hankali yashiga ba ganin Aabid da kuma rainin yawon da yake zomashi dashi.

```Bayan Sati Biyu```

"Abdallah yanzu har kayi arzik'in da zanbaka umarni kak'i bi, danmi yaro yace ga ra'ayinshi amma kace dole sai san ranka zaibi, wanda abinda kake da niyyar aikatawa ba abune maikyau ba, da har zakace dole sai kayima d'anka auren jari, duk irin dukiyar da katara, amma bai ishekaba sai ka hango na wani wanda ka d'ararmawa, don haka umarni ne nake baka bawai shawara ba kabar Aabid ya auri yarinyar da yakeso, tunda waccen mahaifinta yak'i aminta da auren nasu saboda wasu dalilai naku na banza da wofi da d'aurama rai dogon buri"

"Allah ya huci zuciyarka Alhaji Baba yadda kace haka za'ai Allah yasa tazame mashi alkhairi"

"to ko kaifa, Allah yayi maka albarka kaida zuri'arka baki d'aya"....... "ameen tsoho mai ran k'arfe" yak'arasa maganar cikin yanayi na barkwanci

"ina Aabid d'in yake yazo ya maisheni gida" shigowa yayi palourn yana wani soshe-soshen k'eya, dan duk abinda sukace yana lab'e yana jinsu, domin shi yaje ya had'o mahaifin nashi ga Alhaji Baba mahaifi ga Alhaji Abdallah dan yasan shikad'ai zai'iya tursasashi akan yabarshi ya auri zab'in ranshi, harara Alhaji Abdallah yabi Aabid da'ita dan yasan shi yaje ya gayama Alhaji Baba, dan tun kwanakin baya yaje mashi da maganar Azraa yafatatakeshi kanta, amma shine bai hak'ura ba yaje ya had'ashi da mahaifinshi, kama sandar da Alhaji Baba yake dogarawa yayi ya mik'ar dashi sukabar palourn..............

*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA GA:*
```AISHA ALI GARKUWA```
```BIEBEE ISAH```

*PAGE 19*

*"N*a aminta da aurenka da d'iyar talaka, amma kasani nima ina da nawa sharad'in"

"toh Daddy, meye sharad'in naka?"... "in lokaci yayi zan sanar dakai" daga haka suka cigaba da yanda zasu tsara wani bussiness dayake son ya tura Aabid zuwa k'asar india, daga nan har ya dubo Saleemah, dan dama tun tafiyarsu da sati d'aya yaso zuwa amma wani dalili ya hanashi zuwa.

Tun k'arfe shidda ta shirya sanin yau zasu fara jaraba, kuma gashi da subject d'in turanci zasu fara, sanin mai koyar dasu ba mutunci ne gareshi ba yasa tunda ta tashi da Asuba bata koma ba, ganin har takwas tayi ya Rasheed baizo ba gashi k'arfe tara zasu fara yasa tayima Umma sallama ta tafi, kicib'is sukayi bakin zaure, zaishigo ita kuma zata fita, "sorry na b'ata maki lokaci alhali zaki fara exams ko".... "ba damuwa ya Rasheed na maka uzuri" daga haka suka kama hanya sai d'anfodiyo,koda suka isa tara saura minti sha biyar, sallama yayi mata tare dafatan yin jarabawa cikin nasara, sannan yaja motar ya wuce wurin aikinshi.

Bayan sunfito daga d'akin jarabawar, direct capteria suka wuce Azraa da Maryama sai wata k'awarsu Rumanah, amma Rumanah bata da aure, Rumanah 'yar jihar katsina ce karatu ne ya kawota sokoto kuma a cikin compus take zaune, yarinya ce mai hankali da kamun kai, shiyasa tasu tazo d'aya dasu Azraa.

"amma fa Mr Aabid ya tsaurara questions d'in na, dan bakuji yadda kaina ya d'auki caji ba" cewar Rumanah datayi relacsing bisa plastic chair, yatsina fuska Azraa tayi tace "ai ba abinda yasani sai mugunta da k'eta da cin zalin mutane"

"kai Azraa dukshi kad'ai, a d'an raga mashi mana" cewar Maryama, daga haka suka cigaba da tattauna yadda jarabawar tazo masu da kuma shirya wadda zasu fuskanta gaba.

Bayan tayi sallah Issha'e, tana zaune tana lazimi taji shigowar sak'o da kamar tashare sanin kowa yene yasa ta duba taga miyace _"kisameni zaure_", tunanin yadda zata fita takeyi dan tasan gargad'in da Umma tayi mata akanshi, sharewa tayi ta cigaba da laziminta, shuru-shuru baiga ta fito ba yasa yakirata a waya

"Azraa kenake jira".... "bana gida"... "ina kikaje?" shugowar Rasheed yasa ya katse kiran, d'aurewa Rasheed yayi ya mik'ama Mr Aabid hannu suka gaisa, bayan sun gaisa ya wuce cikin gida dan dama lokaci-lokaci yakanzo susha firarshi da Umma.

Bayan Rasheed ya gaishe da Umma itama Azraa ta gaisheshi, "kina da visitors a waje" yayi maganar k'asa-k'asa dan kar Umma tajishi, idanuwanta ta zuba mashi na wani lokaci kamar maison gano wani abu, kawar da kanshi yayi ya cigaba da firarshi da Umma

Ganin ak'alla yashare mintina talatin yana jiranta amma bata zoba yasa yasamu yaro ya aika kiranta, Umma ce kecema yaron ace Azraa bata nan, saurin tsaida yaron Rasheed yayi yace "Umma dan Allah kibarta taje" shuru tayi takyaleshi ganin haka yasa yayima Azraa alama da ido kan taje wajen kiran.

Harara ya jefeta da'ita, da tunanin abinda zaimata, wata dubarace tafad'o mashi arai, dan yasan batason abun, "baki ga text d'inaba"..... "kona gani mezan maka" murmushin mugunta ya saki, matsowa yayi inda take, ganin shegantakar dayakeson yimata yasa tayi saurin barin zauren, taku d'aya yayi ya cimmata matseta yayi jikin bango wanda har sunajin nunfashin junansu, "bari in gwada maki abinda zakiyi mani, tunda wancan garan yakoya maki yadda akema mutane rashin kunya" hannunshi yake k'ok'arin turawa cikin abayarta, gyaran muryar da akayi ne yasashi fasa abinda yayi niyya, jikinshi ya janye daga shige mata da yayi.

Girgiza kai kawai Rasheed yayi yabar cikin zauren ya nufi gida, "Allah ya taimakeki da yau kingane kuranki, yanda ko ance gobe ki k'ara mani rashin kunya bazakiyi ba" gum tayi mashi domin lamurranshi bak'aramin d'aure mata kai suke ba

"Azraaaaaa, inason ki sanarda Umma yanzu zan shigo domin ta bani iznin nemanki, dan banasan maganarmu ta d'auki lokaci, dan nafison a d'aura dake kafin nawa da Saleemah"

"Aabid!! Bari ingaya maka abinda bakasani ba, wallahi ko maza sunk'are a duniya bazan tab'a aurenka ba, tunda kayi silar rabuwata da ya Rasheed, kaima bazaka tab'a samuna a matsayin mata ba, danko Umma bazata tab'a yarda da hakan ba"

Take zufa tashiga keto mashi dan baiyi zaton haka daga garetaba, ya'aza mahaifinshi shine babban shamak'in da yake ganin zai rabashi da Azraa saiko mahaifiyarta, dan tun ranan farko da taganshi baiyi zaton tayi amana dashi, saidai gashi baiyi zaton wuta a mak'eraba amma sai gashi ta b'ullo a masak'a.

Juyowa tayi da niyyar barin zauren akaro na biyu, ganin abinda zatayi yabashi kuzarin fizgo hannunta har tana fad'awa saman k'irjinshi, kallan k'urilla sukewa junansu tare da kai wani irin sak'o ga zukatansu wanda ke dilmiyar da masoya har su rasa wace duniya suke, ganin karya gano logonta yasa tayi saurin jaye jikinta daga nashi, k'insakinta yayi, "Azraa inason ki kalli kwayar idona kice koni kad'ai narage namiji a duniya kin hak'ura da aure, to niko nayi maki alk'awarin zan daina bibiyarki har k'arshen rayuwata"

Kasa d'aga ido tayi ta kalleshi hasalima sai k'ara sunk'uyar dakai tayi k'asa, ganin bazata iya abinda yace ba, "Azraa ya kike ganin zamu fuskanci Umma da wannan zance?"

"nima bansa ya za'aiba, kuma miye makoman aurenka da budurwar da akasa maka ranan aure da'ita?"

"aurena da Saleemah yana nan", wani iri k'irjinta yayi mata jin cewar maganar aurenshi da Saleemah yanan, "kisanar da Umma zamu zo nida MM dan neman iznin fara nemanki gobe, dan inaga zuwa jibi zan wuce india kan wasu harkoki na Daddy da kuma duba lafiyar matata"

"dama akwai wanda yace ba matarka bace" tayi maganar tana yatsina fuska, dariya ce taso kubce mashi jin yadda tayi maganar cike da kishi

"sorry dama bance ta wata bace tawace, nidai ayimani iso wurin Umma"

"kabari inka dawo daga dubiyar matartaka sai a yimaka" daga haka kawai ta shige gida ta kyaleshi, koda ta shiga Umma har tayi bacci saboda maganin mura datasha, saida taji tashin motarshi sannan taje ta rufe masu gida.

Kwana tayi tunani na yadda Umma zata amshi zance Mr Aabid da kuma ya Rasheed zaiji, in har amba Aabid iznin neman aurenta, wace irin fahimta zaiyima abin, sannan wane k'alubane zata fuskanta na zama da kishiya

Koda gari yawaye kasa sanarma Umma tayi, haka tagama shirinta ya Rasheed yazo suka wuce makaranta.

Koda suka fito d'akin jarabawar duk tayi wani sukuku da'ita, ba irin tambayar da Maryama da Rumanah basuyi mata amma tak'i sanar dasu komai.

Suna nan zaune bakin aji, wani d'alibi yazo kiran Azraa, Mr Aabid na nemanta, saida Maryama tak'ara mata magana sannan ta tashi ta tafi wurin kiran, kwankwasa k'ofar ofis d'in tayi kafin yabata iznin shiga, bayan sungaisa yake cemata "Azraa ya kukayi da Umma kinsanarmata ko yaya?"

"bariga da nasanarmata ba tukun"....... "sai wane lokaci"

"kabari har kugama hidimar bikinka da Saleemah sannan lokacin ta ragejin haushina datakeji na ganin nina gujewa auren ya Rasheed".... "hakan kina ganin yafi".... "eh" matsowa yayi kusa da'ita yadda zata fuskanceshi da kyau yace "Azraa kodai kin sauya ra'ayi ne akaina?" wasa ta shigayi da yatsun hannunta, ganin abinda take yasashi juyawa ya rufe k'ofar ofis d'in

