ZIYARAR SHEDAN WAJEN ANNABI YAHAYA (AS)

ZIYARAR SHEDAN WAJEN ANNABI YAHAYA (AS)

Wata rana Iblis wato Shed'an (La) yaje wajen Annabi Yahaya Dan Zakariyya (AS) yace masa : "Ya kai wannan Annabi, Nazo ne don inyi maka nasiha..."

Sai Annabi Yahaya yace masa : "Qarya kake, kai baka isa ka yimin wata nasiha ba, sai dai abu d'aya nake son ka fad'a mani gameda Dan Adam !?"

Sai Shaidan (La) yace : " Ai su 'yan Adam a wajen mu sun kasu kashi uku.
Na farkon su sune wadanda suka fi wahalar da mu. Idan muka zowa  d'ayansu, zamu fiteneshi muga har mun kai ga galaba a kanshi ya kaucewa hanyar Allah.
Bayan ya aikata zunubi sai ya tuba ya koma ga Allah yana mai istigifari, har ya 6ata mana duk wani shiri da mukayi akan shi. Haka zamu yita bibiyarshi muna son 6atashi shi kuma sai ya kasance kullum mai yawan istigifari, don haka irin waddannan mutanen suna wahalar damu.

Amma su kuma kashi na biyu, su yadda suke a hannun mu, kamar kwallo ce a hannun yara, muna juyasu san Ranmu, waddannan mun riga mun gama da su.

Kashi na qarshe kuwa, sune irinka Ma'asumai wadanda Allah ya rigaya ya kiyayesu, ba zamu ta6a samun wata dama a kansu ba."

Sai Annabi Yahaya (as) yace masa : " Duk da haka, shin  ka ta6a samun wata dama a kaina? "

Sai Shed'an (La) yace masa : " A'a. Sai dai sau daya ne rak ! Wata rana an kawo maka abinci zaka ci. Ban gushe ba  ina qawata maka abincin nan, har ya kai ga kaci da yawa, bacci ya daukeka a wannan daren, baka samu damar yin ibadun da kake yi ba kamar kullum."

Sai Annabi Yahaya (as) yace masa : " Ni kuwa, har abada bazan sake cin abinci in koshi ba !"

Sai shi kuma SheDan yace : " Nima kuwa bazan qara yiwa wani Dan Adam Nasiha ba."

***********************

Tunda mu ba MA'ASUMAI bane, babu abinda yafi dacewa da mu, illah mu da dawwama cikin istighifari, zikiri da salatin Annabi (saw) da yawaita karatun Alqur'ani. Da hakane zamu gagari La'ananne ibliss da mutanensa.

ALLAH YASA MU DACE, YA KUMA DA'DA KAREMU DAGA SHARRIN SHEDAN (LA).

Please  share to all Muslims...


Visit Www.ashblog.com.ng for more story
 


Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)