Babban Goro - Shuraih Usman


BABBAN GORO
-----------------------
Littafina daya
.
Part 1A
.
With shuraih 99%
Typing by :- Shuraih Usman
.
Zaku sha karatu har ku gaji
.in naga bakwa respond toh zan ajiye littafina
agefe
.
.
Awani zamani can baya anyi wani attajirin sarki
wai shi abul dinar ,wanda matsafa da masu
harsashe suka tabbatarda cewa babu attajiri
kamarsa a duniya ,saboda tarin dukiyar da Allah
yabashi wannan sarki yana da matan aure guda
goma sha shida kuma yana da kuyangai tamanin
gabaday wayannan mata nasa babu wadda ta
raba haihuwa sai guda daya ,
Wata mace da ake kira hauziya
Duk acikin matan abul dinar hauziyace yar
talakawa ,domin duk sauran daga yayan
sarakuna sai yayan mayan attajirai na duniya
.
A ranar da aka fuskanci hauziya ta sami ciki ,sai
sauran kishiyoyinta suka cika da bakin ciki .
Batare da da bata lokaci ba suka shiga bin
hanyoyin da zasu tabbatar da cewa cikin ya zube
,masu tsafi nayi ,masu surkulle nayi, kai wasu ma
kiri kiri a fili sukka ringa yin abubuwan da zasu
sa cikin ya zube amma ubangijin musulunci shine
mai yin yadda yaso ,sai ya kare hauziya daga
sharrin kishiyoyinta .
Shikuwa sarki abul dinar koda yaji cewar hauziya
ta sami ciki , sai yadauki son duniya ya kwallafa
a akanta . Domin zata share masa hawaye a bisa
bakin cikin daya addabi rayuwarsa ta duniya
,wato rashin magaji ,
Dayake ya tabbatar da cewa sauran kishiyoyinta
bazasu kyaleta ba, sai ya dauketa ya kaita wani
gidansa dake bayan gari .
Ya ajiyeta ita kadai ,
Daga ita sai bayi masu yi mata hidima .
Gidan ya zama ba'ashiga da fita ,in ba shi kansa
ba .sarki abul dinar ya tare wajen hauziya , tare
suke ta rainon cikin har wata takwas .
A ranar da cikin ya cika wata takwas da kwana
shirin da biyar .
Ciwon nakuda ya kama hauziya .
Cikin yan dakiku kadan ta haifi sankaceciyar 'ya,
Wadda atun tana jinjiniyar aka tsorata daganin
kyawunta.
.
Sannu sannu akayi ta rainon yarinyar wadda aka
sawa suna Mabaruka ,har ta girma .
Ta zama cikakkiyar budurwa ,
Wadda saboda tsananin kyau labarinta ya cika
duniya . Jarumai da matsafa da dama sun hallaka
junansu a kan soyayyarta
.
.
Wata rana gimbiya Mubaruka ta fita rangadi , don
shakatawa cikin wata babbar gona ta mahaifinta
,kuyangi da barade na take mata baya.
.
Kwatsam sai ga wata katuwar macijiya mai
girman gaske , ta bayyana a gabansu .
.
Koda ganinta sai barade da kuyangi suka kwalla
ihu, suka ruga baya da gudu ,
.
Baraden nan suka yi ta rige rigen gudu ,sun
mance da aikinsu na tsare lafiyar 'yar sarki .
Ita kuwa mabaruka sai ta tsaya kyam ta kasa
gudu , don tsananin razana , hawayen bankwana
da duniya suka tsiyayo daga idanuwanta .
.
Katuwar macijiyar ta wangame baki zata hadiyeta
, kawai sai mabaruka taga wani bakin bawa yai
tsalle ya rungumi wuyan macijiyar
.
Nan fa suka kama kokawa shi da macijiyar su
fadi can su tashi can.(Ni kaina shuraih sai dana
kusan....basai na karisa ba)
.
Shi yana kokarin ya turmusheta ya rarumi wani
icce dake waje guda ya soketa ita kuma tana
kokarin kannannadeshi ta karairaya kasusuwan
jikinsa . Haka dai suka yi ta dauki ba dadi har
tsawon rabin sa'a , macijiyar nan tai masa fata-
fata , duk jikinsa ya rune da jinin raunuka
Amma hakan bata sa ya saketa ba ,
A hakan dai Allah ya bashi iko , hannunsa ya kai
kan wannan icen cikin zafin nama ya dauki icen
ya caka abakin macijiyar , ya bullo ta tsakiyar
kanta .
.
Nan take macijiyar ta sulale ta fadi kasa
matacciya,
Shi kuma bawan yafadi kasa a sume .
.
Koda ganin haka sai gimbiya mabaruka ta ruga
gareshi ta rungumeshi tana kuka ,
Gaba daya jikinta ya baci da jininsa .
Ahaka sarki abul dinar da dakarunsa suka zo
suka sameta .
.
Nan da nan aka ban bareta daga jikin bakin
bawan , aka tafi da ita shi kuma aka yayyafa
masa ruwa ya farfado daya ke shi bawa ne marar
gata ,
Sai aka tuhumeshi da laifin rungumar 'yar sarki ,
Ba'ama duba sai da ran dayayi ba, dan ceton
'yar sarkin.
.
Saboda haka aka kaishi dakin tuhuma ,aka
dauddaureshi da sarkoki aka yita gana masa
azaba iri iri.
.
A iya tunanin Mabaruka wannan bawa ya mutu
wannan dalili shi yasa tai ta kuka har hankalinta
ya gushe ta suma bayan ta farfado ta mike
zaune daga kan gadon data ke kwance ,
Inda tai arba da mahaifiyarta hauziya zaune a
gefen gadon idanunta cike da hwaye .
Koda ganin mikewar mabaruka sai farin ciki ya
kama hauziya.
.
"Mama ina gawar bawan daya ceci rayuwata?"
Mabaruka ta tambaya fuskarta cike da alamun
bege
.
"Waya ce miki ya mutu? Ai dogon suma yayi
kum, kuma anzuba masa ruwa ya farfado ,yanzu
haka yana can daure a dakin tuhuma"
.
"Me yayi za'a kaishi dakin tuhuma?"
.
Batare da mabaruka ta saurari karin bayani ba ta
mike tayi waje da gudu ,
Mahaifiyarta tana kira amma taki dawowa , bata
tsaya ako ina ba sai a kofar dakin tuhuma,
Da zuwa ta dakawa masu gadin tsawa tace "su
bude mata kofa kofar "
.
Jikinsu na rawa suka bude kofar ta shiga , inda
ta iske shi kwance magashiyyan cikin jini .
Nan take tasa aka kwance sarkar dake jikinsa ,
tasa aka kaisa gidanta inda taimasa wanka ta
sama magani a raunukan jikinsa sannan tasa aka
kawo masa abincin sarauta , ya cika tumbinsa !
Daga nan aka kaishi wani dakin hutu ya kwanta
yai barci, har sai da rana ta fadi sannan ta shiga
dakin ta tashe shi , duk su biyun suka kurawa
juna ido
.
"Yakai wannan jarumi menene sunanka"
.
Bawa yayi murmushi yace "ni sunana Ashwar "
.
"Ya akai kana matsayin bawa a gidanmu na
sarauta amma ban taba ganin kaba ?"
.
Ashwar yasake yin murmushi yace "yake gimbiya
kisani babu yadda za'a yi ki taba ganina , domin
tun da aka haifeni ban taba fitowa ba daga cikin
lambun sarki na can bayan gari sai ayau .
Mahaifina shine bawan dake kula da wancan
lambu na sarki , tun yana saurayi yake wannan
bauta harya tsufa ya mutu , nikuma na gajeshi
Mahaifiyata ma acikin wannan lambu ta rasu
yanzu haka kabarinta na cikin lambun
A yaune sarki ya aika mini naje daya lambun
nasa nayi aiki wanda shine kika ziyarta don
rangadi
To ina cikin aikine na hango shigowarku keda
kuyangi da barade .
Kuma sai naga wannan katuwar micijiya ta
tarwatsa kuyanginki da baraden
Duk sun gudu sun barki shi yasa na sai da raina
don ceto rayuwarki".(Ni 99% nace lallai kacika
sadauki)
.
.
Koda jin haka mabaruka tai ajiyar zuciya
hawayen tausayi kauna suka zubo mata tace "ya
kai Ashwar kasani daga yau bawani namiji da zan
aura in ba kaiba
.
Cikin razana Ashwar yaja da baya ya takure
jikinsa ga bango yace" ranki ya dade ki rufa min
asiri , ki tuna fa ni bawane , bawan ma bakin fata
,ke kuwa gaki balarabiya 'yar sarki,ina ni ina
aurenki"
.$
Mabaruka tayi murmushi tace "ai babu ruwan so
da matsayin jinsi ko launi ,idan duk duniya zata
taru banga wanda ya isa ya raba ni dakai ba ,
abu daya nake so na ji daga bakinka kawai , kana
sona ko baka sona?"
.
"Haba gimbiya ai babu wani namiji da zai ganki
yace baya so , amma ai wutsiyar rakumi tai nesa
da kasa kuma BABBAN GORO SAI MAGOGIN
KARFE"
.
"Kwarai kuwa"wata murya ta amsa daga bayan
su.
.
Mabaruka da ashwar suka dubi bakin kofa a
tsorace , sukayi arba da sarki Abul dinar fuskarsa
a murtuke wasu kartin barade shida na tsatsaye a
bayansa suna muzurai tamakar saci babu.
.