Kamo yatsun hannunta yayi yashiga murza matasu, "Sir Aabid dan Allah kadaina banajin dad'in abinda kake mani" shanyenyun idanunshi ya zubamata, cigaba yayi da murza mata hannun, sak'on nashi bak'aramin shigarta yake ba danko tanajin dad'in hakan, sannin haramcin abun ne yasa take nuna mashi bataso, k'ok'arin sagala hannushi ga k'ugunta yake niyyaryi yasa ta wafce jikinta daga nashi, "pls. Azraa"

K'ofar ofis d'in taje ta bud'e tajita rufe ya kuma zare key d'in k'ofar, "ka bud'eman zankoma aji" takowa yayi inda take hugging d'inta yayi ya rad'amata magana cikin kunne "zanyi kewarki My Heartcon, yau cikin dare jirginmu zaitashi zuwa k'asar india" tare da k'ara kwanto da kanshi saman jikinta

"safe journey" abinda tace mashi kenan sannan tayi mashi alama da yabud'e mata k'ofar, sassauta hugging d'in da yayimata ya kamo hannunta yana kissing d'insu gently, bak'aramin kasala hakan ya saukarmasu ba, ganin karya jefasu cikin halaka yasa ya kyaleta, bud'e mata k'ofar yayi ya koma bisa kujerar dake cikin ofis yazauna, ganin ya bud'e mata yasa tafice batare data ko k'ara waiwayenshi ba......

*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊











©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*






*SADAUKARWA*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*



*INA JINDAD'IN KWARIN GWIWAR DAKIKE BANI* *SIS FIDDOH SODANGI*





*PAGE 23*





*L*eb'anshi na k'asa ya ciza yana wani fidda harshe kamar tsohon maye, ganin ya zubama nonuwanta idanu yasata saurin kwace hannunta tayi saurin taresu da hannuwanta duka biyun, funcike hannun nata yayi yamayar danashi muhallin da yajanye nata, wani irin yarrrrrrrrrr taji ga jikinta jin saukar hannunnashi ga boobs d'inta wanda tunda take bata tab'ajin wani yanayi maidad'i irinshi ba, cigaba yayi damurza matasu yadda yakeso haryana wani gurnanin dad'i, ganin murzawar kamar bazata kaimashi inda yakeso ba yasashi kai bakinshi akansu, saurin tureshi tayi tace "Allah saiya sakamani, tunda basan gaskiya kake yimani ba jikina kakeso" tare da jawo abayarta tamayar





Kasa tab'uka komai yayi saida yaga tana shirin barin cikin motar yasashi saurin sa lock, jinginar da kanshi yayi ga jikin seat yana cigabada maida numfashi kamar wanda yayi gasar gudu, dakyar ya iya furtamata "pls. Azraa inason kiraka ni wani wuri bazamu dad'eba zan maidoki kinji my heartcon"





Yatsina fuska tayi tace "kaje matarka taraka ba bawai jaraba ta ishekaba kazonan kana wani matsata" tak'arasa maganar kamar ba'ita ta furta ba, murmushin gefen baki yayi, yana nanata maganganun nata cikin ranshi, yana cewa lallai batasan an d'aura auranshi da'ita ba kila Umma bata sanarda ita komi ba, "nasan da matar tawa nace kirakani, dan haka ki sanar da Umma zaki fita da mij....." saurin rufe bakinshi yayi sannan ya cigaba da cewa "pls. pls. pls. My heartcon kitaimakama mijin Saleemah" wata irin muguwar harara ta watsa mashi tana yatsina fuska, gira d'aya ya d'agamata yace "muje kin amince zaki rakani".... "ban amince ba, nika fad'i abinda yakawoka baka tusani gaba ba kanasa muna sab'on Allah, danko kad'ai cewar nan damukayi mu biyu to katabbatar shed'an ne cikon na ukkun mu, dan haka gara kafad'i abinda yakawoka kafin shaid'an yaci galaba akanmu"





"har abada Azraa shed'an bazai tab'acin galaba akanmu ba, kinji My sanyin wandona"...... Sanyin wando da ya ambata ta shiga nanatawa a ranta anya Mr Aabid yau ko baisha kwayar tabajeba irin wanga sakin layi dayake, inba hakaba mai zaihad'ata tazama sanyin wandonshi alhali ba matarshi ba wadda zata d'auke duk wata lalurar dake cikin wandonshi.




Jin shurun nata ne yasa yace "daga yau karki kuma zuwa school har sai ranan da nabaki umarni"..... "to Baba Hasheemu yadda kace haka za'ai", sarai yagane gatse tayi mashi amma yashare yace "balle kiyi gigin inganki cikin motar wani da sunan zaikaiki"





Tasan bada kowa yake ba inba Ya Rasheed, yasa tace "wannan badamuwarka bace da zuwana ko wanda zaikaini", murmushi yayi yakamo hab'arta suna kallon juna "to ki kwatanta hakan ki gani, kiga abinda zanmaki" shuru ne yaratsa cikin motar kafin Aabid ya numfasa yace "Azraa bacci nakeji amma inason inji jikina jikin mace tana lugugutani kamar jaririn da yake hannun uwarsa tana lallashinshi yayi bacci"





Jin kalamanshi sun girmi tunaninta yasa tace "aikafini sanin wadda tadace tayi maka haka bawai niba kazo katusani gaba da fitina iri-iri".... "jikinki kawai nakeson nasamu natsuwa dashi bawai wata mace ba, ina fatan kin gane" rasa abinda zatace mashi ne tayi yasa ta kwace jikinta daga nashi, k'ara damk'ota yayi yashiga nuna mata wani irin salo wasannin soyayya dake rikita wanda akemawa ganin yana neman kama wata jihar daga sokoto zuwa kaduna yasata kwaci kanta ta k'arfin tuwo, ganin yana neman sama kanshi jangwam bakuma samu zaiba yasa ya kyaleta yayi mata saida safe ya wuce tare da gargad'in karyasake yaganta makaranta inbashi yace taje ba.






Yau kwana biyu da d'auri auren Azraa, wanda yayi dai-dai da kammala abinda Rasheed yakaishi legos, amma sanin tashin hankalin da yake ciki ya hanashi dawowa garin na sokoto dan kwata-kwata baya fatan yasa Azraa a idonshi yafison harsu gama budirin bikinsu sannan yadawo, dukda shi kad'ai yasan yadda zuciyarshi kemashi azabar ciwo da rad'ad'in rashin Azraa, domin kuwa yasan barin aurenta da Aabid shine kawai mafita gareshi dan bayajin zai'iya had'a shinfid'a da'ita koya aureta alhalin tariga data bama wani kanta tun kafin tashiga gidanshi (oh πŸ€”πŸ€” zato zunibi Rasheedun Umma), koda Hajiyarshi ta tambayeshi yaushe zaidawo cemata yayi baigama abinda yakaishi ba, shareshi kawai tayi dan tasan saboda Azraa ne yahanashi dawowa.








Tun ranan da yazo ya luguigutata bata sake sashi a ido ba dukda zuciyarta na mararin sake sashi a idaniyarta, amma tunawa tayi da yanacan yanashan amarcinshi da Saleemah yasata buga wani dogon tsoki wanda Umma dake tsakar gida tana jiyota, shareta Umma tayi ta cigaba da sabgoginta, wanda tun randa aka d'aura aurenta da Aabid Umma bata sake sakarmata fuska ba saima wani fushi datakeyi da'ita, wanda ita Azraa batasan dalili ba tunda bawanda yace mata and'aura mata aure, ganin yau talata ce kuma suna da darasi yasata ta tashi tayi shirin makaranta dukda tana d'an tsoron gargad'in da Sir Aabid yayi mata, amma hakan bashi zaisashi yahanata zuwa ba tunda baida alhakin hanata zuwa, sallama tayima Umma takama hanyar zuwa skull, dukda Umma taso tahanata zuwa amma datayi wani tunani takyaleta taje.





Shigowarshi cikin d'akin d'aukar karatun yasa d'alibai tashi su gaisheshi domin girmamawa yayinda mafi akasarin 'yan mata zukatansu nagareshi, nusamman yau da yayi wani irin a zabeben kyau na banmamaki wanda burin kowace mace ta nunashi a matsayin mijinta uban 'ya'yanta, take wani irin kishi yalullub'e Azraa ganin yadda 'yan matan ajin suka zuba mashi na mujiya, baisauke kwayar idonshi akan kowaba saikan Azraa daketa wani yatsina fuska, wani mugun kallo ne yajefeta dashi musamman da yaga bak'ar rigar after dress ce jikinta sai d'an kwalin rigar datayi rolling dashi, kallon zakisan nikika ketama doka yayi mata, sannan ya cigaba dayi masu darasi, Maryama ce keta zungurarmata k'afa tak'asan tebur nata mik'a mata jikkarta dake gefen da Azraar take dantaci goro sabida wani amai dayataso mata, banza Azraa tayi tashareta ta cigaba da maida hankali kan abinda ake koya masu, saukar amai kawai taji Maryama ta antayo matashi, hankalin 'yan class d'in ne yadawo kansu banda sannu ba abinda sukema Maryama, tambayar uzuri su Azraa sukayi wurin Sir Aabid suka kamata ita da Rumanah sukabar ajin, bin hips d'inta yayi da kallo yadda take wani irin juyasu, kuta yayi ya juwo zai cigaban masu da darasi sukayi 4 eyes da wani matashin samrayi da ya zubama bayan Azraa ido har wani mik'a wuya yake yana k'ara hangota, kasa cigaba dayi masu darasin yayi, yaimasu sallama yabar ajin cike da jin zafin yadda Azraa tazo makaranta haka bayan ya gargad'eta dakartazo harsai yabata umurnin zuwa.





Hostel suka wuce domin su kintsa jikinsu, bayan Rumanah tabasu kaya suka canja dan duk wanda sukasa yab'aci, kwanciya Maryama tayi bisa gadon Rumanah tana maida numfashi, shigowar wata 'yar ajinsu ce yasa Azraa saurin maida hijabin dake jikinta danko englishwears ne Rumanah ta bata tasa ta wanke rigarta data b'aci da amai, "Azraa, Mr Aabid yace kisa meshi bakin hostel yana jiranki ya kuma ce karki b'ata mashi lokaci".... "jeki kice mashi baki ganni ba"




Maryama ce tayi saurin tsaida Zee kaita da ya aiko tace "Azraa ki rufa mana asiri kitashi kije karki jama kanki laifi".... "to gwagwo Maryama bari natashi naje tunda tsoho yayi kira" dariya suka kwashe da'ita suna mai yima Azraa gwalo musamman Maryama da Rumanah dasuka san kwanan zancen dan MM yafesa ma Maryama ita kuma ta gayama Rumanah ammar ta cema Rumanah karta gayamata and'aura amranta da Mr Aabid, dakyar suka samu suka lallasheta ta tafi.







