Gaskiyar Bayani Game da Kamfanin Okadabooks



Assalamu alaikum



Okadabooks Kamfani ko ince wani  application na android, Iphone ko blackberry da aka kirkira don sauqaqawa Marubuta da Makaranta saye da siyarwar

 littafai. Da yawan Marubuta da Makaranta sunyi amanna da wannan kamfani ba kamar Marubuta da yanzu ya zamar masu hanya mafi sauki da zasu siyar da littafan su kuma su kar6e kudinsu cikin aminci.


CIKAKKEN BAYANI GAME DASU


Kamar yanda masu kamfanin yace : okadabooks an kirkireshi ne dan sauqawa mutane karantawa ko siyar da littafan su akan farashin da suke so. Inda a hakan kowa ke cin riba, masu kamfani, Marubuta da kuma Makaranta.



YADDA ABIN YAKE!


Idan kai Marubuci ne kuma kana bukatar siyar da littafi cikin Wannan kamfani, a duk littafi Daya idan ka mashi farashi okadabooks suna cire kaso 30 cikin 100 na littafin, misali idan ka dora littafi ka masa farashi akan Naira 500, idan wani ya shiga ya siya wannan N500 din okadabooks zasu cire N30 su tura maka N470 bisa account dinka na okadabooks. ba zaka cire kudin ba zuwa bank account dinka har sai kudin sun kai adadin da suke so.


ADADIN KUDIN DA AKE CIREWA


Ba zaka cire kudin da ka tara ba har sai sun kai Naira dubu goma ko fiye da haka ( N10k + ). Sun tanadar da wata wadda zaka bi ka cire kudin, ta hanyar tura masu da Nigerian bank account dinka ko Paypal Email dinka idan ba Dan 9ja bane kai.

Sukan ce idan ka tura masu request tsawon dadewar da zasu dauka basu turo maka kudinka Sati biyu ne ( 2 weeks) .

Amman idan har kaci sa'a cikin kwana uku suna iya turo maka kudin ka.



Insha Allahu Zan cigaba, kuma zanzo maku da yanda zakayi ka dora littafi a okadabooks

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)