Cikin fushi ya dubi mabaruka yace "haba gimbiya
shin kin mance da martabar gidannanne ?kin
manta da matsayinki na 'yar sarki ne?har zaki
wulakanta kanki ki dauko bakin bawa ki shigo
dashi har cikin gidanki mai Albarka.
.
Maimakon mabaruka ta nutsu kota firgita da
wannan tambaya sai ta kyalkyale da dariya
sannan tace "haba Abba ka runa fa mahaifiyata
ta fito daga dangin talakawa ,me yasa ka aurota
har kuka haifeni? Shin baka tsammanin zubar
martabar sarautarka ne? Hakika sone yasa
idanunka suka rufe , tunaninka ya gushe ka
manta da matsayinta......"
.
Cikin hanzari abul dinar ya tari numfashin
mabaruka yace" yata kada ki yi la'akari da
wannan , domin inki kai tunani akwai alaka ta
jinsi da jini tsakanina da mahaifiyarki amma
tsakaninki da wannan bakin bawan babu alakar
komai"
.
"Abba ni dai Ashwar nakeso"
(Shuraih 99% ke magana)
.
Wannan bayani ba karamin girgiza Abul dinar yayi
ba , don tsabar takaici sai da yaji kwalla ta zo
masa amma sai ya juya baya yayi shiru yana
tunani , daga can ya juyo ya dubi mabaruka yace"
na amince da niyyarki amma bisa sharadi "
.
Cikin mamaki mabaruka tace "wane irin sharadi
ne?"
.
"Zakiji sharadin gobe da a fada gaban dukkanin
jama'a.
.
Nan take sarki ya juya ya fice daga dakin ,barade
suka take masa baya.
.
Ashwar da mabaruka suka dubi juna cikin
tsananin damuwa
.
"Ai daman na san wannan al'amari bazai taba
yiwuba , nagaya miki cewa BABBAN GORO SAI
MAGOGIN KARFE"
.
Mabaruka tayi murmushi tace "ashwar ina so ka
kalli cikin kwayar idanuna kaga ya mini abinda ka
gani aciki "
.
Ashwar ya kura mata ido har tsawon 'yan dakiku
kadan sannan ya kawar da kai
"Me kagani acikin idanuna?"
"Banga komai ba face digon baki da zagayen fari"
.
"To wannan zagayen farin daka gani ba komai
bane face fadar zuciyata , wannan digon bakin
kuwa daka gani guda daya tilo ba komai bane
face kai Ashwar Kai kadai nake so bazan so wani
ba yan kai ,idan kuwa aka aura mini wani ba kai
ba saidai ya zauna da gawata"
.
Haka dai Ashwar da mabaruka sukaci gaba
mahawara yana ta kokarin nuna mata matsala
har zuwa gabannin magariba ,sannan ya tafi
gidan gona ita kuma taci gaba da tunanin hanyar
dazata bi ta shawo kan al'amarin .
Wannan shine abin daya faru tsakanin jarumi
ashwar da gimbiya mabaruka .
.
Shuraih ke magana
.
Al'amarin sarki abul dinar kuwa lokacin daya bar
gidan 'yarsa mabaruka sai hankalinsa ya dada
dugunzuma ya rasa abinda yake masa dadi
aduniya , har ya isa turakarsa yana cikin wannan
hali , ya kasa zauni ko tsaye sai da dukkanin
barorinsa da fadawansa suka fahinci lallai akwai
abin da yake damunsa .
Bayan yayi dogon tunani sai ya tura aka kirawo
masa yan majalisarsa cikin turakarsa daga cikin
yan majalisarsa sarki Abul dinar akwai waziri,
galadima ,wambai da Gulmanu sarkin matsafa na
garin.
.
Bayan dukkaninsu sun zauna , sai sarki Abul
dinar ya basu labarin abinda ke faruwa tsakanin
'yarsa mabaruka da kuma jarumi Ashwar, sannan
yace
"Kunsani cewa abin kunya ne ace 'yarmu ta auri
bakin bawa ,tabbas idan akai martabar
masarautarmu ta zube , sauran kasashe ma dake
makwataka damu sai sunzage mu sun raina mu
ku sani idan muka sanar da mabaruja kuru-kuru
cewa ba zamu amince ta auri ashwar ba , tabbas
zata iya hallaka kanta, nidai nace da ita zan bata
shi amma bisa sharadi ,sharadin kuma nace sai
gobe da safe zan tara jama'ar gari na fadi a
gabansu .
.
Toh ku sani sharadin nan fa ni kaina ban san shi
ba , wannan shine dalilin dayasa na tara ku anan,
inaso muyi tunani mai zurfi mu kafawa ashwar
sharadin nemo wani abu mai tsananin wuyar
samu a duniyar nan, wanda a sakamakon neman
sa ma zai hallaka in yaso kun ga dole mabaruka
ta rungumi kaddara"
.
Yayin da 'yan majalisa suka ji wannan bayani na
sarki abul dinar sai duk suakayi shiru suka shiga
tunani aka rasa wanda zaice kala , har ya zuwa
wani lokaci daga can sai gulmanu sarkin matsafa
ya mike yace
.
"Ya sarkin sarajkai hakika ni ina da mafita akan
wannan al'amari kuma na rantse da wata
sharadin da zan dora Ashwar akai bai is ya haye
shi ba ina so ku yi hakurin jin wannan sharadi
har zuwa gobe da safe "
.
Koda abul dinar yaji wannan batu sai fuskarsa ta
fadada da murmushi yace na yarda dakai sarkin
matsafan duniya gulmanu , shikenan na
sallameku, kowa ya tafi gida sai gobe da safe mu
hadu a kofar fada
.
Nan take 'yan majalisa suka watse batare da
wani daga cikinsu yace kala ba aka bar sarki
acikin dumbin farinciki
.
Birnin sarwaliya babbar garine mai tsohon tarihi
,wanda a halinm yanzu sarki abul dinar yake
sarauta a cikinsa gaba daya al'ummar farin
ma'abota Addinin bautar wata ne , duk sa'adda
wata ya cikja kwana goma sha biyu gaba
dayansu maza da mata yara da manya sukan fito
tsakar dare , suyi sujjada ga watan suna masu
fadin bukatunsu da rokon gafarar kurakuransu,
wannan abu ne wanda ya yi matukar tasiri
zukatunsu
.
Bayan sarki yagama shawara da yan majalisarsa
sai yasa akayita shela da yekuwa aka sanar da
jama'ar gari cewar gobe da safe ana gaiyatar
kowa a fada ba ayafewa ko da yara ba . Masu
shela basu daina sanarwa ba har sai da dare yayi
, sannan suka je suka kwanta.
.
Shuraih 99% ke magana
.
Kashe gari jama'a sukayi ta tururuwa suna zuwa
fada kungiya kungiya ,ayari ayari ,har daga
kauyuka,kai wasu ma saga makotan kasashe sai
da suka zo don son ganin kwakwaf,saboda labari
ya bazu cewa akan maganar 'yar sarki ne da
bakin bawan data nace tanaso.
A cikin wadanda suka halicci wannan taron akwai
wasu jarumai kimanin su shida masoya mabaruka
, wadanda suma ashirye suke dasu salwantar da
rayuwars son ganin sun sami aurenta.
.
Bayan sarki abul dinar da'yan majalisarsa sun
hallara , sai aka tura wani bafade yaje yakira
ashwar daga gidan gona . A sannan ne gimbiya
mabaruka ta iso tare da kuyanginta da baradenta
, nan take taje ta zauna bisa kujerar dake daf da
karagar sarki ,
Sarki ya dubeta yai murmushi .
Hakan keda wuya kuma sai ga ashwar tare da da
bafajen da aka aika ya kirawo shi sun iso, da
zuwa aswar ya fito tsakiyar filin fada , ya fadi
yayi gaisuwa ga sarki , bayan an amsa gaisuwar
ne aka yi masa izinin mikewa tsaye , yana
mikewa ne yayi ido biyu da abar begensa tana
mai yi masa wani irni murmushi mai tona asirin
zuciya .
Cikin karfin hali ashwar ya yiwa mabaruka
murmushi , sannan ya kau da kai ga barin
kallonta don tsoron kada tsananin kyawunta ya
rinjayi zuciyarsa ya kamu da sonta .
Tun daga ranar da ashwar ya fahimci cewa
gimbiya mabaruka na sonsa , tsoro da damuwa
suka cika zuciyarsa .
Badon komai ba sai don ya tabbatar mahaifinta
ba zai maraba dashi ba , wannan dalili yasa ya
danne sha'awar bege da so a zuciyarshi ,har a
halin yanzu ashwar bai yadda son mabaruka ya
shige shi ba , kai in ba don ma bin umarnin sarki
ba da tabbas ba zaizo wannan kira da akayi
masa ba.
.
.
A cikin wannan gona ta sarki wadda ashwar ki
aiki , akwai wani dattijo abokin aikinsa wanda ake
kira makabul. Makabul tsohone sosai , domin
shekarunsa sun kai kimanin tamanin da doriya .
Makabul aminin baban ashwar ne , don asali ma
tare aka siyo su a matsayin bayi daga nahiyar
kasar bakaken fata,
Tun suna samari yan shekara sha tara.
Tun ashwar na yaro karami ya taso yake ganin
abotar da ke tsakanin mahaifinsa da makabul,
don haka bayan rasuwar mahaifinsa sai ya rike
makabul tamkar mahaifinsa komai zaiyi sai ya
shawarce shi . Yanzu hakama makabul dinne
yabashi shawarar yazo fada don amsa kiran sarki
kuma yace dashi kome aka bukaci da yayi akan
mabaruka kada yaji tsoron komai ya amsa cewar
zaiyi, komai wahalar al'amarin. Koda ashwar ya
tambayi makabul dalilin da yasa yace ya sai da
ransa.
