Allah ne yayi mana maganin mulkin Abacha, kuma shine zai kara taimakon mu a 2019 – Obasanjo


-Tsohon shugaban kasa Obasanjo yace " Allan da yayi mana maganin mulkin Shugaba Abacha, kuma shine zai taimakemu a 2019."



haka zalika, ya bukaci ‘yan sabuwar jam’iyyarshi a CNM da su tabbatar sun tanadi katin su na zabe domin samun bayar da tasu gudunmawar kafin barin komai a hannun Allah

- Tsohon shugaban kasar ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar tashi da kada su karaya ko su ji tsoro

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja da kuma farar hula, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewar ya mika dukkan lamarin fitar da shugaba Muhammadu Buhari daga gidan gwamnati a hannun Allah. Ya bukaci ‘yan jam’iyyar sa da su mallaki katin zabe kafin zaben shekarar 2019.

Obasanjo na wadannan kalamai ne yayin wani taro da ya yi a garin Ibadan na jihar Oyo da ‘yan sabuwar jam’iyyarshi ta CNM (Coalitiona Of Nigeria Movement).


lokacin da yake bayar da misali ga masu sauraronshi, Obasanjo, ya ce haka Allah ya yi maganin Abacha lokacin da ya kafe sai ya cigaba da mulkin Najeriya ta kowanne hali.

wadanda suke a kan karagar mulki basa son a fada masu cewar suna yin ba daidai ba, burin su kawai su cigaba da zama a mulki Amma idan muka fada masu gas laifin mu,” a cewar Obasanjo.


Sannan ya kara da cewar, “Allah-n da ya taimake mu jiya ya kawar mana da Abacha shine zai taimake mu a zaben gobe na 2019. Amma fa mu ma sai mun bayar da tamu gudunmawar kafin mu bar wa Allah ragowar.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)