Mutum tara ne suka mutu a hare haren kunar bakin wake a kasar Nijar

A kalla mutum tara ne suka mutu, wasu da dama kuma suka ji rauni a wasu hare-haren kunar bakin wake uku da aka kai birnin Diffa da ke kudu maso gabashin Jamhuriyyar Nijar, kusa da kan iyakar Najeriya.

Biyu daga cikin 'yan kunar bakin waken 'yan mata ne, kuma cikin wuraren da suka yi niyyar kai harin har da wata makarantar islamiyya.

Duk da cewa babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma mayakan kungiyar Boko Haram sun sha kai hari Diffa.

Sai dai an dauki tsawon watanni ba a samu wani tashin hankali ba a yankin, har sai da aka kai wannan hari a ranar Litinin da yamma.

Tags

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)