.
Sai yace dashi" tun mahaifinka nada rai mun taba
zuwa wajen wani boka wanda yayi bincike akan
ka , bokan ya sanar damu cewa zaka shahara a
duniya , kuma zaka auri 'yar sarki, amma sai ka
karbi Addinin musulunci
.
Koda jin wannan batu sai ashwar yayi shiru yana
tunani daga can yace" kai baba makabul yanzu a
ina zan sami ma'abocin wannnan addinin daka
fadi? Kasani cewa babu masanan sa anan garin
dakuma kasa shen kewayenmu"
.
Makabul yayi murmushi yace "kada ka damu
akwai tafiya da zakayi tabbas zaka hadu da
ma'abota Addinin musulunci,da zarar kun hadu ka
karbi Addinin, in da rabon mu ma zaka dawo gida
ka sanar damu wannan Addini mu karbe shi, don
tabbas shine Addinin gaskiya , amma kiri kiri
sarakunanmu sun ki shi don kwadayin duniya , da
son mulkinsu na kama karya "
.
,
Duk wannan hira ta wakana ne adaren jiya
tsakanin ashwar da makabul.
.
Yayin da ashwar ya karbi umarnin mikewa tsaye
gaban sarki a tsakiyar fada, sai sarki Abul dinar
da sarkin matsafa gulmanu suka dubi juna , nan
take gulmanu ya mike tsaye , yayi gaisuwa ga
jama'ar gari sannan yace
.
"Yaku al'ummar sarwaliya kun sani cewa
sarkinmu ya dade da rashin samun haihuwa sai
bayan shekara da shekaru ya sami mabaruka,
Yau gashi Allah ya yarata takai mun zalin aure,
ku sani cewa 'ya'yan sarakuna jarumai, da
mtsafa sunzo da yawa ba adadi sun nemi aurenta
, amma basu samu ba saboda tace bata sonsu .
To yau an wayi gari gimbiya mabaruka ta budi
baki ta fadi wanda takeso ,kuma bawani bane
face bakin bawannan dake tsaye agabanku wato
ashwar"
.
Nan fada ta rude da hayaniya sai da aka yi tsawa
sannan kowa ya yi shiru.
.
Boka gulmanu yaci gaba da cewa " to mu muna
da ka'idoji a wannan masaruta ta mu muna kafin
mu aurar da yar mu duk wanda zai auri 'yar
sarauta dolene ya kasance daya cikin uku, abu na
farko shine sai ya kasance. Mashahurin mai arziki
, abu na biyu dole ne ya kasance dan sarauta ,
abu na uku dolene ya zama jarumin da yayi
mashahuriyar jarumtaka a duniya . Kun sani cewa
wannan saurayi ashwar dake tsaye a gabanku bai
kasance cikin daya daga cikin wadannan ka'idoji
dana lissafa ba saboda haka yanzu dama daya
gareshi dole ne yaci jarabawar da zamu yi masa
akan jarumta , indai yaci wannan jarabawar to
zamu amince mu aura masa gimbiya mabaruka"
.
.
Ehem shuraih 99% ke magana muje zuwa
.
Koda jama'a sukaji wannan batu sai akayi shiru
kai kace mutuwa ce ta gifta ,
Kowa ya kasa kunne don yaji wace irin jarabawa
ce za'ayi wa jarimi ashwar.
.
Boka gulmanu yayi shiru zuwa 'yan dakiku kadan
sannan ya nisa yace"Abin da muke so ashwar
yayi don mu tabbatar da jarumtakarsa shine ,
munasa kaje birnin Duma ka shiga fadar sarkin
Aljanu kifyan, ka dauko mana Bishmalu dan
sarkin Misra wanda tun yana jariri sarki sarki
Kifyan ya sace shi, ahalin yanzu Bishmalu ya cika
shekara ashirin da biyar. A duniya .
Kasani indai kayi nasarar dauko Bishmalu , sarkin
Misra yayi alkawarin zai raba kasarsa biyu
yabaka Rabi , mu kuma take zamu aura maka
gimbiya mabaruka , kaga ka jefi tsuntsu biyu da
dutse guda kenan wato ga sarauta ga auren
'yarsarki
.
Boka gulmanu na gama wannan jawabi fada ta
sake rudewa da hayaniya, kowa na cewa wannan
aikora da haline , dan tabbas an san cewa babu
wani mahaluki daya isa yaje birnin Duma don gari
ne na Aljanu zalla , Aljanun ma bakake mazalunta
kuma kafirai, sarkinsu kifyan shine ubangijinsu
don shi suke bautawa.
.
Ragowar jaruman nan guda shida , wadanda suka
zo da niyyar sallama rayuwarsu son aurar
Gimbiya mabaruka sai duk suka zare jikkunansu
suka boye a cikin jama'a don sun tabbatar da
cewa ba zasu iya cin wannan jarabawa ba,
dominn labari ya bazu ko'ina a duniya cikin
wannan zamani cewar sakin Aljanu kifyan ya
zama gagara badau, ya Addabi dukkan aljanu da
bil'adama dake doron kasa.
.
Littafin :- king of Adventure stories(Abdulaziz
sani madakin gini)
.
.
WANE NE BISHMALU
.
YA AKAI SArKIN ALJANU KiFYAN YA SACESHI
.
SHIN AShWAR ZAI YADDA YA AMINCE DA
WANNAN JARABAWAR
.
IN MA YA AMINCE SHIN ZAI SaMU NASARAR
DAUKO BiSHMALU DAGA FADAN SARKI KIFYAN
.
BABBAR GORO
.
Littafina daya (1)
Part 1B
.
With shuraih 99%
Typing by :- http://facebook.com/shuraih.usman
.
Sarki abul dinar ya mike tsaye da kansa ya daka
tsawa , nan take akayi tsit.
.
Sarki ya dubi ashwar cikin murmushi yace" ya kai
ashwar kaji jarabawar dake gabanka shin zaka
iya ?"
.
Gaba daya idanun jama'a suka zubo kan ashwar.
Ashwar yayi shiru yana kallon jama'a har
idanunsa suka kai kan gimbiya, inda ta mike
zumbur tana mai kokarin tace ya amsa, amma sai
ya da kansa ya dubi tsho makabul, nan take
makabul yayi masa inkiya ya amsa.
.
"Ran sarki ya dade na amince da wannan
jarabawa , kuma nayi alkawarin zan zo da
bishmalu dan sarkin misra cikin wannan fada
taka"
.
Cikin tsananin farin ciki ta daka tsalle sama
sannan ta rugo da gudu ta rungume ashwar
agaban jama'a , nan take fada ta sake rudewa da
hayaniya ,
Sarki da 'yan majalisarsa suka mike suka shiga
cikin gidan sarauta ,
Ita kuma gimbiya sai ta tafi da ashwar izuwa
gidanta .
Surutai iri iri daga bakin jama'ar gari suka
yawaita. Wasu suce hakika ashwar mahaukacine,
wasu kuwa suce yarinta ce ta dibeshi yayi wauta,
wasu ma har zuwa sukai suna yiwa tsoho
makabul ta'aziya suna cewa"dan ka ya zama
gawa"
.
Shi kuma sai dai yayi murmushi kawai agaresu
su tafi suna gulmarsa.
.
Farin ciki wajen gimbiya mabaruka a wannan rana
yafi karfin misaltuwa .
Nan take tasa aka shiryawa ashwar walima ta
musamman , inda kuyanginta suka shiga hidimar
girke girke .
.
Cikin kankanin lokaci aka samar da abinci iri iri
da ababan sha kala kala .wannan walima an yi
tane awani daki ta musamman cikin gidan
gimbiya mabaruka ,
Kuma ba'a gaiyaci kowa ba face ashwar shi
kadai, sai kuma abar begensa wato gimbiya ,
ma'ana su biyu kadai.
Suka zauna karkashin wani dogon tebur mai
dauke da kujeru hamsin, akan wannan tebur aka
shirya dukkanin wannan abincin da ababan sha
bisa farantai , akan kowane faranti akwai
kuyanga tsaye rike da cokali , da zarar gimbiya ta
bukaci abincin sai kuyangar ta garzayo ta kawo,
ta zuba a cikin wani babban faranti dake gabansu
ita da ashwar anan fa mabaruka ta nuna tsantsar
soyayyarta ga ashwar domin da hannunta ta
dunga bashi abincin yana ci , ganin haka shima
sai ya dunga ciyar da ita da hannunsa, har suka
ci suka koshi.
.
Nan take mabaruka ta kama hannun ashwar ta
kaishi cikin falonta inda take saukar manyan baki
suka zauna. Dayake ashwar bai sa ba da ko'ina
ba in ba gidan gona ba ,sai ya zama dan kauye
yayi ta kalle kalle a cikin falon
.
Mabaruka ta bushe da dariya tace"haba
masoyina ya zaka dunga kalle-kalle kamar wanda
ya fito daga kauye.
.
Wannan batu yasa ashwar yayi murmushi yace
"ranki ya dade dolene ki ga kauyanci a tare dani
domin tunda aka haifeni a cikin gidan gona na ke
rayuwata , ban taba shigowa cikin gari ba sai
ranar dana hadu da ke , hatta sa'adda aka kaini
dakin tuhuma hankalina ya gushe ban taba shiga
wajen ba sai a ranar. Hakika kece sanadin
shigowata cikin Al,umma , tun tasowata ban san
komai ba face bauta da biyayya ga sarki abin
dana ga iyayena nayi , ban san sanya sutura mai
kyau ba irin wadda nake gani yanzu ajikin su,
bansan kwanciya ba akan shimfida sai ciyawa da
harawar doki.tabbas kin sauya komai na
rayuwata bazan taba mancewa dake ba "
.