Tana isa bakin hostel d'in taga motarshi parker a wurin, bud'ewa tayi tashiga, jan motar yayi sukabar cikin makarantar, ko k'ala baice mata ba saima driving d'inshi da yakeyi cikin gwanancewa, haka itama ta shareshi batare data tankamashi ba, ganin yakawota gidanshi wanda suka tab'a zuwa kwanaki yasa ta kalloshi, d'auke idonshi yayi daga kallon datamashi saima horn da yakeyima getman, saurin wangale mashi get d'in yayi shiko ya danna hancin motar cikin gidan, dai-dai bakin part d'inshi yayi parking, "ki fito zanrufe motata" kallan bashi da hankali tayi mashi naya zata shiga gidan alhali matarshi na ciki "kina b'atan lokaci ko saina d'aukeki" ganin karta had'ama kanta zafi biyu ga shigowa gidan wata gata kuma rumgume da mijinta yasa ta fito dan tasan ba k'aramin aikinshi bane d'aukarta.




Part d'in yasama key bayan sun shiga ya zare key d'in daga jikin k'ofar ya tura cikin wandonshi, ganin yarufe k'ofar ya kuma zare d'an makullin yasa hankalinta tashi tare da jama su Rumanah Allah ya'isa danko su suka matsa mata dataje wurin kiran dayake mata gashin nan yana neman tozartata, ganin ya nufota gadan-gadan yasa tashiga karanta _la'alaha inna anta subba hanaka inni kuntu minal zalimin_ tare da tofa mashi tofi ga jiki, hannunta duka biyun ya had'e wuri guda yace "meyasa da nahanaki zuwa makaranta kikaje tare dayin wata irin shiga marar ma'ana"...... "sorry Sir k'addara ce takawo ni, amma ina rok'onka da kayi mani arzik'i ka bud'e mani intafi walkahi bazan sake zuwa ba sai kace naje"




"baki isa in bud'e maki kitafi ba batare da nahuta dake ba" zaro idanu tayi tace "kaji rsoron Allah karka k'eta mani haddi, sannan kuma kaji kunyar idon matarka karta ta risk'eka kana aikata mugun abu"





Baima saurareta taba ya wancakalar da abayarta danko yasan halalinshi zai murza bata wani ba, ganin ya cire mata abaya yasata saurin tsugunnawa danko bomshirt ne jikinta da halfbest



"ya salam! ya salam!! ya salam!!!" kawai bakinshi ke furtawa dan bak'aramin tada mashi hankali surar jikinta yayi ba, musamman dayasan yana daga cikin maza mabuk'ata..........
















*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊

©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*

*SADAUKARWA*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*

*PAGE 24*

*M*ik'ar da'ita yayi tsaye daga tsugunnin datayi, hannunshi guda yasa ga k'ugunta yayi mata makari dashi, yayinda d'ayan yashiga murza mata mazaunanta dashi, take wani irin k'arfi yazomata dan inbatayi dagaske ba to lallai Mr Aabid yana neman rabata da abu mafi mahimmanci da duk wata macen arzik'i take tunk'aho dashi, cikin zafin nama ta ture duka hannuwan nashi daga jikinta ta gefe, taga-taga yayi zaifad'i saboda kwata-kwata baida kuzari ga jikinshi, saurin dafa kujerar dake kusa dashi yayi kafin yasamu kuzarin k'ara cabkota, glass cup dake saman stool tad'auka "Wallahi Mr Aabid matsawar baka rabu dani ba kobaka bud'e mani k'ofa ba wallahi zan illataka, dan naga kwata-kwata babu tsoron Allah cikin lamurranka, nagaji da cinkashin dakake da jikina, alhali karabani da masoyin gaskiya wanda har gobe Ummata nafushi da hakan, kazo kana neman b'ataman rayuwa"

Kallo kawai yake binta dashi, danshi kad'ai yasan kid'an alantar da ake mashi cikin wando bugu da k'ari bayajin zai'iya kyaleta haka batare da yayi koda romancing d'inta ba dukda irin barazanar datake mashi don inya kyaleta tabbas zaicutu, sausauta murya yayi yace "pls. My Azraa kitamakama mijinki wallahi ina cikin wani hali, ko kinason rasani batare da mund'and'ani zumar junanmu ba dan wallahi da kinsan yadda ake kad'a mani alanta a cikin wandona tabbas da kinyi gaggawar kawo mani d'auki dan kiceci rayuwata daga fad'awa halaka", kallan yazare tabishi dashi, ganin irin kallon datake mashi yasashi mamarta yawafce cup d'in dake hannunta, tureta yayi tafad'a saman kujera 3seater, kwance tayi rigin-gine k'irjinta na fuskantar fuskarshi, jin ank'ara mashi sautin kid'an cikin wando yasashi haye ruwan cikinta, bakinshi yakai gana shanunta danko su sukafi tsone mashi idanu, bil hakk'i yake tsutsarsu kamar mayunwaci, yayinda wando nashi kamar ana k'ara mashi iska sai wani k'ara cika yake kamar tayar da ake k'arama iska, jin wani icce-icce na zungurarta yasata sakin wata razanan nan k'ara danko ta gane sandar aikin tashi ce take tsaye hartake tab'ota, jin k'arar data saki ne yasashi d'agata yana maida numfashi, hanyar bedroom yanufa har yana wani tangad'i dan yakai k'ololuwar wajen buk'ata, zare kayan jikinshi yayi yasakarma kanshi shower tare da dangwalo sabulu yana murzama kayan aikin nashi ko yasamu sa'ida takwanta dan ya fuskanci ruwa kawai bazai kwantar da'ita ba, saida yayi wanka janaba ya kintsa sannan yafito, lokacin Azraa tayi kuka harta gaji da irin k'addarar dataso afkamata, wurin k'ofar fita yayima tsinke batare daya tankamata, dama tunda yatashi daga samanta tasaka hijabinta, bin bayanshi tayi tana wani cin magani tare da jifanshi da hararar tsana da kyamatar halayyartashi.

Wani shagon saida jallabiya ta mata ya wuce da'ita, "minti d'aya ina zuwa" daga haka yafice yabar cikin motar, tsala-tsalan riguna yasai mata guda uku masu kyau da tsada, ganin macace ketsaran shagon yasa yace mata ta fito, "kishiga ki canja kayan dake jikinki ki kuma maida wannan hijabin bayan kinsa rigar" daga haka ya wuce cikin mota yatsaya jiranta, daga nan kuma basu zame ko ina sai shagon da ake saida waya, nanma hanata shiga yayi saida kawai dayafito ya mik'o mata kwalin waya iphone 7, ko kafin subar wurin saida yayi mata settling komai akan wayar sannan sukabar wurin, bayan sun isa k'ofar gidansu Azraa, harta kama marfin k'ofar zata fita yace "wannan yazama na k'arshe da inga k'afarki k'ofar gidan nan, inba ninayi maki iznin fita ba koda kuwa Ummace ta aikeki dan nafita iko dake"

Kallan wawa marar hankali tayi mashi sannan ta yatsina fuska ta fita, girgiza kai yayi yaja motar yatafi, kwakwalwarta ce tashiga cikin rud'ani da dogon nazari, taya zaice wai "kitaimakama mijinki" sannan kuma yace "koda Umma ta aikeki dan nafita iko dake" anya ba akwai alamar tambaya game da magangunanshi, dan abin nad'aure mata kai sosai kan yadda yake wasu d'abi'u akanta tunranda yazo da daddare, kuma Umma ce ta umurceta dataje yana nemanta bayan kuma ita tahanata tsayuwa dashi tare da gargad'i maitsanani

Jin zata sakanma kanta haniya da yawa yasa ta cire rigar daya saimata yanzu ta d'aura zani, dan tasan dole saitayi wanka kafin ta fuskanci ubangijinta dan bak'aramin jagwalgwala mata jiki Mr Aabid yayi ba.

"Hauwa'u wane shiri akema Azraa nagame da kayan gyaran jiki kinga bai wuce kwana ukku ba tarewarta kan yadda aka tsara" cewar Hajiyarsu Rasheed data kawoma Umma ziyara "wane gyara kuma Hajiya banda abinki, ita dataji tagani saishi saita nema ta gyara mashi"..... "a'a Hauwa'u karmuyi haka dake yaza'ai kice ita zata nema, kenan baki yadda da k'addara ba kuma matar mutum ai kabarinshi baikamata dan bata auri d'anki ba ace ba'a yimata komai na gyaran jiki, ina Azraa take tafito muje ni nasa a gyaraman d'iyata ke kuma kuyita fushi keda yaronnaki tunda kunkasa hak'ura ku yarda da k'addararku kusan komai yin Allah ne"

"muko mukasan hakan shiyasa mukabarku da zab'inku" murmushi Hajiya tayi tacema Azraa ta tattaro duk wasu 'yan kayan buk'atunta tazo sutafi can gidanta, text ta turamashi nacewa zata fita, dan kawu jiya da daddare yazo yayi mata bayani kan yadda akayi auren, tare da damk'a mata sadakinta na sisin goal, _"inkin fita ina zaki_?", shareshi tayi tabi Hajiya suka tafi dan mundin tagaya mashi ga inda zata dawuya yabarta.

Gyarane Hajiya tasa ana mata bana wasa ba dan ciki da wajenta gyara sukesha bakad'an ba cikin yini biyu komai ya canja ga jikinta, ga wani k'amshi dake tashi jikinta.

Umma ce tanemi alfarma da a k'arama mata sati kan yadda akace Azraa zata tare danta ida sauran 'yan hidimominta, wanda ba k'aramin dad'i Hajiyarsu Rasheed tajiba ganin sunk'ara samun damar gyaran jiki sosai da sosai

Hajiyar Rasheed ce zaune cikin d'aki ita d'aya Azraa kuma nacan d'akin data ware mata saboda gyaran jiki wayartace ta d'auka ta dannama Rasheed kira koda ya d'auka bata tsaya amsa gaisuwarshi ba tace "Abdul-Rasheed nasan abinda yakaika legos kagamashi, dan haka komai kake ka biyo jirgi kadawo gobe kaji nagaya maka" tanakainan ta datse kiran datayi mashi, tare da tausayin d'an nata narasa mata tagari wadda tafito daga tsotso maikyau wanda duniya da abinda ke cikinta bai rufema mahaifanta idoba.

