Yan Nigeria na cigaba da fadar ra'ayoyinsu akan wannan bawan Allah Masoyin Buhari


'Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da wani hoto wanda yake nuna wani magoyin bayan Shugaban Kasar Muhammadu Buhari, inda yake rike da hoton shugaban yana annashuwa lokacin da shugaban ya kai ziyara jihar Bauchi.


A ranar Alhamis ne shugaban ya kai ziyarar jajantawa al'ummar jihar bayan wata mummunar guguwa da gobara a kasuwar garin Azare.
An yi ta yada hoton wannan bawan Allah a shafukan sada zumunta.

BBC ta samu dimbin ra'ayoyin jama'a a shafukansu na sada zumunta bayan wallafa hoton da bbc tayi a shafinta Facebook .

Wasu 'yan kasar sun bayyana ziyarar da cewa siyasa ce kawai, ganin cewa zabe ya karato kuma shugaban na neman wa'adi na biyu.
Yayin da magoya bayan shugaban suke kare shi, suna masu yaba masa da kuma yi masa addu'ar samun nasara da karin lafiya.

Mariya M Aliyu cewa ta yi:

"Hakika jihar Bauchi ta cancanci Baba yaje mata,koda kuwa wasane yakaishi, ba jajeba,duba da yadda duk Najeriya, ba jihar da ta kunshi 'yan gani kasheninBaba irin Bauchi."

Shi kuma Usman Abdu raddi ya yi wa magoyin bayan Buharin:
" Wannan ya hadu da wahala. Ya tafi kawai yaso annabi (SAW). Gashi yunwa tayi masa illa."

Saminu T Usman cewa ya yi: "Dan wahala ne. Maimakon ya riko hoton aikin da yake so a yi masa a jiharsa, amma ya bige da wannan."
Haka zalika Gazali Muhammad Adc Shuni ya ce:
"Son masoyin wani koshin wahala. Talakawa na soun Shugaba Buhari yayin da shi kuma baya sun su."

Amma Ali Aliyu Umar shi nuna farin cikinsa ya yi dangane da batun:
" Yayi kyau Baba masoyin Baba. Allah Ya karemana kai. Baba Buhari ikon Allah 2019 da 23. Insha
Allah."

Baya ga wannan hoto akwai kuma hoton wasu mata da ke kuka don murnar ganin Shugaba Buharin.

Shi ma dai wannan hoto ya jawo mutane sun yi ta tofa albarkacin bakinsu a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)