Yayin da ashwar yazo nan a zancensa sai ya ga
idanun gimbiya mabaruka ya ciko da kwalla , nan
da nan hawaye ya fara zuba bisa kuma tunta .
Wannan yasa hankalin ashwar ya tashi, yadan
matsa kusa da ita ya durkusa bisa guiwowinsa
cikin kaskantar da kai yace
.$
"Ya shugabata ki yimin gafara idan na saba miki
a cikin maganganun dana fadamiki"
.
Bisa mamaki sai yaga fuskarta ta fadada da
murmushi , sannan ta rike kafafunsa suka mike
tsaye tare, ta dubeshi da kyau tace
.
"Ya masoyina na rantse da wata ko kadan baka
bata mini rai ba, kawai na tausayawa rayuwarka
ne . Hakika sai yanzu na tabbatar da cewa
mahaifina yana mulkin zalunci, domin an tauye
hakkinka dana iyyenka , A matsayinku na
bil'adama da ba dabbobiba, bai kamata ace baku
da sutura ba face walki, tabbas inda nasan cewa
akwai irinku a garinnan da tuni na kai muku "
.
Shuraih ke magana
.
Koda jin wannan batu sai ashwar yaji duk tsigar
jikinsa ta tashi, jikinsa yayi sanyi, ya kura mata
idanu kuma ya kasa cewa komai . Mabaruka na
ganin sauyin........
.
Kash kuyi hakuri makaranta fallen littafin ya
lalace akalla dai fallen daya lalace yakai goma
sha daya. Amma zanyi kokari na dan bayyana
muku abubuwan fallen ke kunshe da shi cikin
gaggawa
.
Shuraih kemagana
Boka gulmanu yazo ya samu sarki abul dinar ya
sanar dashi cewa" lallai wannan yaro kar ya wuce
kwana uku bai yi wannan tafiya ba kuma a sanar
dashi cikin wata uku kacal akeson ya dawo tare
da bishmalu"
.
Sarki abul dinar ya dubeshi cikin mamaki yace "
yakai sarkin matsafa shin meyesa kace haka "
.
"Aljanina ne ya sanar dani haka kuma ya
tabbatar min muddin bai bar garinnan cikin
kwana uku ba toh tabbas zaiyi nasarar shiga
birnin duma kuma ya dauko bishmalu"
.
Sarki abul dinar najin haka yai umarni ga wani
bardensa. Dayaje ya sanar da jarumi ashwar
cewa cikin ya tabbata cikin kwana uku ya fita
daga garinnan ya nufi birnin duma , sannan wata
uku gareshi muddin wata uku ta gota koda da
kwana dayace to ko yazo da bishmalu wannan
gari to tabbas ya fadi
.
Wannan shine abin daya afku a fadar sarki abul
dinar
.
Shidai mahaifin bishmalu wato sarkin Misra ya
auri wata kyakkywar mata , ita wannan matar
duk wanda ya aureta mutuwa yake sakamakon
sarkin aljanu kifyan dayake matukar sonta koda
sarkin misra ya aureta sai aka ringa tsorota da
shi ana mai kashedin ya rabu da ita ,
Wata rana ya fita farauta shida baradensa suna
cikin jeji sai sukaji wata murya ta barke da dariya
sannan akace da su "ya kai wannan sarki mai
taurin kai lallai ka rabu da wannan mata taka don
ita mata ta ce ni kadai"
.
Sarkin misra na jin wannan batu yace karyarka
tasha karya baka isa karabani da mata ta ba ......
.
Wata sarka yagani ta shake wuyansa nan take ya
ringa makyarkyata .
Can sai yafadi wata kalma sai wannan sarka ta
tsinke ,
,
Baraden suka juya tare da sarkin misra suka
dawo cikin gari
.
Toh fa tun daga wannan rana ne wani ciwon kai
mai tsanani ya addabi sarkin misra.
Wannan ciwo ta hana shi sakat domin idan ta
tashi mai tamkar zai mutu haka yake .
.
Koda matarsa taga wannan ciwo taki ci taki
karewa sai ta tafi wajen boka ta sanar dashi
wannan ciwon na sarki take bokan ya bata wata
laya yace ta dauara layan awuyan sarki.
.
Tazo ta daura layan , aiko tana daurawa sarki ya
ji shi garau tamkar wata ciwon kai bata taba
samun saba a duniya.
.
Ana nan ana nan rannan sai matar sarkin misra
ta samu ciki ,
Sarkin misra yai murna kwarai , bayan cikin ya
cika wata tara sai ta haife santalelen yaro wanda
tsabar kyaunsa ma ana zaton aljani ne
.
Sarkin misra yayi murna kwarai amma mai hade
da bakinciki sakamakon mutuwar matarsa yayin
haihuwa ,
.
Aka saka ma yaron suna bishmalu ,
Wata rana da daddare sarkin misra yai mafarki da
wani garjejen aljani yana rike da dansa yace mai"
tun da ka kashe mata ta toh na dauki danka
daga yau yazma dana baza ka sake yin arba da
shiba.
Har ka mutu
.
Washe gari sarkin misra ya farka baiga bishmalu
ba yai neman duniya amma bai ganshi ba daga
bisani yaje wajen boka toh ananne boka ya
tabbatar mai da cewa dansa yana nan a raye
wani hatsabibin sarkin aljanu ne ya sace shi ya
kaishi birnin duma sunan wannan aljani kifyan
.
Sarkin misra ya tura sadaukai , jarumai da dama
amma duka ba labarinsu
.
Daga karshe ya hakura ya sadakar
Amma sabi da bakin ciki kullum cikin kuka yake
yanzu haka yana fama da wata irin cuta , wannan
cuta anyi magani anyi magani amma ina taki
warkewa ,
Amma bokansa ya fadami duk randa yai arba da
dansa bishmalu toh zai warke daga wannan cuta
.
.
Wannan shine takaitaccen tarihin bishmalu daga
bakin shuraih 99%
.
.
Koda ashwar ya sami sanarwar sarki abul dinar
kan cewa ya gaggauta barin garin kafin kwana
uku
.
Sai yayi shiri
Tsoho makabul ya iso gareshio dauke da wasu
makamai , mashine da takobi sai kuma kibiya
.
Tsoho makabul ya mika mai yace " amshi
wayannan makamai kasani wannan bokan daya
fadamana cewa zakayi gagarumar shahara a
duniya shine ya bamu wayannan makamai yace
duk sa'adda ka girma in damka ta a hannunka.to
yanzu lokaci yayi "
.
Ashwar ya amsa yana mai godiya ga tsoho
makabul
Zuwa asuba ashwar yagama shirin shi sannan
yarubuta wasika ya bawa tsoho makabul kan
cewa in gimbiya mabaruka tazo ya bata sannan
ya sanar da ita shi yatafi .
.
.
Bayan fitarsa daga birnin sarwaliya ya yanki daji
yaci gaba da tafiya
Sudai wayannan makamai da tsoho makabul ya
bashi sihirtattun makamaine
1.acikin makaman akwai wata mashi wadda duk
abin da aka soka da ita to fa saide wani bashiba
ita wannan bashi har dutse fasashi take ta
tarwatsa shi sannan ta wuce
2sai wata kwari da baka wanda shi wannan
kwarin I zan har ka harbata toh zataje ta cake
duk wadda kake bukata ta cakeshi sannan ta
dawo cikin gwafanta itama wannan kwari tana
huda dutse sannan ta tarwatsa shi
.
(Har yanzu dai ni shuraih hakuri nake baku
sakamakon lallacewar sauran fejin kuma ni kaina
nasan bazan baku labarinnan yadda take ba
amma zan dan kokarta)
.
3sannan kuma akwai wata sihirtacciyar takobi
wadda take da kaifin tsiya koda bishiya aka sara
da wannan takobi toh anan take zai bushe
sannan ganyayyen bisansa su bushe yafadi kasa.
Shi wannan takobi idan dare yai sai kaga yayi
haske inda zai haskaka ma marikinshi hanya
.
.
Wata rana ashwar ya kwanta yana barci saiyayi
mafarki a cikin mafarkin nasane aka sanar da shi
cewa akwai wata gari agabansa izan ya shiga
garin kada yaci komai ko ruwa ne kada ya yadda
yasha
,
Koda ya farka daga barcin ne sai yaga mai ai
safiya tayi sannan rana ma ta fito .
Tafiya kadan yayi sai ya hangi wani gari
agabansa batare da shakkar komai ba ta dumfari
wannan garin yana shiga cikin wannan gari sai
yaga wani tsoho yana noma koda tsohon ya
gansa sai ya kariso gabashi suka gaisa bayan
sun gaisa ne tsohon ya dauko wasu dabino ya
mika ma aswar.
.
Har ya kai hannu zai karba sai kawai ya tuna da
mafarkin da yayi jiya da daddare .
Sai yafasa amasar wannan dabino.
Tsohonnan yayi yayi da ashwar ya ci dabinon
amma ashwar yaki sai wannan tsohon ya tashi
mai haikan yana so ya kasheshi koda ashwar
yaga haka sai ya zaro takobinsa ya fille kan
wannan tsohon sannan ya ci gaba da tafiyarsa
izuwa cikin garin
.
