ba za ki taba zama kyakkyawa ba sai kina bilicin


@BBC

Hadiza wata 'yar shekara 19 ce wadda aka haife ta da bakar fata mai kyau da kuma laushi.

Ta yanke shawarar fara bilicin ne lokacin da kawayenta farare suka samu mazajen aure.
"Zan yi ado in sa tufafi mai kyau kuma in sha kamshi, amma maza ba su kulawa da ni -kuma ma in sun kula da ni, toh dan wata farar yarinya ta ki su ne.
Fararen mata su ke jan hankalin duk mazan, shi yasa na yanke ma shawarar cewa zan fara shafe-shafe domin in zama fara.
An karba bleaching sosai a al’umma. Kamar an fi daga wa fararen mata kafa akan bakake.
Alal misali, a cikin tatsuniyoyinmu kusan dukkanin bayanan 'yan mata masu kyau da ake bayar sun fi mayar da hankali ne mace siririya fara mai dogon gashi da kuma idanu masu kyau.
Akwai wani karin magana da ke cewa wai "farar mace alkyabbar mata"!
Kuma za ki ji mutane suna cewa "ya samu mace fara kyakkyawa".
Amma ban taba jin wani ya taba cewa "baka ce amma kyakkyawa".
Kusan kamar yadda muke auna kyau na nufin mace baka ba za ta yi kyau ba.
Ba abin mamaki ba ne cewa, a cikin birnin Kano, ana tunanin cewa mazansu sun fi sha’awar mata farare.
Saboda wadannan matsin lambar, 'yan matanmu ba su da wani zabi sai dai su yi bleaching.
Cinikin kayayyakin bilicin a Kano yana kara zamowa mai riba domin rashin amincin matanmu da kuma kin jinin bakaken mata.
ÆŠaya daga cikin masu sana'a ya gaya mani cewa: "Mace bakar mace ba za ta taba yin kyau ba sai ta haskaka fatarta"
Duk da cewa bilicin wani abun da ake yayi a yanzu; an dade da fara yinsa.
A halin yanzu ana kiran abun da haskaka ko sauya alunin fata. Illolin yin bilicin na tsawon lokaci a kan fata yana da hadari sosai.
Illolin sun hada da ciwon daji na fata da gazawar koda, wanna zai sa mutum ya nemi sanin ko yin bilicin din na da amfani?
Tags

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)