Wani mutum dan shekara 57 mai suna Magaji Dansale a jiya juma'a yayi ikrarin yadda da zargin da ake yi masa na yiwa jaririya diyar matar sa yar wata 7 fyade

- Magaji Dansale yace sharrin shaidan ne ya ja ya aikata hakan yayin da yake bada ba'asi a caji ofis tare da wasu sauran bata gari dake a kulle


yayin da yake yin ikrarin, Magaji Dansale ya kuma roki hukuma da da sassauta mashi hukuncin da za'ayi masa.

Yayin da yake bada ba'asi, mai laifin yace gani yayi acikin mafarki cewa idan har yayiwa yarinyar fyade to tabbas zai bar yawace yawacen da yake yi.


A cewar sa: "Bayan na auri mamar jaririyar sai kawai na rika yin wasu tafiye-tafiye bana zama gida. Kwatsam sai nayi mafarkin cewa idan nayi wa jaririyar fyade to zan bari."

Amma ba da wata mummunar manufa nayi hakan ba. Allah ne ya kaddara zanyi. Ya ci gaba da cewa.


@HausaNaij

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)