Shidai wannan gari sarkinsu ya kasance mugune
kuma azzalumi , yana bautar wani dodone kuma
wannan dodo kullum sai an yakama sa bil'adama
yasha jininsa , kullum barade sukan fita zuwa
farautar mutane, sukuma mutanen garin yayin da
baki suka shigo gari sai su yan yamesu da
abubuwan makulashe wanda aka zuba amaganin
bacci aciki kana ci shikenan naka yaja
.
Yayin da dakarun sarki masu farautar mutane
suka fita farauta izan har basu sami mutum ba
sai sudawo izuwa birnin su a cikin mutanen gari
sai ayi kuri'a duk wadda tafada kansa toh shine
za'a yanka wa dodon da sarkin ke bautawa ya
shi jininsa.
.
.
Ashwar na zuwa kasuwar wannan gari sai jama'a
suka yanyameshi dakayan ciye ciye shikuma duka
ya basar yace musu bayaci
Koda sukaga alamar cewa ashwar bazaici kayan
ciye ciyen ba sai suka hasala suka haiko masa da
nufin su kamashi
Koda ashwar yaga haka ai saiya ciro takobinsa
yaringi saransu yayin dasuka ga ashwar yayi
musu muguwar barna sai suka rabu dashi
.
Can sai gawasu dakaru nan sun kama wani
mutumi ma'abocin fararen kaya sun yiwa wannan
mutumi jina jina suna tafaman jansa akasa
.
Koda suka kariso gaban sadauki ashwar sai
shugabansu yace dashi kai wa ne ne kai da
harzaka shigo cikin birninmu sannan kayi mana
irin wannan ta'adi
.
Ashwar yace dashi ni bakone
.
Shugabar wannan dakaru ya zaburo domin
yakama ashwar aisai aswar yai wa shugabar
dakarun karo afuska,
Sai gashi ya baje akas ko shurawa baiyiba da
jama'a suka suka ga haka sai gudu, sauran
dakarun da suke tsaye suka ce da wa Allah ya
hadasu in ba ashwar ba? Ashwar baiyi tunanin
amfani da makami ba a wannan fada, don haka
hannu da kafarsa ne makamansa cikin kankanin
lokaciya tarwatsasu.
.
.
Shuraih 99% ke magana
.
Kuyi hakuri in kunji nayi kuskure ku gyara min
.
Muhadu a part 1C
,
Littafin Amdulaziz sani/m gini(kings of adventure
stories)

.
Littafina day (1)
.
Part 1C
With shuraih 99%
.
Typing :- http://facebook.com/shuraih.usman
.
Ashwar ya kwance wannan dattijo , sai ya hangi
wasu dakarun sun bullo da kwari a hannayensu.
Ashwa ya yunkura yai alkafira izuwa inda dokinsa
yake , ya ciro mashinsa ya rike a hannu daya
yana majajjawa da shi . Dattijo ya koma bayansa
ya buya . Dakarun nan suka sako ruwan kibau ,
ashwar yai ta kadewa da mashin hannunsa , har
kibiyoyin nasu suka kare , sai suka zare takubba
suka yiwo kansa anan nefa ashwar yayi tunanin
yazama wajibi yayi amfani da makami.
Don haka sai ya matsa jikin dokinsa ya dau
takobin nan nasa zabbau , nan fa wuri ya
yamutse, barade na kai masa sara da suka yana
karewa , shi ma yana kai musu , sai da aka sami
sa'a guda ana wannan fafatawa sannan ya karar
da su.
.
Koda ya waiga bayansa sai yaga dattijannan
akwance jini na zuba ta gefen cikinsa . Ashwar ya
ruga gareshi ya sunkuya ya dauke shi . Faruwar
hakan keda wuya ya hango wata bataliyar ta irin
wadannan dakarun da yayi fada dasu , wadannan
dakarun yawansu ya ninka na baya sau uku.
Badan tsoro ba sai don ya ceci yaruwar wannan
dattijon
Ashwar yayi sauri ya haye dokinsa rungume da
dattijon yayi cikin jeji a sukwane , dakarun suka bi
bayansa amma cikin kankanin lokaci ya basu rata
mai yawa , har ya bace musu ,
Dole suka hakura suka koma da baya.
.
Yayin da ashwar ya fuskanci sun tsera wa
wadannan makiya , sai ya tsaya a karkashin
inuwar wata bishiyar , ya sauko da dattijon nan
yayi masa shimfida ya kwanta , sannan ya dauko
wani dogon rawani daga cikin jakarsa ta daure
cikin dattijon don tsaida jinin dake zuba .
.
Ashwar ya dubi dattijon a yayin dayake kakarin
mutuwa yace "yakai babana sanar dani inda zan
kaika kusa ayi maka magani"
.
Dattijon ya yunkura cikin karfin hali tare da
taimakon ashwar ya hada bayansa da jikin
bishiya ya zauna , numfashinsa na fita sama-
sama yace
"Yaro kada ka wahalar da kanka ,ni tawa ta kare ,
kasani daga nan zuwa garinmu tafiyar wata guda
ce , nafito daga birnin Nurul islam ne , garine na
ma'abota Addinin musulunci , abin dayasa kaga
wadannan mutane sun kamani suna tayi mani
azaba , saboda sun ga ina bautar ubangijin
musulunci ne ina sallah"
.
Koda da jin wannan batu sai ahwar ya tuno da
labarin da tsoho makabul ya bashi dangane da
maganar boka akan daukakar da zai samu
aduniya , nan take ashwar ya sake tallafe tsohon
nan akirjinsa yace
"Tuni ina da labarin wannan Addini naka , kuma
nayi imani dashi a zuciyata shigar dani cikinsa"
.
Dattijon yayi wani irin tari mai ban tsoro idanunsa
suka kakkafe kamar ya mutu , amma sai
numfashinsa ya sake dawowa yace a cikin
karamar murya "yakai wannan saurayi ka saurari
abin da zan fadi yanzu ka maimaita shi, idan kayi
haka ka zama musulmi.
.
Nan take dattijon yai kalmar shahada , daa
ashwar yakasa kunnensa da kyau dai dai dattijon
na gama fadin kalmar ransa ya fita ,
Shi kuma ashwar sai ya maimaita kalmar
shahada, sannan ya mike ya haka rami ya binne
dattijon yasa alama a kabarinsa , sannan ya hau
dokinsa da nufin tunkarar birnin Nurul islam
.
Kwanci tashi ashwar nata tafiya a cikin jeji kwana
da kwanaki bai sake gamuwa da komai ba face
namun jeji, wasu sai yayi kallon kallo da su ,
wasu kuma ya fafata da su ko su tsere da kansu
don ganin wuya ko kuma ya hallaka su , shi
kansa ashwar sai da ya dunga mamakin irin
wannan baiwa daya keda ita ta sadukantaka da
jarumta da kuma rashin tsoro, ya tuno da cewa
tun baifi shekara goma sha ba , mahaifinsa ke
tafiya da shi farauta jeji, da hanunsa ya sha kama
'ya'yan kura da damisa ya murde mudu wuya su
mutu.
.
Tafiya dai taci gaba har ya sami kwana talatin cif
, duk tsawon iyakar kwanakin nan ashwar yayi a
lissafe suke a kwalkwalwarsa , kuma arubuce jikin
kefen takobinsa , ba dan komai ba yayi haka ba ,
sai don kada ya wuce wa'adin da sarki abul dinar
ya diba masa ba komawa gida , sau tari idan
ashwar ya tuno da gimbiya mabaruka sai yayi ta
yan wake wakensa ta soyayya shikadai cikin
tsakiyar dokar daji,
In banda tsuntsaye da suke tayashi da sautin
kukansu, ba ya samun mai tayashi debe kewa
.
Kwatsam ya hangi karamin gari a gabansa , kai
tsaye ya tasamma garin har ya isa , da zuw a ya
iske gaba dayan mutanen garin sanye suke cikin
kamilar sutura mazansu da matansu, musamman
ma matan ko'ina a jikinsu a rufe yake , kwayar
idanunsu kacal ale gani Abin da ya fara riska
shine wani gini wanda ya iske mutane a kofarsa
suna ta shiga, wasu kuma sun tsuguna suna
wanke gabban jikunsu da ruwa. Daga can kuma
sai yaga wani daga cikinsu ya hau bisa wani tudu
dake jikin wannan gini yana wasu maganganu
masu kama da karatu, aciki karatun ne ya ji ya
ambaci kalmar nan ta shiga musulunci wadda
marigayi dattijo ya biya masa .
Koda jin haja sai farin ciki ya lullube Ashwar. Ya
gane cewa wannan gari shine Nurul islam
.
Shuraih 99% nake ce daku
.
Ashwar ya sami wuri ya tsaya , ya sauka daga
kan dokinsa ya tsaya cak yana kallon mutane
suna kallonsa. Jim kadan sai yaga kowa ya shiga
cikiN dakin nan, mutum daya ya wuce gaba saura
suka tsaya bayansa aka fara wani aiki mai kama
da bauta . Ashwar na tsaye yana lekensu da
mamakin abun da sukeyi har dai suka kammala ,
suka firfito wannan mutum wanda ya shugabanci
aikin bautar ya nufo inda ashwar ke tsaye
.
Balarabe ne fari , kuma dogo kyakkyawa,
shekarunsa zasu kai hamsin da doriya, kamar
yadda yake balar
Abe haka dukkanin sauran mutanen garin suke
.
Da zuwa ya kalli ashwar yace" yakai wannan
bako daga ina kuma me ya kawoka birninmu"
.