```Bayan kwana ukku```

Yau aka kawo lefen Azraa, kaya nagani na fad'a akwati goma shabiyu fad'ar irin dukiyar da akanarkar b'ata lokaci ne saidai maikaratu ya k'iyasta da kanshi.

Fitowarta kenan daga wanka wanda aka sama ruwan wanka wasu irin turarurruka masu a zabar k'amshi da kama jiki, jin ringing d'in wayarta a kusan karo na biyar yasata hamzarin d'auka dan tunshigarta kewayen ba dad'ewa takejin ringing d'inta "ina jiranki k'ofar gida" ware ido tayi tace "bana gida"..... "what! mekikace?"

"aina tura maka sak'o ranan nace maka zanfita, shine har yau bandawo ba"......"kina ina?"...."gidansu ya Rasheed" wani tsalle yaji zuciyarshi taimashi kafin yace "good" yadatse kiran, bin allon wayar tayi da kallo, yatsina fuska tayi ta cigaba da shirinta ta share zancenshi

"oyoyo Ya Rasheed your wlcm" cewar Aysha k'anwarshi data amshi jikkar dake hannunshi wanda dawowarshi kenan daga tafiyar da yayi, wani sanyayar k'amshi ya doki hancinshi d'agowar da yayi da niyyar yaga ta ina k'amshin kefita suka had'a ido da Azraa dake fitowa daga kitchen hannunta rik'e da plate d'in abinci, saurin kawar da kanshi yayi daga gareta yana mai la'antar shaid'an dayasashi jin wani abu dangane da'ita alhalin tana matar wani, jiyayi kwata-kwata gidan ya isheshi duk d'aukin zuwan dayake yafita ranshi shiyasa ma tunfarko yak'i dawowa harsai sungama hidimarsu sannan yadawo amma Hajiya tamatsa mashi, saurin barin palourn tayi tashige d'aki, dakyar ya daidaita kanshi ya gaisa da Hajiyarshi ya wuce part d'inshi tare da al'k'awarin bazai k'ara takawa part d'in Hajiyarsa harsa Azraa tabar gidan dan ga yadda yaga alama a gidan take zaune.

Kasa samun natsuwa yayi tunda yaji Azraa na gidansu Rasheed yakuma kasa gano mai tajeyi gidan har tsawan wa inna kwanakin, kasa hak'ura yayi yashiga neman layinta tana ringing amma ba'a d'auka ba, saida yabata kusan 3 misscall kafin ta d'aga "kizo inasan ganinki gani nan k'ofar gidan Umma"... "ok, a'm coming"

"Hajiya zanje gidan Umma in d'auko abu bazan dad'e ba zandawo"....."to karki dad'e, dama yanzu zan aiki Aysha da yayanki saisu sauke ki su wuce"

"Hajiya subarshi kawai zantaka da k'afa"....."a'a Azraa barsudai su ajeki, saboda gyaran jikin da ake maki ba'ason kina shiga rana" ganin bata iya jayayya da Hajiya yasa tabi su Rasheed su sauketa, kodata shiga motar baya ta zaune kanta na sadde k'asa tun gaisuwa babu abinda yasake had'ata dashi wanda take cike da matsananciyar kunyarshi.

Suna ajeta suka wuce, wurinshi ta nufa, yana ganin ta tunkaro inda yake ya bud'e mata seat d'in gaba tashiga, wani irin mayen k'amshi ne ya doki k'ofofin hancinshi, lumshe idanu yayi tare da kamo hannunta, jin yadda yaji fatar hannunta tayi laushi da santsi kamar jikin tarwad'a yasashi fad'i "wowww masha Allah" baisan lokacin dayatashi motar ba sukabar unguwar yana maik'ara murza hannun nata da hannu guda d'ayan kuma narik'e da sitiyari

Wani k'aramin gidan hutu yakaita, bayan yakama masu d'aki suka shige, abayar dake jikinta ya cire mata ganin doguwar rigace ta atamfa jikinta yasashi zage mata zip d'in yakawoshi dai-dai k'ugunta, batayi k'ok'arin hanashiba dan tasan matsayinshi gareta, amma saidai abu guda ne bazata tab'a yadda yayi da'ita shine sex har sai ranan data tare gidanshi amma dan 'yan latse-latse bazata hanashi ba, bra d'inta yab'alle ya juyo da fuskarta suna fuskantar juna, kamo hannunta yayi suka zauna kan sofar dake cikin d'akin "My sanyin wandona zansha no....." saurin sadda kanta k'asa tayi ta dod'e kunnuwanta domin rashin kunyar Aabid tafi k'arfinta, ganin zancenshi yasata jin kunya matuk'a yasashi cabkar halalinshi yanasha bilhakk'i da gaskiya..........

*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊





©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*






*PAGE 25*






*S*aida yasamama kanshi natsuwa da'ita ta hanyar romance d'inta sannan ya kyaleta, bathroom yashiga ya tsabtace jikinshi, bayan yafito itama tashiga ta gyara nata jikin, makullen motarshi da wayoyinshi ya zara yayi mata nuni da ido data biyoshi, cikin lokaci k'ank'ani sukabar cikin masaukin bak'in, driving yake cike da nishad'i yana sakin murmurshi lokaci-lokaci, kallan sashen datake yayi yaga ta wani sunk'uyar dakai kamar duka kenan wai ita kunya bayan yasan bashi kad'ai yaji dad'in abunba harda ita



"yadai My sanyina, naga kinyi shuru ko bakigaji ba ind'an k'ara" yak'arasa maganar yana wani shu'umin murmushi, k'ara jan abayarta tayi tarufe fuska tashare zance nashi, lokaci guda kuma yasha mur kamar bashi yagama murmushi ba, cikin kausashe harshe alamar ba wasa yace "mekike a gidansu wance yaron har tsawon kwanaki batare da kin koma gidanku ba?"...... "Hajiyarsa ce tabuk'aci da inje", wani tunani ne yayi yasashi share zance.




***





Maryama ce zaune gaban Umma tanacin shinkafa da wake da soyayyen manja da yaji, saida takai geji sannan ta numfasa, ruwan randar k'asar Umma tajawo da aka zuba mata cikin kofi maisanyi kamar ansa cikin fridged tasha, "Alhamdulillah Umma, nakwana biyu banci abincin da naji dad'inshi ba kamar wake da shinkafar nan"





"santi da kawai kike Maryama" murmushi kawai Maryama tayi dan tasan Umma bata fad'i k'aryaba, "Umma bari in k'arasa gidan Hajiyar daga nan sai in fad'ima Azraa sak'on da kikace"... "To, nagode kwarai Maryama da hidima Allah yabar zumunci ya kuma rabaki da abinda ke cikinki lafiya"... "ameen" daga haka tayi sallama da Umma ta wuce gidan Hajiyarsu Rasheed wurin Azraa, kayan da Maryama takawoma Azraa ne Umma tashiga dubawa, kayan kitchen ne na zamani Maryama tasawoma Azraa a matsayin gudumuwarta wanda babu ce kad'ai ke babu acikin kayan dasuka danganci kitchen, hamdala tashiga yima Allah ganin yakawo masu wata mafita ta wannan b'angaren.





Koda ta isa gidan Hajiya ta iske anasama Azraa dilka ga jiki saida aka gama mata komai sannan suka shiga daga cikin d'akin da aka warema Azraa, "Amaryar Mr Aabid wannan irin kyau haka masha Allah"





"to kinfazo kenan zakisama kaina hayaniya".... "au hakama zaki fad'a yayi maki kyau, ni ba wannan ba Umma tace ki sanarda mijinki sukawo motar d'aukar kaya gobe" shuru Azraa tayi ta kyaleta saima tashi datayi ta bud'e wadrop ta fiddo wasu IV Card tamik'ama Maryama "gashi nan inkinje skull gobe kiba Rumanah akwai wasu fan's d'inmu dazata ba munyi waya da'ita d'azu"..... "ok Ma" murmushi tayi ta zauna kusa da'ita, dialling number Mr Aabid tayi





A b'angarenshi yana zaune kusa da mahaifinnashi yana ganin kiranta yadatse, kashe wayar yayi gaba d'aya yamaida hankalinshi kan maganar da Daddyn nashi kemashi



"kasan kafin in amince da auranka da wannan yarinyar kasan nace maka akwai sharad'i ko?, to sharad'in bawani bane shine banyadda kasata wannan gidan naka ba dan bata can-canci zama a cikinshi ba saidai kanema mata gida dai-dai da irin na iyayenta kasata tunda kaji kagani sai kuyita rayuwarku da'ita irin ta talakkawa"..... "Daddy ina neman alfarma a bari ta tare albashi daga baya sai in nema mata wani gidan irin wanda kakeso"




"abinda baka isaba kenan dole kaje kayi rayuwa da ita irin tasu ta talaka sannan kagane banbancin da nake k'ok'arin gwadamaka, dan haka tashi kabani wuri nariga da nagama magana, kuma banyadda ka kamamata unguwa mafi tsadan rayuwa saidai local wuri wanda ba ruwa ba wuta kaji nagaya maka ban kuma amince kasai injin maibada hasken wuta ba, shashashan banza shashashan wofi tashi ka b'ace man da gani" cika yayi da mamakin Daddyn nashi duk irin hallacin da iyayen Azraa sukayi masu baigani ba, kan yadda mahaifin Saleemah yatozartasu a cikin bainar jama'a amma baisa ya saduda ba saima sakayyar da yakeson yima wanda suka rufama nashi asiri ta hanyar k'ask'antar da d'iyarsu, gwiwa sab'ule yabar palon, wayarshi ce yakunna baifi minti biyu da kunna taba sak'on Azraa yashigo wayarshi na sunason a turo motar kwasar kaya, kanshi ne yaji yamashi wani iri samakon zafin da mahaifin nashi yake nema jefashi ciki dan mi zai tozartashi akan dole saiya kama mata gidan haya alhalin duniya tasan sunadashi kuma hakan na iya jaza masu zagi daga shi har Daddyn, amma ai koda yake hakan bazai hanashi bata ciyarwa maikyau ba ko sutura maikyau kuma bashi da damar da zaice bazai kusanci matarshi dukda tana gidan haya, murmushi yasaki ganin sharad'in na Daddy yazo mashi da sauk'i dan baiyi tsamanin haka daga gareshi ba tunda ba Azraa kawai zatayi rayuwar gidan haya harda d'an nashi mafi soyuwarshi, da wannan tunanin yasamu kwarin gwiwar kiran MM dansu tsara yadda abubuwa zasu tafiyarmasu da batun neman gidan haya.





Gida irin wanda Daddyn nashi keso suka kama, saidai sukad'a ne a ciki danko gidan k'arami ne sosai palourn guda sai d'akin bacci shima guda d'aya sai d'ankaramin kitchen da sito, sai filin tsakar gida d'an tsukut, 'yan jere cika sukayi da mamakin gidan da za'akai Azraa ganin yadda lefenta yakasance uwa uba sadakin sisin goal da akayimata dashi amma ace an ajeta a irin wannan gida wanda basa tunanin ko wutar nepa akwaita unguwar, take suka shiga tsegumi na mata wanda Hajiyar Rasheed najinsu tayi shuru dan itama duk jikinta yayi sanyi kan wannan al'amari, haka suka gama jeren ko ruwa ba'a kawo masu ba daga b'angaren ango wanda yak'ara tabbatar masu lalle akwai matsa kila dangi ango basa maraba da'ita, wanda rabin kayanta basu samu matsugunni a gidan ba, dan Rasheed bak'aramin bajinta yayi mata ba wajen yak'awata mata palourn nata da kayan kallo da kujeru na keta sa'a.




Ba abinda su Adama matar kawu basu fad'ama Umma ba dangane da gidan Azraa, tab'e baki Umma tayi tace "duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kandoka, ba ita taji tagani ba ai sakayya yanzu tafara gani inma dangin mijin kad'ai ne ke basasanta banda mijin ta auna arzik'i" daga haka ta cigaba da hidimominta dan bak'i sunfara sauka 'yan biki.





