Hakan ne ma ya sanya muka dukufa wajen zakulo maku kadan daga cikin alfanun na sa a rayuwar bil'adama.
Fatan mu shi ne daga yau za mu waiwaye shi domin yin anfani da shi a rayuwar mu ta yau da kullum.
1. Maganin wari: Masana sun tabbatar da cewa bakin gawayi yakan zuke dukkan wani irin nau'in wari a duk inda yake.
2. Gawayi na hana lalacewar abinci: Bincike ya tabbatar da cewa dukkan abincin da aka sawa ruwan gawani to ba zai taba lalacewa ba.
3. Wankin hakora: Tamkar mangoge baki na zamani ko ma fiye da hakan, bincike ya tabbatar da cewa gawayi yana wanke hakora fes-fes.
4. Kwaranye guba: Idan kana kokwanton abinci yana tare da irin maganin nan na kwari ko guba dake da lahani a jikin dan adam, gawayi yana wanke ta.
5. Saurin warkar da ciwo: Haka zalika bincike ma ya tabbatar da cewa gawayi yakan taimaka wajen saurin warkewar ciwo.