Soyayya : Yar Afrika mai shekaru 39 dake soyayya da wani bature mai shekaru 91


Ance "ita soyayya bata jin shekaru..." Wannan maganar ta sanya wannan Matashiya soyayya da tsoho mai shekaru 91.

Awanni biyu kenan da wata mata mai suna Adel a shafin sadarwa na facebook ta dora wadannan masoya, inda take cewa " Matashiya yar asalin kasar kamaru mai shekaru 39 na soyayya da wani tsoho mai shekaru 91. Masoyan na zaune ne a wata a nahiyar turai.

Abinda zai baka sha'awa ga masoyan shine yadda suke nunawa junan su so da kauna.. da yawan mutane na zargin cewa wata qila Matashiyar saboda kudinsa ne sonshi ... Wasu kuma na ganin kawai soyayya ce da ake cewa daman bata jin shekaru.


Mutane da dama sunyi ta tofa albarkacin bakin su akan wadannan masoya, inda da yawan mutane fatan alkhairi da tayasu murna sukeyi.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)