Da ashwar yaji wannan tambaya acikin yaren
daya sani ne wato larabci sai murna ta kama shi,
nan take ya kwashe labarinsa tun daga farko har
karshe ya zaiyana masa . Duk wannan abu dake
faruwa sauran jama'ar gari na tsaitsaye a gefe
suna kallo.
.
Ashwar na gama bada labari ,sai wannan mutumi
ya rungumeshi yace "ai ka zama dan'uwanmu
tunda ka shiga Addinin Musulunci, wannan daki
daka gani mun shiga masallacine ne inda muke
sallah, wannan dattijo daka gamu dashi a wancan
gari na baya daga cikinmu yake, kuma yaje ne
isar da sakon Allah ga wadannan makafirta , shi
yasa suka tsareshi suka yi tayi masa azaba .
Kashe shi da sukayi kuwa sun taima ka mashine,
don yasamu shahada babban rabo a wajen
ubangijin musulunci"
.
Balaraben ya kara da cewa "Ni sunana Imamu
Hamid , ni ne shugaba a wannan gari yanzu
tunda Allah ya kawo ka garemu sai ka zauna
awannan gari don kasab yadda ake bautar Allah
kuma ka fahimci Addini , tabbas ubangijin
musulunci mai taimako ga bayinsa ne , wadanda
suka dogara dashi , tabbas zaka nasara a bisa
abin daka fito nema . Izan har baka kaucewa
dokokin Allah ba"
.
.
Nan take Imamu Hamid ya rukke hannun ashwar
ya tafi da shi izuwa gidansa. Gaba daya garin
kuwa ya cika da labarin zuwan jarumi ashwar ,
da kuma ababan al'ajabin da ke tattare da shi
.
Ashar ya zauna a garin Nurul islam har tsawon
sati uku inda ya koyi ibada har da karatun
alkur'ani daya ke Allah yabasi kaifin basira cikin
'yan kwanakinnan ya samu ilmi mai yawa, kuma
ya karbi littatafai na sauran fannonin ilimin
Addinin kamar tauhidi da dae sauransu, ya
kudurce a ransa zai ci gaba da neman ilmin
addini a duk sa'add ya sadu da masana.
.
Ranar da ashwar ya cika kwana ashirin da uku a
wannan gari na Nurul islam, a rannan yai sallama
da su Imamu Hamid aka kawo guzuri mai kyau
aka bashi , ya yi godiya sannan yai bankwana
dasu , yatafi yana mai bakin cikin cikin rabuwa
dasu, suma suna yi, sakamakon shakuwa da
albarkar HASKEN MUSULUNCI(next book insha
Allah)
.
LoKacin da ashwar yayi dan nisa da gari , sai
rubuta adadin kwanakin da yayi ajikin kufe na
takobinsa, ya lissafa dana baya sai yaga a halin
yanzu ya cimma wata uku saura kadan, ya
zamana kenan baifi saura wata guda da 'yan
kwanaki ba wa'adin da aka dibar masa ya cika ,
wannan yasa hankalinsa yayi mummunan tashi ,
domin ko abirnin inda Nurul islam bai samu
wanda ya taba jin labarin inda birnin duma yake
ba.
.
"Yanzu yaushe nasan inda wannan gari yake har
naje na dauko bishmalu ,sannan na koma
garinmu duk a cikin wadannan kwanaki?"
.
Tambaya ce wadda ashwar yayi wa a zuciyarsa ,
kuma shi kansa baisan amsarta ba .
.
Bayan kamar rabin sa'a yana tafiya , sai hadari
ya hado , nan take ruwa ya kece kamar da bakin
kwarya ,dan haka sai ashwar ya ruga karkashin
wani dutse ya fake , ya daure dokinsa a jikin
kafarsa sannan ya kishingida , cikin yan dakiku
kadan bacci ya saceshi.
.
Yana cikin wannan baccine dokinsa yayi haniniya
yaja kafarsa , ashwar ya tashi ya duba bai ga
komai ba ,
Kawai sai ya koma baccinsa. Dokin ya kara
haniniya a karo na biyu . Ashwar ya farka a
fusace ya mike ya dada dubawa ko'ina bai ga
komai ba , sai yayi tsammanin dokin nasane yake
bukatar yayi kiwo, don haka sai ya kwance shi ya
koma baccinsa .yin hakan keda wuya , kawai sai
yaji saukar wani abu ajikinsa , yana bude ido
yaga raga ta rufe shi, wasu dakaru kimanin su
arba'in na ruke da ragar da makamai sun kewaye
shi
.
"Tashi mu tafi " daya daga cikin baraden ya fadi.
.
Kada ku manta kuna tare ne da shuraih 99%
.
Ashwar ya dubeshi ya dubi sauran, ya tabbatar
babu imani a fuskokinsu, da farko yayi niyyar ya
ganar dasu kuransu, amma sai yace a ransa
.
"Bari dai naga gudun ruwarsu"
.
Batare da gardama ba ya bisu izuwa wani gida
aka sa shi cikin wani daki aka kulle har magariba
ta kawo jiki.
Wannan tsarewa da aka masa batazo masa da
illa ba sai dai rashin sallah da kuma dokinsa da
yake tunanin ya bace a jeji, gashi duk
makamansa na fada na jikin dokin .
Ashwar yadaga hannunsa sama ya roki Allah
yasa wannan tsarewa ta zame masa alheri
.
Washe gari wannan tawaga data kamo ashwar
suka taru acikin gidan , gaban ubangidansu, inda
dayansu da ke bayanin cewa basu samo koda
tsuntsu ba sai wani yaro da suka samo yana
ajiye a cikin daki.
.
"To yaushe zaku cinyeshi? Ko kuwa kun fison ku
gama da tsofaffin da ku ka kamo tukunna"
.
Gaba daya sukace ai sunfi son yaron, saidai yayi
musu kadan, dan wani ma bazai samu koda
rabon kunne daya ba , nan take ubangidan
wadannan mutane yayi musu sulhu, akan a fito
da naman gaba daya a cinye don kar ayi fada.
Wannan zance gabadaya a kunnen ashwar akayi
shi.
Don haka sai ya cika da mamaki daya ji ana
maganar a cinye dan adam kamar yadda ake cin
naman dabba.
.
"Ni kuwa naga ta yadda za a cinyeni ina ji ina
gani"ashwar ya fadi cikin zuciyarsa.
.
Dankari makari,lallai yau akeyinta inji 99% ke
magana'
.
Jim kadan aka bude dakin da ashwar ke ciki,
abinci ne aka kawo, wani gajeren mutum ne kato
ya shigo da shi cikin wata karamar tasa ko
sallama babu ya ajiye , ya juya ya fita aka
garkame kofa, ashwar ya dubi abincin na yaga bai
san irin saba gashi yana jin yunwa amma sai
yafara wasi wasi ko yaci ko ya bari.
Tabbas yasan dae mutanenan kafiraine baisan
ma koda me sukayi abincin ba. Kawai sai ya
yanke shawarar yayi baccinsa na jiya da baikarisa
ba , nan take ya bingire yai ta sharara barci
kamar wadda yake cikin gidansa
.
Kwatsam yaji wata murya a sama ance " tashi
mu tafi"
.
Yana bude idanunsa yaga wasu kartine suk uku.
Ashwar ya tashi bako musu suka sa shi agaba
sai wajen babbansu , wani katone mai tumbi, ya
saki ciki sai kace garwa. Cikin tsawa ya dubi
kattin yace
.
"Ku ajiye shi anan ! Ku fito da tsofaffin"
.
Ashwar ya zauna yana kallon ikon Allah sai yaga
an fito da mutane sun fi dari, nan dai yaga anjera
su gaba daya alayi kamar masu shirin tada sahun
sallah,
Hardashi ahwar din
Mai katon cikinnan ya tashi da kyar ya fara
zagaya su ashwar, bai dafa kowa ba sai wani
tsoho wanda ko kyaleshi akayi ya kalli kisan da
za'aiwa sauran zai iya mutuwa don tsananin
firgita , don ko ayanzu ma baisan cewa yana
fitsari a wando ba , jikinsa na kyarma tamkar mai
mugun zazzabi , nan take karti suka kama
wannan tsoho suka jefa shi cikin wata katuwar
tukunya wadda ke karkashin wata murhun wuta
na dafuwa, ruwan ya cikinta sai zabalbala yake ,
Ai kamar hadiyar kwayar gero haka tsohonnan ya
lume cikin tukunyar , ko tarinsa ba'a jiyo ba.
Wasu karti su biyu da suke rike da ludayin
tukunyar suka hada hannayensu hudu suka tura
ludayin zuwa karkashin tukunyar suka tsamo.
Sai ga gangar jikin tsohonnan ta motse kamar
curin nakiya, gaba daya fatar jikinsa ta sutale
duka akansa kuwa babu silin gashi koda daya ,
atakaice dai ya dahu yai lugub . Ja daya za aiwa
tsokar namansa ta rabu da uwar jiki.
.
Koda ganin wannan al'amari sai ashwar yai salati
yace" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
.
Kafin a ankara ya suri kato guda ya mai dashi
bulala , yai ta dukan sauran kattin , nan da nan
gida ya rikice da ihu da kuwwa , katon nan da ke
zaune a kujera kamar kula sai kujerar ta karye ya
fado ji kake tim! Bama kafiran azzaluman
mutanen ba wadanda ma aka kamo don acinye
saida suka gigice.