Duk wasu zurga-zurga yana k'ok'arin yaga ya danne zuciyarshi yana mata musamman b'angaren k'awayenta wurin ganin yakaisu inda suke buk'ata, hankalinshi bak'aramin tashi yayi ba jin inda Aabid zai'aje Azraa, har yafara sama kanshi zargin anya ba sha'awarta yake ba dazaran ya biya buk'atarshi ya wofintar da'ita, saurin istigifari yayi domin zato zunibi koda yakasance gaskiya, haka aka cigaba da gudanar da shagulgulan biki,
shirye-shiryen zuwa dinner ake wanda zasu gudanar dashi d'ank'ani hotel




Tunda ta d'aura idonta akanshi taji wani miki ya harbi k'ahon zuciyarta wanda tarasa sanin komiyeshi, ko yanzuma anata hidimar d'aukar k'awayen amarya zuwa d'ank'ani, parking motarshi yayi nesa data abokan ango yafito yana kallan k'ofar gidan Umma yadda mutane keta shige da fice, kamar ance ta kalli sashen da yake suka had'a ido, jitayi wani abu na fizgarta nadataje wurinshi, saidai kawai ganin kanta tayi a gabanshi, soshe-soshen kunya tafara tanason barin wurin, "bissimillah shigo mana" daga haka ya bud'e mata motar tashiga cike da kunya, wanda shi yayi tsaye yana kallon duk motsin kowa (R²)





Saida aka kwashe duk k'awayen amarya amma yana tsaye yakasa bin ayari yatafi kamar mai jiran wani abu, wata black hommer jeep sabuwa dal mai duhun gilasai tayi parking k'ofar gidan Umma, mutuwar tsaye ce takamashi dan saida komai ya d'auke mashi na wucin gadi kafin ya dawo duniyar sama jannati, Azraa ce cikin shiga ta alfarma na wani material mai azabebben kyau da tsada kalar ruwan hoda da ratsin bula jikinshi ammata d'inki fited gwon wanda yayi matuk'ar fito da surar jikinta sai head blue datayi amfani dashi akanta da takalmi bulale sai k'aramar jikka ta hannu bula, MM ne yafito daga mazaunin direba ya bud'ema Azraa baya tashiga yayinda Maryama data rik'omata hannu tashiga gaba, take MM ya lula kan motar saman titi sai d'ank'ani, yayi danasanin tsayuwar da yayi a wurin ganin irin kayan takaicin da yayi arba dashi, naganin Azraa tazama ta wani batashi ba duk irin dakon sonta da yayi shekara da shekaru amma wani lokaci d'aya ya kwace mashi, baisan lokacin da wasu zafafan hawaye suka rink'a sauka kan fuskarshi nazafin rad'ad'in rabuwa da Azraa, a zafafe ya bud'e motar yashiga dan yamanta da wata Rumanah dake cikin motar tund'azu, kallanta yayi da niyyar ta saukar mashi a mota yafasa kaita, saidai kash!! tayi mashi kwarjinin da bazai iya yimata wannan rashin mutuncin ba ganin lokacin data d'auka tana zaman jiranshi, jan motar yake slowly kamar baisan tafiya suka harba saman titi sai d'ank'ani.










Shagali yai shagali bakajin komai natashi sai kid'a, Amarya da ango aka buk'ata dasu k'awata wurin da rawa, kamo hannunta yayi suka shiga filin rawar, take abokan ango dana amarya da sauran 'yan uwa da abokan arzik'i suka rufesu suna masu lik'i, Rasheed shima baiyi sanyaba wajen nuna bajintarshi nayiwa Azraa lik'i, yana tunkaro inda suke Sir Aabid yak'ara rungumo matarshi yana wani kareta, dukda yaga abinda yayi baisa yafasa ba yak'arasa yayi mata yayafin bandir d'in riyal 50, saida yaga bandir d'in sun k'are sannan yabar filin zuciyarshi cike da wani irin mahaukacin kishi, dukda yasan tayi mashi nisa na har abada, kasa zama yayi yabar hall d'in, tafe yake yana share hawayen dasuka kasa tsayawa daga idaniyarshi.........










*Mrs Abdul sule*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊









©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK.....*







*SADAUKARWA*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*





*PAGE 26*






*D*uk tana lura da yanayin da yafita wanda kwata-kwata bataji dad'in hakan ba domin har abada bazata tab'a manta alkhairinshi garesu ba, ganin tashiga wani d'an yanayi tun lokacin da Rasheed yafita yasashi yimata rad'a dai-dai kunnenta wata magana ya gayamata wanda take tasaki murmurshi akan fuskarta, aka cigaba da gashi



*


Da wani irin mugun guda yafita cikin hotel d'in, zuciyarshi namashi k'una.......





Tun shugowarta hall d'in gabanshi yabada dammmmmmm, mazewa yayi kamar baigantaba wanda har ido saida suka had'a da'ita, cikin izza da tak'ama tak'araso fagen rawar, lik'i tashiga yima Mr Aabid da dallors na isa da tak'ama dan har wani goga jikinta take danashi dama gashi d'inki rigar tata duk rabi k'irjinta waje, ganin barikin datake mashi ne yasa Azraa cire hannunta dake cikin nashi, takoma mazauninsu, cikin hikima ya silale yabar fagen rawar, haka a cigaba da gudanar da shagalin har zuwa k'arfe sha biyun dare, bankwana MM yayi da Mr Aabid da sauran abokansu ya d'auki matarshi suka tafi dan yasa ankawo mashi motarshi wurin, a gurguje yayi bakwana da mutane shima ya d'auki Azraa dan yamaidata gidan Umma dan sai gobe ne tariya, tunda suka taho take lura da take-takenshi ta shareshi, donko bak'aramin shak'atayi ba ganin wannan mai zubin karuwan dake mashi lik'i, ganin tak'i bashi had'inkai yasa yashafama kanshi lafiya ya maida hankalinshi kan steering.




Koda suka isa saida safe kawai tayi mashi takama gabanta, zubamata idanu yayi harta shige gida, cike da rashin kuzari yaja motar yatafi.





"Amma Najancy ba 'yar air irinki, aina aza kinshafe babin Aabid a rayuwarki duba da irin abubuwan dasuka faru a baya"..... "Meenat kenan kina tunanin duk irin b'ataman lokaci da yayi natsayin shekaru ina jiranshi zaitafi a banza, aikema kinsa ba abu bane maiyuwuwa da hakan zaisa inbarshi yatafi a banza ko kinmanta wacece Najancy in tuna maki"




"haba tawan aiko shed'an na tsoron tuggunki, bare mutum"....."barshi kawai bazai gane bashi da wayo ba sai gobe, ankaimai amarya" tashek'e dawata irin dariyar mugunta "adaiyi mashi arzik'i yasamu damun furar gobe"..... "hahhhhhhhhhhh ai tundaga yau nafara dasa mashi makaman yak'ina, kedai ki zuba ido kiyi kallo, ba boka ba Malam amma saina saukar mashi da wannan girman kan nashi da nuna isa da iko"...... "adai sauk'ak'a mashi kinsan sabon shiga da d'aukin abun kamar maikai ciki yaye".... "niko zan shaidamaki shi sabon shiga ne, danko duk irin kissata da kisisinata baisa ya kusance niba, sai d'an banza romance nad'aga hankali"......"waishi waliyi" cewar Meenat, tafawa sukai suka cigaba da dariyar shak'iyancin tasu........






**




Washe gari da misalin k'arfe biyar da rabi aka sada amarya da d'akinta, Hajiyarsu Rasheed ce da Umma da sauran wasu 'yan uwa najiki sukayi mata nasiha akan sabuwar rayuwar dazata shiga daga haka aka d'auketa sai gidanta, wanda sai bayan da akai sallar ish'sha'e sannan 'yan kai Amarya sukabar gidan.






Duk wani motsi da Aabid zaiyi, Daddy yasamashi ido kan kozai canja wani sharad'i da ya gindamashi mussaman yasamu wanda ke kula da gidan.......




Su MM ne ketamashi shegantaka kan yace bawani wanda zairakashi balle yace zaisayi bakin matarshi, duk shegentakar dasuke mai yanajinsu yasharesu dan Alla-Alla yake su kyaleshi yatafi dan yasan bak'aramin tsuma kanshi yayi ba, dan tunkafi yafarajin kaziri-kaziri cikin wandonshi kwara su gyaleshi ya sanfe, ganin sun tusashi gaba yasa yayi masu dibara yace masu "one minute akwai sak'on dana manta banbaku ba" haba yana shiga motar saida k'urar motar kawai suka gani yakama gabanshi, Hamdala MM yayi dan harga Allah bayason sauran abokanansu susan ina Aabid zai zauna dan zai'iya kawo surutai iri-iri, danshi kad'ai yasan abinda kefaruwa, d'aya daga cikin abokan nasu ne TJ yace "Allah tsorona karya halaka masu d'iya, dan naga yasin a matse yake" dariya suka kwashe da'ita, suka cigaba damashi shegantaka iri-iri, daga bisani sukayi sallama da junansu kowa yasan inda dare yayi mashi.......




Cike da kwarin gwiwa najin cewa shi ango ne, yake kwad'a sallama, jinshuru ba motsin kowa ya tabbatarmashi da kowa yakama gabanshi, labulen d'akin yaye ya hangeta can k'arshen gado ta takure, takawa yayi har inda take ya yaye lullub'in datayi, "masha Allah" ya ambata a fili, zauna yayi dab da'ita ya rungumuto jikinshi "My Sanyina, Allah yanufa yau gani gaki a matsayin ma'aurata, godiya ta tabbata ga sarki Allah maikowa maikomi" fasali ya yaja ya cigaba da cewa "My Sanyina tashi mumik'a godiyarmu ga sarki Allah daya gwada mana wannan lokaci maidaraja"... "nayi sallata, saidai kai katashi kayi" tafad'i haka ne dan tana fashin sallah... "nasan dakinyi taki, wannan ta dabance" Alla-Alla yake ta tashi dantsumi yafara aiki, anfara kad'a mashi alanta, ganin kamar zata b'ata mashi lokaci yasashi mik'ar da'ita, bazato yaji ringing d'in wayarshi, cika yayi da mamaki wane marar hankalin ne zaikirashi a irin wannan da d'add'an lokacin ganin sunan N nayawo kan screen d'in wayarshi yasashi fad'uwar gaba, dan yasan shed'anci irin na Najancy, tabbas taga harafin N akan wayar, amma baisa ta nuna mashi ba, saurin kawar da wayaryayi ya maida cikin aljihu, kamo hannunta yayi a lokaci wani kira yasake shigowa, still now harafin N ne yak'ara bayyana dogo tsakiya yayi dan karta gane macace takirashi yace "Najasi ko kai mayene yasin yau kana bari na, tunda can bakayi mani Allah yasa alkhairi ba sai yanzu danake shirin sauke lodi"



