Wani Mutum mai shekaru 87 wanda Allah ya azurtashi da 'ya'ya 13 da jikoki 127 da kuma 'ya'yan jikoki 203


Wani mutum mai rayuwa Ukraine wanda ake kyautata zaton shine yafi kowa yawan iyali a duniya.

Pavel Semenyuk, mai shekaru 87 wanda kullum bayada wani mafarki kamar a ce ya tara iyali masu yawa.. Cikin ikon Allah mafarkin Mr. Pavel ya tabbata, yanada mata daya wadda ta haifa masa 'ya'ya 13.

Bayan aurar da 'ya'yansa da Haife haifen da akayita samu, a yanzu haka Mr. Pavel yanada jikoki 127 da kuma É—iyan jikoki 203 da kuma É—iyan jikokin jikoki 3.


A yanzu haka dai wannan iyali suna rayuwa ne a cikin wani kauye mai suna Dobroslav dake cikin kasar Ukrain a karamar hukumar Odesa.


"A koda yaushe cikin farin ciki nake da wannan baiwar da Allah yayi min." a cewar Mr. Pavel ya kuma qara da cewa "Nasan sunayen wadanda suka fi girma a cikinsu amman bazan iya tuna sunan wadanda suka fi yarinta a cikinsu.




Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)