Tsoffin cikinsu suka shiga wani hali don wasunsu
ma sun fado sun ture abincin . Azzaliman kuwa
duk sun firgice sun dimauce , wasu su kayi waje
da gudu wasu suka yiyo kan ashwar wato masu
karfin halin kenan , shi kuwa yaci gabada da
rugurguzarsu suna zubewa kamar mai kada
karmami. Musulman da aka kamo suka hau
salati.
.
Bayan da ashwar ya sumar dana sumarwa ya
kashe na kashewa , masu gudu kuwa suka tsere
ya rage saura shugaban masu cin naman
mutanen nan kadai, kwance akas ya kasa tashi
bare ya gudu, sai nishi yake da kyar , nan take
ashwar ya kaimasa wawura ya sunkuce shi sama
duk girmansa ya zama na banza , don tamkar
ashwar ya daga buhun audiga ne, tsundum ya
jefashi cikin wannan tukunya mai zabalbala ,
jama'a gaba daya suka rugo wajen ashwar suna
yi masa godiya da sa albarja ashwar ya fice ya
bar su suna ta murna da wake-wake .
Wani abin mamaki yana fitowa daga cikin gidan
sai ya iske dokinsa tsaye kamar dama yasan da
fitowarsa yanzu,
Ashwar ya kalli dokin yayi murmushi sannan yace
"Daga yau nasa maka suna ganjarma"
,
Kai masu karatu nafara gajiya fa 99% ke magana
,
Ashwar yayi tsalle ya haye kan ganjarma , ya
sukwane shi zuwa cikin jeji.
Wannan shine abin daya faru ga jarumi ashwar,
bayan ya baro garin Nurul islam
.
.
Naga kamar bakwason littafinnan
Anya kuna son inci gaba kuwa
.
.
Littafin abdulaziz sani/m gini(kings of adventure
stories)
BABBAN GORO
-----------------------

Littafina daya
.
Part 1D
.
With shuraih 99%
Typing by :- http://facebook.com/shuraih.usman
.
Al'amarin kifyan sarkin aljanu kuwa wanda
gidansa yake cikin karkashin kasa , a tsakiyar
ruwa, rabon daya fito tun lokacin daya bayar da
tsaron bishmalu dan sarki kan'anu na misra
.
A halin yanzu bishmalu ya zama saurayi dan
shekara sahirin da biyar. Kuma a iya tunaninsa
bai da wani uba wanda ya fi kifyan , amma bai
taba ganinsa ba a zahiri sai acikin madubin tsafi
.
Fitowar sarki kifyan keda wuya aka lullubeshi
masu gaisuwa nayi, masu bambadanci nayi
shikuma sai ya hau kankaragarsa ta mulki ya
zauna , sannan yace aje a zo masa da dansa ,
nan take aka zo da bishmalu , bishmalu ya
durkusa yayi gaisuwa.
.
Kifyan yace" na fito ne domin ganinka , dakuma
son gabatar da wani muhimmin zance a gareka ,
wanda baka san dashi ba , yanzu ne lokacin da
zan yi maka bayani ka fahimta tunda ka mallaki
hankalin kanka .ya kai bishmalu ka dubi kowa
dake cikin fadar nan ka dubi kanka ,zaka ga cewa
ba irin kirar halittar ka bane , domin mu aljanune
kai kuma bil'adama ne, to kasani kai ba dana
bane . iyayenka bil'adama ne kamar kai , ni sato
ka nayi tun kana jariri sakamakon laifin da
mahaifinka yai mini, ya auri matar dana ke so"
.
Nan take kifyan yai nuni da hannunsa izuwa wani
madubin tsafi ! Sai ga hoton sarki kan'anu
kwance bisa gado a turakarsa yana jinya.
.
"Wannan shine mahai finka, daga nan zuwa inda
mahaifinnan naka yake tafiyar wata da watannice
. Kasani ya kai bishmalu son dana kewa
mahaifiyarka shine ya dawo kanka a yanzu.
.
Kifyan ya sake nuni da hannunsa izuwa wani
madubin tsafi sai ga hoton ashwar bisa doki a
dokar daji yana tafiya.
.
"Wannan wani jarumine da ake kira ashwar ,
wanda ya taho da niyyar fitar dakai daga cikin
gidannan ya mai da kai hannun babanka, amma
bai san cewa yayi babban kuskure ba , har duniya
ta tashi ba wani mahalukin bil'adama daya isa
ya shigo cikin fadata"
.
Kifyan na gama wannan jawabi ya tuntsure da
mahaukaciyar dariya wadda tasa gidan ya kama
girgiza , har sai da ya rufe bakinsa sannan gidan
ya tsaya daidai.
.
Bishmalu ya dubi sarki kifyan yace " ya kai sarkin
sarakai badan kada ranka ya baci ba da nace
kasa akaini wajen mahaifina mu gana "
.
Cikin fushi sarki kifyan ya mangare bishmalu da
iskan bakinsa sannan yace" a kul nakara jin kace
na kaika wajen babanka"
.
'Da nine inba sai ankaini wajena babana ba ko
ata masifa 99% ke magana
.
.
"To kasani daga yau duk kimarka ta zube a
idanuna gwarama ka kasheni na huta da takaicin
abin daka yiwa mahaifina"
.
Kifyan ya sake bushewa da dariya , sannan
yadubi fadawansa yace" ku na son wannan yaron
ko kuwa na kasheshi yanzunnan?"
.
Gaba daya suka rude da cewa " muna sonsa ya
sarkin duniya"
.
Wannan hayaniya ta fadawan kifyan tasa
bishmalu ya firgice ya fadi kasa sumamme,
Nan take sarki yasa akayi wani turare na hayaki ,
aka fesawa bishmalu ya farfado, sarki ya sake
dubansa yace
" Yanzu wakake so mu ko iyayenka"
.
Bishmalu yace" ku nake so, don ku ne kuka
reneni , ban san wadan can ba"
.
Koda jin haka sai fada ta rude da shewa , nan
take akayiwa bishmalu wanka ya zama dan sarki
kifyan, aka yi biki da gagarumat walima , bayan
an kare, sarki kifyan ya zagaya da bishmalu cikin
fadodinsa guda ashirin da bakwai da ke cikin
wannan gida na sarauta, ya nuna masa sirrikansa
gaba daya banda sirrin inda ruhinsa yake.
.
Wannan shine abin daya faru tsakanin sarki kifyan
da bishmalu dan kan'anu na misra, wanda ke can
kwance cikin jinyar rashin lafiya tsawon shekaru
ashirin da biyar.
.
.
Shuraih 99% ke ce daku
.
Ashwar na can cikin jeji ya kutsa kai , bai san ma
inda yake nufa ba . Kwanci tashi yaje wani gari ,
yasamu wasu mutane a bakin kofar shiga ashwar
ya sauka daga kan ganjarma yayi wa mutanen
sallama , sai yaga basu kalleshi ba , ya kuma
matsawa yai sallama , kawai sai suk zabura
wajen su goma shahudu suka kewayeshi, wani
daga cikinsu yace
"Kai yaro mene ne ya biyo dakai ta wannan
kofar? Baka sani ba cewa garinnan yana da kofofi
hudu amma wannan ta zama mallakinmu? Ba a
wucewa ta nan sai anbiya harajinka dana
dokinka"
.
Ashwar ya dubesu a wulakance yace" menene
kuma haraji?"
.
Wannan batu ya harzuka gudansu, don haka sai
ya zagaya bayan ashwar da nufin ya sharara
masa mari, caraf sai ga hannunsa a hannun
ashwar, ya zaci abin na wasa ne , sai yaji ana
rumurmutse masa hannu kamar gyale , mtumin
ya ringa ihu da sauran suka ga haka sai suka
debi sanduna suka rufe ashwar da duka titim!
Titim!! Suna bugunsa sandunan na karairayewa ,
tamkar akan dutse suke bugawa . Gaba dayansu
suka firgita da ganin wannan al'amari, sai suka
arce
.
Ashwar ya kada linzamin dokinsa ya shiga cikin
gari . Yana cikin tafiya yaga wasu 'yan mata su
shida kyawawan larabawa , sun debo ruwa a tulu
daga rafi . Ashwar ya dubi wadda tafi sauran
kyawu yace " 'yan mata dan Allah taimaka mini
da ruwannan mana na sha"
.
Batare da jin kai ko wulakanci ba ta miko masa
tulunta, Ashwar ya karba ya kafa kai ya zuke fiye
da rabinsa, sannan ya miko mata, sannan yayi
godiya .
Sauran 'yanmatan suka dubeta suka kyalkyale da
dariya , wata cikinsu tace
.
"Yanzu ke Asma'u don wahala bata isheki ba
shine zaki bayar da kyautar ruwan da kika debo
acan nesa da gari , aikuwa mu baza mu koma da
baya ba don raka ki debo wani"
.
Nan take suka wucu su kai gaba , ita kuma
Asma'un sai ta dora tulunta aka ta juya da baya
dan komawa rafi. Koda ganin haka sai ashwar ya
sauka daga kan dokinsa yace ta hau , shikuma ya
ruke mata tulun , batare da musu ba Asma'u ta
hau kan ganjarma Ashwar ya ruke mata linzamin ,
su kai gaba suna tafe suna hira kai da kagansu
sai ka dauka bawa ne da uwargijiyarsa,
kasancewar ashwar bakin fata ita kuma
balarabiya.
.
Shuraih 99% nake ce daku"Kai kuna tare dani
kuwa "
.
"Baiwar Allah shin anan garin kuwa akwai
musulmi mabiya Addinin musulunci?"
Ashwar ya tambaya
.