Fuzge hannunta tayi, shikuma cikin dubara ya turama Najancy txt dan baisan yakashe wayar Azraa tagane macece ke kiranshi, txt d'in nashigowa ko dubawa batayi ta sake danna mashi kira, komawa tayi gefen gado tasamashi ido, k'in d'aukar wayar yayi wannan karonma harta tsinke, daga can b'angaren Meenat kecema Najancy "ki kyaleshi haka karki hana abashi tuwan yau".... "aiba tuwoba hatta mai gaba d'ayan saita hanashi"






"tabbb aiko inkiyi mashi haka bakiyi mashi adalci ba" watsa mata wani mugun kallo Najancy tayi tace "ni adalci yayi mani kenan daya b'ataman lokaci yakuma hanani kula kowa k'arshe yak'i aure na, har kike tunanin zan sarara mashi" daga fad'in haka taciga da dannama Mr Aabid kira





"kad'aga mana kila tana buk'atar jinka yanzu" tayi maganar cike da k'ulafacin kiran dataga ana mashi, ta 'yan maza yayi ya d'aga kiran, jin and'aga tace "ango kasha k'amshi barka da warhaka" tayi maganar cike da duniyanci, dakewa yayi yace mata "i'm at home, i will call you back" daga haka ya yanke kiran, shek'ewa sukayi da dariya suka tafa itada Meenat "bari in bashi 30 minutes kafin yak'araji na" daga haka suka cigaba da firar duniyancin tasu




Jin har and'auki 3 minutes baiji kiranta yashi yazama relax, "My Sanyina pls tashi muje muyi sallah muci abinci"... "nafad'a maka nayi sallah, saidai kai kaje kayi taka" agurguje yatashi yashiga band'aki ya watsa ruwa ya d'auro alwala, bayan yayi sallah yakama kan Azraa yayi mata addu'o'e, jiki na kyarma yatafi kitchen dake tsakar gida yad'auko masu plate, spoon fork, and cups ya aje masu a tsakiyar palourn dan yafi cikin d'akin walin fili, duk tana lura dashi tak'i nuna mashi alamar tana fashin sallah dan ta horas dashi kan lik'in dataga wata tana mashi jiya da kuma wayar da aka ishesu da'ita yanzu wanda take da tabbaci macece maikiran





Bayan yafito da kazar da yashigo da'ita da sauran drink's da yazo dasu, yashiga ciyar dasu, da kamar bazata amsa, amma cikin salo da yauk'i tarink'a amsa harya ciyardasu suka k'oshi, cikin kyarma yakwashe kayan yamayar dasu kitchen, hannunta yaja suka shige cikin uwar d'aka, kayan bacci yad'auko masu, ganin yanada niyyar sasu a gabanta yasa ta d'auki nata tayi palour, saida suka gama kintsawa suka haye gado, har yajawo wayarshi dake bisa bedsite drawer zai kashe yatuna basu da wuta kuma ko fitilar torchlight babu kuma yasan zasuyi amfani da haske musamman inkomi yamanuna







Wasani yake mata amma tanok'e kamar bada ita yake ba, kamar daga sama yaji ringing d'in wayarshi, hannunta takai wurin wayar da zummar d'auka shima yakai nashi dan yayi imani da Allah wannan ibilishiyar yarinyarce, Allah yabata nasara tarigashi d'auka, wurin amsa kiran ta d'aga jin muryar mace yasa tabashi wayar, daskarewa yayi a wurin dan yasan and'ana mashi bom d'in da'aza hanashi wargaje gajiya, amsa yayi yakashe wayar gaba d'aya, take duhu ya gauraye d'akin lalubarta yashigayi amma tana tureshi, haka ya cigaba dayi amma tana k'ara tureshi, ganin bazata saurareshi ba yasa yace "duk hukuncin dazakiyi mani akan haka kiyi mani, amma karkice zaki horar dani wurin hanani halalina, zanjuri komai nadaga hukunci daga gareki amma wallahi banda ta k'urya mai gumin dad'i kinji nagaya maki" yayi maganar in serious tune........








*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊





©
*KAINUWA WRITERS ASS🀝🏻*
®
*HALIMA MK......✍🏻*





*SADAUKARWA*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*





*...............HBD Sameenah Aliyu, Allah yak'aro shekaru masu albarka.....*





*PAGE 27*







*C*ika tayi da mamakinshi,da kuma ko kwanton anya ba jikinta yakeso ba, amma baya ga haka ya za'ai yayi wannan furucin harda cewa zai'iya jure komai amma banda ta hanashi yin auratayya da'ita, Wanda shigowarta gidan ko a wanni bata rufe ba amma tafara fuskantar bacin rai nadaga kiraye-kirayen wayar 'yan matanshi, anya batayi kuskure auren Mr Aabid ba a rayuwarta, wata zuciyar kuma tana cemata, bakomai bane kika fara gani illah sakayyar Rasheed, da kuma k'in cizewa kibi umarnin Mahaifiyarki, gashi kin fad'a gidan da ba'asan mutuncin talakaba, numfasawa tayi kan tunanin da tashiga, "Azraa nasan kinajina kikayi shuru kamar badake nake ba"






"Sir Aabid, ka kyaleni bacci nakeji bani da time nawasu zantukanka, a biii" tayi hakane da yashafa mata lafiya, dan bazata tab'a yarda ya kusanceta ba alhali bata ida tantace son dayake mata ba, don tanason ta banbance so ne aranshi ko sha'awa, dan tafara tsorata da lamarinshi, cigaba yayi da lalubarta dan yakai k'arshe wajen yaga yasauke lodin dayatarama kanshi, bugemashi hannu tayi dayake shirin turamata cikin riga, "pls,,, Azraa ki natsu, kibani wallahi ina cikin wani hali, dan Allah kitaimaki d'an almajiri" yak'arasa maganar cikin k'osawa dayasamu biyan buk'atarshi, zumbur tamik'e tabar bisa gadon, ganin tabar bisa gadon ne yasashi kunna wayarshi, fitilar wayar ya kunna take haske ya gauraye cikin d'akin, tunkarota yayi haik'an, ganin yana nufo inda take gashi kayan aikin nashi sunyi ishe-ishe sun cika wandon kayan baccin dayasa yasata fad'uwar gaba, hanyar guduwa ta nema amma yatare hanyar dazata wuce tayi palour, matseta yayi jikin bango wanda ko numfashin kirki da kyal takeyi gashi yana wani turomata sandar girmanshi ga jikinta dukda baifidotaba amma tanajin yadda yake goga mata ita akan mazaunanta, ganin wannan ce Damar dazata kwatarma kanta 'yanci daga gareshi nata gane son Allah yakemata koko hallitar jikinta yakeso, musamman dataga yanzu tana jinin al'ada wanda ko kiranta yayi ga shinfid'arshi dan tabijirema buk'atarshi bataje ba tasan bazata kwana cikin tsinuwar mala'iku ba, domin Allah shiya haramanta saduwa da iyali matsawar suna cikin najasa, amma kuma bazata nuna mashi tana cikin najasa ba har sai randa ta aminta da kowane kalar son yakemata, k'ok'arin kaita gado yake, amma tana tirjewa cikin fusata da k'osa da abinda take mashi yace







"Azraa wai mekike nufi dani ne?"..... "inaso ka kyaleni bana cikin moon d'ina".... "olright" daga haka ya janye daga rik'on da yayi mata, take zuciyar 'yan miskilancin suka motsa mashi, zuciyar maza ta harzuk'a, filo ya d'auka ya nufi palour dashi cike da tunani kala-kala a ranshi, da kuma k'udurin bazai tab'a nemanta ba harsai randa take cikin yanayi makyau tunda yanzu tace mashi bata cikin moon d'inta, tsoki kawai yake saki lokaci-lokaci jin yanda kayan aikin nashi ke k'ara kunburi hankalinshi nak'ara tashi yarasa yazaiyi juyi kawai yake nata k'ara sautin tsakinshi, tare da tsinema d'an yarbawa a ranshi da yakawo mashi wani had'i nasu na yarbawa harce mashi yake kahek'a-kahek'e inkaga yayi kunfa saika shanye, togashi yashekoma kanshi bala'i yarasa inda zaishek'e ayarsa, tanajin duk tsakin dayake tayi kwanciyarta ta kyaleshi






Ganin yana neman halaka kanshi yasa yanufi toilet, ruwa kawai yaita ambamamata tare da addu'a har Allah yasa ta kwanta, alwala yayo yashiga jera nafiloli, Asuba tagari A² lol........





***






Rasheed Kwana yayi cikin wani mayuwacin hali ganin daren wannan ranan mai cike da tarin damuwa, wani ya mallaki abinda yake matuk'arso da muradin kasancewa dashi har k'arshen rayuwarshi, amma ina Allah bai hukunta hakan gareshi ba, saima waninshi dayaba wanda yasan mawuyacin abune yakyaketa baiyi mata karatun bebeba, haka yacigaba da juyi har zuwa k'arshen dare, tare da addu'ar Allah yabashi mace tagari da kuma hak'urin rashinta.............








Koda asuba tayi yatasheta tayi sallah shi kuma ya wuce masallacin dake cikin unguwar dan gabatar da sallah, saida gari yasha rana tafara fitowa sannan yadawo gida, lokacin Azraa ta gyara ko ina na gidan ta tsabtace jikinta cikin shigar atampha super vilisco d'inki riga da siket wanda yayi matuk'ar amsar jikinta hips d'in nan kamar an aza kwarya, sai hidimar had'a masu break take dan batasaran daga gidan inlow nata zasu kawo mata, wani irin mugun miyau ya had'e arba da yayi da mazaunan Azra datake ta juyasu kamar da gayya, wanda naturally haka yanayinta yake shiya koda yaushe take suturta jikinta da abaya maib'oye surarta, baisan lokacin da yashafi gabanshi ba, saurin shigewa d'aki yayi ganin ana neman fara buga mashi alanta yana cema kanshi "ba alanta zaku kad'a mani ba ko sklewu zaku kad'a wallahi nasan Azraa bata bani inyi koda d'and'ani haukacine" nanfa yashiga kwashema Najancy albarka tunda duk itace sila da yanzu yana cikin washshagale, jin basarara mashi zasuyi da kid'an alantarba yashiga matsa k'afunshi dan bak'arami tsumashi d'an yarbawa yayi banda wanda yaje yaita bankama kanshi, kasa hak'ura yayi ya isketa kitchen, saida rumguma taji kawai daga bayanta dan kwata-kwata bataji motsin shigowarshi ba, hannu yasa yakashe gas d'in yakamo hannunta sukabar kitchen d'in, baizame ko ina data ita ba sai saman sofa, zip d'in rigarta ya zuge yashiga murzar nasha nunta, lamo tayi dan harga Allah sak'on nashi nakaimata yadda yadace amma martani ni kawai bazata iya mayarmashi ba, jin tayi lamo gashi har wani k'ara bank'aro mashi sutakeyi yasashi saurin zare rigarshi, ganin yana neman kwale wando yasata tureshi tashige cikin d'aki harda rufe k'ofar d'akin da key, ajiyar zuciya tasaki ganin tasha da kyar





