Illar Auto liker na wanda zaka samu likes da yawa a post dinka na facebook 


Illar Auto liker na wanda zaka samu likes da yawa a post dinka na facebook 


Assalamu Alaikum

'yan uwa abokai barkan ku da warhaka barkan ku da sake kasancewa da ni a wannan lokaci.


Ina mai baiwa duk wani wanda ya bibiyi post dina na baya mai suna "Yadda zaka samu Likes sama da 500+ a post dinka na facebook" Hakuri akan rashin sanar daku illar dake tattare da yin anfani da auto likes a facebook.


Shi dai Auto likes yawancin likes dinda mutum yake samu ta wannan hanyar da yawansu fake ne, domin a yau da naje na duba likes din da suke ban, mutumin da duk aka nuna yayi min likes idan na ziyarci account dinshi na duba active nashi sai inga ya kwashe kusan shekaru da yawa rabonshi da hawa online, daidaiku ne kawai zakaga 'yan kwanaki ne rabonsu da hawa facebook.


Duk bama wannan ba, ka sani idan har ka shiga cikin masu saka auto likes a post dinsu kuma baka iya kare facebook account dinka ba, to tabbas zaka iya rasa account dinka. Domin kana fara wannan harka zaka dinga ganin wasu sauye sauye a facebook dinka, misali zakaga wani yayi maka repley akan wani comment da baka san kayi ba, idan ka shiga notification din zakaga photo mutumin ya dora kai kuma kayi masa comment da "Nice pic" shi kuma yayi maka repley da thanks. kai kuma baka san lokacin da kayi masa comment din ba. Kuma zasu rinqa aikawa wasu friend request da sunan kai ne ka tura, ko kuma su rinqa join dinka a wasu tarkacen groupes da bakada ra'ayinsu.

Kuma koda baka fada hannun makwamusa ba, to facebook da kansu zasu kwace account dinka a matsayin kana yawan anfan da wasu website wanda basu dace ba.

Don Haka idan har kasan bazaka iya kare account dinka ba, yanada kyau ka hakura da wannan harka...


Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)