"Kwarai kuwa , fiyr da rabin mutanen garinnan
duk musulmine sai de , saidai sarakunanmu
azzalumaine , kuma mai karfi shi ke da ikon yin
abinda yaga dama , yanzu haka da akwai wasu
azzalumai 'yan fashi da suka addabe mu, shi
yasa da zarar magariba tayi kowa sai ya shige
gidansa ya rufe kofa , komai zafi ba a isa ayi
kwanciyar waje ba , in kuwa mtum ya kwanta a
waje saidai da safe a ga gawarsa "
.
Koda ashwar yaji haka sai ya cika da mamaki
yace " Ni kuwa da yardar Allah zanyi muku
maganinsu daga yau sun dai na yin fashin"
.
"Haba dan samari wane kai , ai BABBAN GORO
SAI MAGOGIN KArFE. Mutanan da sun fi mayakan
garin nan ma karfin tsafi da sihiri , ya za kai da
su"
.
"To shikenan tunda kina shakka ina so ki amince
mini kwana a kofar gidanku"
.
"Wannan mai saukine amma fa duk abin daya
sameka kada ka zargi kowa ka zargi kanka"
,
99% ke magana kuna biye dani kuwa
.
Haka dai ashwar da Asma'u suka ci gabada hira
har suka je rafi suka debo ruwa suka dawo.
Asma'u takai ashwar gidansu ta gabatar dashi a
gaban iyayenta , tare dayi musu bayanin tarar
aradu daka wadda yace zaiyi cikin mamaki
mahaifin Asma'u ya dubi ashwar da kyau yace
.
"Kai yaro shin rayuwar duniyace ta ishe ka haka
ko kuwa wani abin bakin ciki ne yasa kazabi
mutuwa akan rayuwa?"
.
Ashwar yayi murmushi yace " baba babu ko daya
amma dai ni nakasance mai son yin fada da
karya da kuma azzalumai, na tsani kafirci da
zalunci , burina Addinin musulunci ya rinjayi
kafirci a doron kasa, bana dogoro ko takama da
karfi ko tsafi,face taimakon ubangijina wanda
shine masanin dukkan abinda ke fili da boye "
.
Wannan batu yasa jikin mahaifin asm'u yai sanyi
yayi shiru daga bisani yace
"To masu magana sunce ba'a kwacewa yaro
garma amma wannan garmar da kake shirin
dauka tafi ka nauyi sai dai muce Allah yaba sa'a"
.
Haka dai ashwar ya cigaba da hirarsa da Asma'u
da iyayenta har rana ta fadi.aka kawo abinci
sukaci tare gabadaya , magariba nayi suka yi
sallama da shi suka shiga cikin gida suka rufe
kofa .shi kuwa gogan sai yai alwala yai sallah a
kofar gidan , har ya idar da sallar yayi yan
Addu'oinsa baiga wani yazo gare sa ba ,
Ashwar ya debi ruwa arijiya ya baiwa ganjarma
sannan yai shimfida. Agefe gida yayi kwanciyarsa
tamkar yana cikin dakin matarsa.
.
'Yan fashinnan da suka saba shigowa sai gasu
sun dira akan ashwar kimanin su arba'in ashe
Asma'u a soro ta kwanta koda taji magan
ganunsu sai ta kwalla ihu take ashwar ya farka ,
alokacin har daya daga cikinsu ya hau kan
ganjarma yana cewa
" Ni kam yau na fito a sa'a na samu lafiyayyen
doki"
.
Ashwar ya mike zumbur ya dube su yace " ku
azzaluman bayi me ke tafe daku"
.
Gaba dayansu suka bushe da dariya , dayansu
yace
"Yau kuma bakon marar kunya aka samu a
garinnan ? Kai yaro yau karar kwana ta kawo ka
makasa "
.
Wannan batu ya fusata ashwar nan take ya hausu
da duka, gashi babu ko allura agareshi amma su
da manyan makamai a hannunsu ya zame musu
ala kakai, duk wanda yakai masa sara ko suka
sai ya goce cikin zafin nama ya kama hannunsa
ya murde ko ya karya. Cikin kankanin lokaci ya
zubar da mutum goma kasa sumammu da 'yan
fashinnan suka ga haka sai suka fara jarraba
tsafe tsafensu da sihirce sihirce, amma duk suka
zama a banza don basuyi tasiri ba akan ashwar ,
sakamakon Addu'ar daya ke ta karantawa a
zuciyarsa , nan fa wuri ya dada ya mutsewa , ihu
da kuwwar 'yan fashin tasa duk jama'ar garin
suka bubbude gidajensu suka fito, don ba'a taba
jin irn wannan tashin hankali ba a garin . Yayin
da jama'a suka taru sai aka iske ashwar tsaye
shi kadai a kofar gidansu Asma'u .
'Yanfashinnan gaba dayansu su arba'in suna
kwance cikin jini, wasu a sume , wasu akarairaye.
Nan take gari ya dauka da shewa don farin ciki
aka yi ta al'ajabin jarumtakar ashwar.
.
Koni nan nafishi jarumta 99% ke magana
.
Ita kuwa Asma'u saita ruga da gudu ta rungume
Ashwar tana cewa ta samu mijin aure Mutanen
gari sukayi ta kawowa ashwar kyautar dukiya,
amma ko daya bai karba ba .
Anan ya sanar dasu labarinsa da dalilin fitowarsa
daga garinsu, ya bukaci o akwai wanda yasan
inda birnin duma yake .
Gaba daya akayi shiru sai daga can wani dattijo
tsoho tukuf wanda duk garin babu mai tsufansa
ya dogaro da sanda ya karaso inda ashwar ke
tsaye ya dafa shi ya ce
.
"Yaro nasan inda birnin duma yake"
.
Koda jin haka sai farin ciki ya kama ashwar , ya
rungume tsohon yana mai matukar farin ciki,
daga nan yabi tsohon zuwa gidansa.
.
Daga nan zuwa birnin duma tafiyar shekaru
ukune.
Birnin duma garine na aljanu zalla inda sarki
kifyan ke mulki" dattijo yafadi tare da ajiye
numfashi.
.
Cikin tsananin damuwa Ashwar yayi ajiyar zuciya
yace " hakika duk abin da aka fadi haka yake ,
amma ni yanzu guiwata tayi sanyi , burina ya
yanke ,domin babu yadda za'ai naje birnin duma
a cikin kwanankin da aka diba mani wa'adi"
.
Bisa mamaki tsohon ya dubi ashwar yace "ban
gane bayanin ka ba "
.
Shuraih ke cewa daku
.
Nan take ashwar yai masa cikakken bayani kan
sharadin da sarki Abul dinar ya shimfida masa ,
kafin ya amince ya aura masa gimbiya mabaruka
. Tsoho yayi shiru yana tunani har izuwa wani
dan dogon lokaci , sannan yace
"Ya kai wannan jarumi ina da wani dan'uwa
wanda zai iya taimakonka a bisa wannan al'amari
sunansa raslanu , bawan Allah ne wanda ya
kaura daga cikin gari ya koma can jejin surgam
yaci gaba da bautar ubangiji, don kada wani abun
duniya ya rude shi daga nan zuwa jejin surgam
tafiyar kwana goma sha biyuce, amma ka sani
akwai ababan hadari a wannan jeji, fiye da
shekaru sittin a tarihi babu wani mutum wanda
ya keta ta cikin surgam batare da ya zama gawa
ba, face wannan dan'uwa nawa wato ruslanu. Shi
ma hakan ta farune sabida Allah ya hore masa
baiwa mai dumbin yawa . Idan har ka sami
nasarar ganinsa , tamkar ka sami nasarar shiga
fadar sarki kifyan ne"
.
Ashwar yayi shiru yana nazarin wannan bayani
sannan yace " ya kai wannan dattijo mai albarka ,
ina tabbatar maka da cewa ko zan rasa raina sai
naje jejin surgam na sadu da wannan dan'uwa
naka Ruslanu, kuma gobe goben nan zan yi shiri
na tafi
.
Ashwar na rufe baki suka jiyo tambura sun cika
gari , cikin sauri suka fito daga cikin gidan, kawai
sai su kai arba da mutane jingim akasa , sun rako
wani doki guda daya izuwa ga ashwar , ba kowa
bane akan dokin face Asma'u ta sha kwalliya da
ado irin na amare, cikin mamaki ashwar ya
tambaya
"Me ke faruwane"
.
"Ai an daura aurenka ne da Asma'u , yanzu haka
amaryarka muka kawo maka"
Mahaifin Asma'u ne da kansa tabada wannan
amsar
.
.
Laifin dadi karewa
Abdulziz sani m/ gini ke ce daku
Kash! Mai karatu anan zan dakata sai mu hadu a
BABBAN GORO KaSHI NA BIYU don mu ji yadda
zata wakana
.
SHIN JARUMI ASHWAR ZAI YADDA DA WANNAN
AURE DA AKA YI MASA BATARE DA NEMAN
AMINCEWARSA BA?
.
ME ZAI FARU YAYIN TAFIYARSA ZUWA JEJIN
SURGAM?
.
A CIKIN WANI HALI GIMBIYA MABARUKA TAKE
AYANZU?
.
SHIN ALJANIN BOKA GULMANU KUTUNTUMA NA
BIYE DA JARUMI ASHWAR KUWA?
.
TA YAYA ASHWAR ZAI SHIGA BIRNIN DUMA HAR
YA SHIGA FADAR SARKI KIFYAN YA DAUKO
BISHMALU?
.
Toh Alhamdulillah dama tun kafin nafara na sanar
daku cewa book 1 ne kadai akasa
.
Sai kun jini a sabon littafi

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)