Wani Matashi ya kashe kanwarsa don ta dauki lokaci a bandaki ( Toilet)



Wani abu da ya faru a ranar 18 ga watan june a yankin Georgia ta Amurka.

Gavin Henderson mai shekaru 27 ya shigo gidansu a matse yana son shiga ban daki ( Toilet ) amman kuma sai ya tarar da Kanwarsa mai suna Keaira mai shekaru 15 a ban dakin.. Gavin yayi yayi da kanwar tashi ta fito domin a matse yake amman Kwanwar qememe taki fitowa kan cewa bata karasa abinda takeyi ba, hakan kuwa ya fusata Gavin a take ya nufi dakin girki ya dauko Wuka ya nufi bandakin ya shaqo kanwar tareda soka mata wukar har sau 53 a ciki. Wannnan abun duk ya faru ne akan idon karamar kanwarsu mai shekaru 16 a yayinda kuma iyayensu basu gidan.

Bayan wannan abu da ya faru matashi Gavin da kanshi ya fita da gudu uwa waje yana neman agaji.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)