Wani tsoho mai shekaru 72 yayiwa wata mata wanka da ruwan acid


Wata kotu  a garin Ile-ife jihar Osun a Nigeria ta garkame wani tsoho mai shekaru 72 a kurkuku a jiya Talata, 19 ga watan Yuni kan laifin yi wa wata wanka da ruwan Acid.

Wani tsoho mai suna Adegboye Emmanuel, mai shekaru 72 an gurfanar dashi a kotu kan laifin niyyar kisan keta akan wata mata.


Alkalin kotun mai suna Ishola Omisade, ya yi watsi da belin da lauyan wannan tsoho mai suna Mr Bolaji Adewale, ya nema. Alkalin Ya ce wajibi ne a garkame mai laifin a kurkukun Ile-ife.


Lauyan gwamnati mai suna Insp Emmanuel Abdullahi, ya bayyanawa kotu cewa tsohon ya aikata wannan laifi ne ranan 6 ga watan Yuni misalin karfe 9 na safe a Oluorogbo phase III on Ondo road, Ile-Ife.


Lauyan yace Tsoho Emmanuel ya yi kokarin kashe matar mai suna Abayomi Veronica ta hanyar watsa mata wani ruwa da ake kyautata zaton ruwan acid ne wanda ya ji mata mumunan rauni a jiki.

Tags

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)