A b'angaren Aabid kau yakai k'ololuwa wajen k'uluwa kan salon da Azraa take nema kawo masu daga kawota jiya, cike da sanyi jiki ya nufi toilet, sakarma kanshi ruwa yayi sannan yafito, har lokacin bata bud'e ba yasashi fara knocking d'in k'ofar, "pls My Sanyina kibud'e akwai abinda zan d'auka, albarshi inna d'auka saiki rufe" da kamar bazata bud'e ba, amma wani tunani datayi yasa ta bud'e mashi, ko kallan inda take baiba ya wuce wurin closet ya d'auki wani boyel fari da aikin brown yafice palour, tab'e baki tayi cikin ranta tace tafi nono fari, cikin shirinshi nafita ya lek'o yace mata "My Sanyina zanfita banjimawa zandawo", dai-dai lokacin kira yashigo wayarshi, "on my way" daga haka ya yanke kiran, "ba wani abudai ko, kinsan halin tafiya kar abubuwa surik'e ni"....... "bakomai" tayi maganar cike da sanyi jiki dan a tunaninta ko wajen mai harafin "N" zashi,, wanda shikuma a b'angarenshi zaije yayi sallama da fans d'inshi da sukazo mashi daka sassa daban na cikin k'asarnan harma da k'asashen k'etare, jin yadda tayi maganar yasashi matsawa kusa da'ita bakinsu ya had'e yashiga tsotsa, take yaji kamar wanda kunama ta harba yaji joystick d'inshi nashirin tashi, take yazare harshenshi daga cikin nata da yake wasa dashi, numfashi yashiga- mayarwa kamar wanda yabuga wasan ball, waving hand d'inshi kawai yayi mata yabar gidan dan ko magana yakasayi.......








Koda yaje MM duk yasallami da yawa daga cikin abokan nasu k'alilan ne basu wuce ba, Tj ko dawa Allah ya had'ashi in ba Aabid nan yashiga yimashi tsiya kala-kala, dakyar yasamu yaja MM sukabar wurin, gidan Umma suka nufa danyi godiya da angwaye ke zuwa bayan amarya ta tare, daga gidan Mr Aabid yayi sallama da MM ya wuce gida dan gaidasu Daddy da sauran 'yan uwan dasuka zo biki, nan ma baib'atama kanshi lokaci ba ya wuce gidanshi.........










*MRS ABDUL SULE*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊





©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK..............*





*SADAUKARWA*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*







*PAGE 28*








*H*ad'uwar Najancy da Mr Aabid tasamo asaline a wata semina da aka turashi garin kano ta tsawon sati biyu, sun had'u da Najancy a sahad store yaje yin shooping itama ta ziyarci wurin, Najancy wata irin shu'umar macace data kware wurin iya bariki, lokaci guda taji Sir Aabid yatafi da imaninta, wanda shi ko kallo d'aya yayi mata kawar da kanshi gareta duba da yanayin shigar datayi gatadai mace har mace amma ta zubda ni'imar da Allah yayi mata wurin bayyanar da'ita gakowa maimakon ta killaceta, ganin yagama d'aukar abinda yakeso ne yasashi nufar wurin biyan kud'i, saurin riganshi tayi dan tana hankalce dashi, koda sukaje wurin biyan kud'i take tabayar danashi dukda kwata-kwata baiso hakan ba, rigashi fita tayi daga shopping mall d'in amma abin mamaki sai kawai ganinta yayi jingine da motarshi wanda ya cika da mamakin ya akai tasan motarshi ce, basarwa yayi kamar baiganta ba amma tayi saurin tarar gabanshi take tasakar mashi wani shu'umin murmushi, cike da kissa da kisisina da rangwa tasamu taja hankalin Aabid har yasaurareta dakyar da su d'in goshi ya yarda yabata digitals d'inshi, tundaga nan alak'a ta shiga tsakaninsu wanda har masaukinshi take kawo mashi ziyara, tun yana sharewa har ta ribba ceshi ya cigaba da kulata, naci da jajircewa kan duk wani wulak'anci da yake mata yasa ta shawo kanshi har ya amince zai aureta da sharad'i saita daina duk wata shiga marar kyau da kula kowane namiji, sannu kan hankali yafara romance d'inta amma baitab'a kusantarta ba saidai yana wasanni da'ita over dayaji zai zarce zai zare jikinshi daga gareta wanda bak'arami k'ona ran Najancy yake ba, daga bayane yagane cewar tana kula wasu mazan bayanshi shine dalilin dayasa yaja baya da hudd'a da'ita, daga haka dai suka cigaba da tarayya da'ita sama-sama dukda har ziyara tana kawo mashi sokoto, kwatsam saidai maganar aurenshi taji wanda koda wasa baigaya mata ba, shine dalilin dayasa tayo tattaki tunda kano ta dabo tumbin gwiwa har zuwa birnin na Shehu................




*




Driving yake cike da nishad'i kiran d'an yarbawa ne yashigo wayarshi, parking yayi gefen titi lokacin wayar harta tsinke, bin bayan kiran yayi danma ko baikirashi ba to yazama dole dama shi yakirashi, "Ango,,,, Ango,,,,, akwaifa sabo kaya in kanaso ankawosu daga can gari namu" muryar d'an yarbawa ce dake ta zuba tund'aga d'aga kiran da Mr Aabid yayi mashi "d'an yarbawa wane sabon kaya wanda kabadama akwai matsala inda yanda zakai ka warwareshi to kabani, dan gaskiya ina cikin wani hali"






"oga ban gane ba kako hek'a yanda nace kayi, danko kayan nan yanada kyawu sosai-sosai kuma amaryama zataji dad'i sosai"... "kai d'an yarbawa da Allah iman shuru, kaida baka gane hausa sosai, cemaka nayi wannan na shek'awar idan mutum yashashi in baiyi abinba ba wani magani da mutum zaisha yadenajin komai cikin jikinshi"...... "owooooooooo nage abinda kana nufi, gaskiya yin wannan shine kawai samu sauk'i naka"..... "to banni iyanan d'an yarbawa ina cikin wani hali" daga haka ya yanke kiran, dariyar shak'iyanci d'an yarbawa yashek'e da'ita yana k'ara nanata abinda Aabid yace mashi kafin yabashi maganin har cewa yake "wanda yafi kowane k'arfi zaka bani zanbiya konawa ne" dariyarshi yaciga dayi yace a fili "dana sani nabashi falle gado da yau yayi kwanan itigi" dariyar ya cigaba dayi har yana rik"e ciki, kafin daga bisani ya rufe shago dan ango meenal yakirashi (lol...)






Jikinshi ne yayi sanyi lallai d'an yarbawa bak'aramin bom ya had'amashi ba, parking yayi bakin inuwar dogon yaro (bedi) dan gida baida inda mutum zaishiga da motarshi, kwance ya isketa bisa sofa tana bacci, sand'o yayi ya shige cikin d'akin kayan jikinshi ya rage dagashi sai singlet da shortnika yafito, lallab'awa yayi ya kwanta gefenta dukda yasan kujerar bazata iya d'aukesu ba, jin mutum kusa da'ita yasata saurin firgita, ihu take da niyyaryi yayi saurin had'e bakunansu wuri guda, wani irin salo ya shigayi da harsunan nasu, hannunshi ya tura cikin rigarta Allah ko yabashi nasarar cafkar dukiyar fulaninta take ya birkice a wurin makaman aiki suka shiga nasu girman, bakinshi yazare cikin nata yamaidashi kan breast nata take tayi wani irin zullo wanda Aabid yaji kamar numfashinshi zai d'auke dan dad'i, ganin yana neman kwale gajeren wandonshi yasata saurin tureshi ya fad'i k'asa, d'an yarbawa kawai yake kwashema albarka dashi da Najancy, dan yana ganin duksu suka jefashi cikin wanga yanayi, mik'ewa tayi tanufi hanyar bedroom tad'atse, sallamar da ake ta kwad'a masu daga tsakar gida yasa Aabid yin mazurai, gashi dai Azraa tashige cikin d'aki ta rufe kayanshi na ciki gashi kuma bak'i nasallama daga k'ofar palour, bubbuga k'ofar yayi a hankali wanda itama Azraa taji sallamar da akeyi ne yasa ta nufo palourn, bud'e mashi tayi sukayi kicib'is bakin k'ofa hararar k'asan ido yayi mata yarab'e ya wuce, fita tayi tana mai amsa sallamar da akeyi, ganin su Rumanah yasa ta fad'ad'a dariyarta






Iso tayi masu har cikin palourn, ruwan swan da cincin, dibilan, alkaki, cake da dai sauran tarkace kayan biki ta wadata gabansu Rumanah dashi, "Amarya kinsha kyau meye sirrin kwana d'aya naga duk kincanja kodai duk gajiyar daren jiyace" yatsina fuska tayi tace "share kawai bazaki gane ba".... "nima bazanso in gane ba" suna firar tasu k'asa-k'asa dan kar Aabid yajisu dan Azraa tayi mata alama da yananan, bata d'auki lokaci ba ta tafi, Mr Aabid ne yafito daga cikin d'aki ya nufi hanyar k'ofar gida, gark'ame gidan yayi tare da cema Azraa kowa ya buga karta bud'e hutawa yakesonyi........


*


Duk wanda ya dubeshi yasan baya cikin yanayi maidad'i, kallon tausai Hajiyarshi tabishi dashi har yabar cikin palourn yana wani layi kamar wanda yasha kwaya.......




*


Family Aabid ne zaune suna ta firar bikin nashi da kuma nuna rashin jindad'in yadda mahaifinnasu yace dole sai Aabid yayi rayuwar gidan haya kan wani dalili nashi marar tushe ko mafari, Aymana ce yar autarsu tace "ni wallahi ya Aabid yaban tausai sosai Momy kinga gidan da suke zaune ko wutar nepa babu unguwar"...... "to Ummu ya za'ai mahaifin naku ne yayi nisa kan........." takun tafiyarshi sukaji alamar zaishigo yasa Momy yin shuru bata k'arasa zancen datayi niyyar fad'aba, gaishe sukayi gaba d'ayansu, kafin yashige, dai-dai zai hau wani step da zaisadashi da dinner area yayi missing step, take ya yanke jiki ya fad'i tayis ya yankan mashi yatsan k'afa........



*


Zaunar da ita yayi saman cinyarshi, zare mata kallabin kanta yayi yashiga wasa da gashin kanta da hannu guda yayin da hannun guda na wasa da cibiyarta, lamo tayi jinkishi tana amsar sak'on dayake aika mata, ganin sak'on namata dad'i yashi kai hannunshi cikin rigarta, wasa ya cigaba dayi dasu yana wani fito dasu daga cikin riga kamar wanda zaishayar da yaron dakeshan nono, lumshe idanunta tayi dan kunyar abinda yakemata, ganin ta rintse idanunta yasa sakarmata light kiss ga kumatu "pls Maisanyi na kin amince inmaidake cikarkiyyar mace kamar sauran mata da suke da aure?" girgiza mashi kai tayi alamar bata amince ba.......






