Wata Kotu a kasar Faransa Ta Daure Wasu ‘Yan Najeriya 16 Akan Fataucin Mata

Wata Kotu a birnin Paris a kasar Faransa ta yankewa wasu ‘yan Najeriya 16 hukuncin daurin shekaru 2 zuwa 10 bayan ta samesu da laifin fataucin mata inda suka yaudaresu da alkawuran aiki daga baya kuma suka tilasta musu yin karuwanci.




Masu shigar da kara sun ce mambobin wani shafin facebook ‘Authentic Sisters’ ne ke yaudarar mata inda suke nuna kansu a matsayin wata kungiyar da ke taimakon baki daga Najeriya, kamar samar musu aikin yi irin gyaran gashi, ko a wajen sayar da abinci ko kuma su ce za su samar musu guraben karatu.



An kwashe makonni ana shari’ar wadannan mutane 16 da suka kunshi mata 11 da maza 5, inda aka sami kowannensu da laiffuka dabam-dabam da suka hada da kawalci da fataucin mata.



An yankewa shugabar gungun masu karuwancin tare da maigidanta kowannensu daurin shekaru 10 da kuma biyan taran Euro dubu dari biyu.


Alkalin kotun ta ce wannan kadan kenan daga tanadin da suka yi wa masu aikata wannan mummunar aikin a kasar. Kuma wannan hukunci zai zama gargadi ga saura, saboda haka in kunne ya ji, jiki ya tsira.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)