_kuyi managed jiki da jini_






*MRS*hi
🍊🍊🍊🍊🍊🍊
*AZRAA*
🍊🍊🍊🍊🍊🍊



©
*KAINUWA WRITERS ASS✍🏻*
®
*HALIMA MK*






*SADAUKARWA*
*AISHA ALI GARKUWA*
*BIEBEE ISAH*




*PAGE 32*






*D*ak'yar yasamu yatashi ya nufi toilet dan jikinshi har wani makarkata yakeji kan tsananin buk'ata,, ruwa kawai yaita sakarma kanshi har saida yaji yafara dawowa dai-dai sannan ya d'auro alwala yafito,, lamo tayi kamar mai bacci amma ba baccin take ba asalima sotake tashiga toilet dan ta wanke najasar dake jikinta amma kunya ta hanata yin haka,, cikin dakiya ta tashi ta nufi hanyar toilet,, niyyar yin wanka janaba ta d'aura dukda dai bashigarta yayi ba amma saboda abubuwan dataga sunfita daga gareta kawai yasata yin wanka, bayan takammala ta fito d'aure da towel sai abaya data rufe jikinta da ita dan karyaga kanta a jik'e,, kamar munafuka ta nufi wurin clos'et dan d'auko wata rigar baccin dan waccan tab'aci da ruwan m....,,


Saurin cimmata yayi wurin ma'adanar aje kayan, hijabin jikinta ya cire take sumar kanta datake jik'e tasauka kan kafad'unta ruwan wankan datayi yana d'iga saman jikinta,, lumshe idonunshi yayi yana shak'ar k'amshin ruwan wanka nata da yahad'e da man datake amfani dashi wurin gyara gashinta,, wata irin kunya ce ta rufeta ganin yaga kanta ajik'e wanda tasan tabbas yasan miye musabbabin jik'ewar kan nata,, amon muryarshi ce taratsa dodon kunnenta shine yak'ara sata jin wata matsananciyar kunya "My Sanyina wankan mekikai haka da yajik'e maki gashinkanki haka?" yana maik'ara shafo ruwan dake kanta,, shuru tayi tarasa bakin magana,, towel d'in jikinta yake neman kwancewa,, k'ok'arin hanashi take ta hanya tamke towel d'in sosai,, fisga d'aya yayima towel d'in saigashi k'asa take surar jikinta tabayyana,, saurin duk'ewa k'asa tayi tare da kare jikinta da hannuwanta,, mik'ar da'ita yayi yamaida hannuwanta baya yatsaya daga bayanta yataresu,, hannunshi yasa duka biyun yana wasa da nonuwanta cikin wani irin salo, dan har jan kan nipple d'inta yake yana murzasu sannan kuma yasa hannu ya damk'esu kamar wanda yarik'e kwai yana lailayarsu,,, k'afafuwansu ne suke neman kayar dasu yasashi kamota a hankali suka zube bisa gado,, bargo yaja ya rufesu ya cigaba da bata hot romance wanda tamanta duniyar datake ciki..... Asuba tagari Azraa^Aabid,,


***


"Meenah yau nakeso plan d'ina yafara aiki kan waccan kucakar mata Aabid dan nasa anbincikoman komai kanta da iyayenta da kuma alak'arta da 'yan gidansu Aabid inda nasamu labarin kwata-kwata mahaifin Aabid baya ra'ayinta da kuma burinshi nayima Aabid auren jari, to da wad'annan damarmakin zanyi amfani dasu wajen tarwatse gidan Aabid,, ga kuma numbert dana samu wurin wannan Kawun nata shima mai d'an banza san kud'in tsiya"




"duk yaushe kika samu wad'annan sirrikan wanda banda samaniyar lokacin dakika gudanar dasu" tsoki Najancy tayi tace "ina ko zaki sani kinacan kina rabama guys albarkatun gonarki, wanda baki wannan hotels baki wanca" gummm tayi dan tasan duk shaid'anci na Najancy bakowa take mallakama kanta ba,, wayarta dake chargin Najancy tad'auko, layin da aka turomata na Azraa shitayi dialing,, saida tabata kusan 3 miscall bata d'auka ba,, kwafa tayi tak'ara kiran layin Azraa,, dan ganin maikiran na neman damunta da hayaniya kuma gashi baida niyyar denawa yasa tad'aga kiran don lokacin fitowarsu daga break kenan,, cikin sanyaryar murya irin ta miskilan mata tayima Najancy sallama,, bak'aramin rikitata murya Azraa tayi ba don saboda dad'in amo dataji nata,, daurewa tayi ta amsa sallamartata cikin murya ta gogaggun bariki



"dafatan ina magana da Mrs Aabid Abdallah?" k'in amsawa Azraa tayi saima tambayarta datayi "menene damuwarki kansanin ko itace".... "inasan tabbatarwa dan jiya da yazo guna yake ban numberki koda na buga mashi bansameshi ba to nakira wannan layin naki dafatan kin fahimta" Azraa jitayi kamar and'aura mata aradu aka jin yadda Aabid yabada numberta ga 'yanmatanshi,, jin shurun nata ne yasa Najancy tace "yana kusa kibashi dan munyi dashi zamu fita amma nakira layinshi baya zuwa, in kuna tare bashi inason magana dashi",, dak'yar tattaro miyan bakinta da yagama bushewa tace "baya kusa amma in yazo za'a gayamashi" daga haka tai saurin yanke kiran bata saurari abinda zatak'ara cemata ba,,, wani irin tuk'uk'i ne takeji cikin ranta da kuma rainin wayo irin na Aabid watau ita yad'auka sakarai da har zairink'a rabama 'yan matashi numberta, kantane taji yana saramata kamar zaifad'o k'asa dan cika datayi da takaicin abinda Aabid yayi mata,, su Maryama duk na lura da yanayin data shiga tun lokacin datake amsa wayar, ganin batace masu komai ba yasa suma sukaja bakin salatinsu sukayi shuru dan sunsa halinta suna iya tambayarta tace masu sun dameta da hayaniya,, a daddafe tagama darasin ranan bawai dan ta fahimci abinda aka koya masu ba,, koda tazo wurin dasukai parking kasa cemashi komai tayi saima motar dataga ya bud'e mata tabud'e tashiga,, take kayan cikinshi suka yamutsa dan yau yayi niyyar koda k'arfin tuwo ne yayi sunna da'ita susamu su kashe arnan unguwarsu koda goma ne dan d'an yarbawa yabashi wani tsumin wai yayi testing yagani gashi ga dukkan alamu yau Azraa bata cikin yanayinta,, gwiwa sab'ule yabud'e motar yashiga,, motar yayima key yaja sukabar cikin makarantar,, wasu-wasi yashigayi cikin ranshi nason gano miya b'ata mata rai amma yakasa gano hakan gashi duk fuskatar na cikin nik'ab yasan akwai damuwa a tattare da'ita dan tunda tashigo cikin motar batace mashi komai ba,, tafiyar kurame sukayi dan kowa da abinda ke cikin ranshi,, shigowar sak'o ne yasata ciro wayar daga cikin bag d'inta,, ganin sak'on yafito daga number datayi saving da X yasata fad'uwar gaba,, nik'ab d'inta tazare danta k'ara tabbatar da abinda tagani,, tabbas ba gizo idanta kemata ba abinda tagani da farko shine yanzuma bai canjaba,, yana kula da duk abinda take ganin zufa naketo mata yasashi amsar wayar daga gareta,, baita aune ba sai ganin wayarta tayi a hannunshi,, zaro ido waje yayi yana k'ara bin sak'on da kallo inda take yagano inda sak'on ya dosa,, parking yayi gefen titi dan gudun haddasa afkuwar had'ari,, wayarshi ya zaro ya d'auki number da aka turoma Azraa txt da'ita,, Harafin N daya gani a wayarshi yasashi saurin katse kiran duban sashen da Azraa take yayi,, kallon tuhuma ta bishi dashi da san sanin k'arin bayani danmi zai d'auki numberta yaba budurwarshi "My Sanyinah, wallahi bansan komai akan haka ba, hasalima bansa ya akai tasamu number wayarki ba",,, cikin wata irin murya dabatasan tana da'ita ba tayi mashi magana "to inba kai kabata wayabata!!!?, har cemata kayi inbata sameka ba takirani".... "wallahi azeemu bani nataba,, dan Allah Azraa kiyarda dani" shuru tayi ta kyaleshi ya cibaga da rantse-rantsenshi ta shareshi,, bud'e murfin motar tayi takama zatafita "ina zaki?" yayi maganar cikin murya takalar tausai,, batace mashi komai ba saima k'ok'arin fita datake,, hannunta yajawo ta koma cikin motar,, rufe k'ofar motar yayi yatada suka tafi..........



Koda suka isa share juna sukai kowa ya cigaba da hidimar gabanshi dan yafara k'uluwa da irin abubuwan datake mashi, kuma yasanshi har ga Allah bashi yaba Najancy numberta ba dan bayadda za'ai yacima iyalinshi mutunci wurin Irinsu Najancy wanda basusan mutuncin kansu ba balle nawani,, ganin yafita batunta yasata k'ara k'ulewa tare da tabbatar da gaskiyar zance Najancy,, "roststert fish with irish nakeso kiyi mana" daga haka ya cigaba da buga game d'inshi ta criminal case tamkar bashi yayi maganar ba,, da kamar bazatai ba amma kawai ta d'aure tashiga k'ok'arin had'awa dan suna da komai dake buk'ata,, sai bayan data kammala komai ta ajemashi wurin da sukecin abinci, kewaye tashiga dan watsa ruwa dan magrib ta gabato,, bayan tafito ne shikuma ya wuce toilet d'in dan gabatar da tashi alwalla,, kiciniyar mak'ala karfin breazia take daya cire amma takasa dan tasa bra d'in mak'alma d'aya ta cire shine takeso ta mayardashi batare da ta curo bra d'in daga jikinta ba,, fitowarshi toilet d'in kenan yaga tana kokowarsa braezia,, hannunta ya janye daga saman bra d'in, k'arfen yake k'ok'arin maida mata amma shima yakasa,, juyo da fuskarta yayi suna fuskanatar junansu tare da jin huccin junansu ga nonuwanta dake gogar fad'aden k'irjinshi,, sunfi tsawon mintina ukku a haka kafin yace "kibarmanisu a haka tunda dagani saike cikin gidan, su kansu saisunfi sakewa inbaki samasu wannan abunba" tare da ida zare bra d'in gaba d'aya,, yad'auko mata wata bodyhug mai hannun shimi da tsayinta dakad'an ya wuce hips d'inta,, komawa toilet yayi dan k'ara d'auro wata alwallar dan waccan ta kare ya wuce masallaci,, itama alwalla ta canja ta d'aura zani kan riga ta gabatar datata sallar......








*MRS MK*
posted from Bloggeroid

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)