Yanzu Yanzu : Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Kauyukan Dake Cikin Sokoto

Wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun kai hari kauyukan dake kewayen Gandi a karamar hukumar Rabah dake jihar Sokoto, inda suka kashe wasu mutane da ba’a bayyana adadinsu ba sannan kuma suka kona gidaje da sauran kayayyaki.

Kamfanin dillancin labaran Nigeria ta ruwaito cewa mazauna yankin da suka rayu a hare-haren na nan sun zama marasa galihu a yanzu.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandar jihar, Cordelia Nwewe, ya tabbatar da lamarin.


Nwewe ya ce kwamishinan yan sanda na jihar, Muritala Mani, da jami’an lafiya sun tafi karamar hukumar domin duba yanayin da lamarin ke ciki da kuma duba yawan mutanen da abun ya shafa.


Ya kara da cewa za’a ji Karin bayani da zaran kwamishinan yan sandan ya dawo.

Nwawe ya ce ana nan ana ci gaba da bincike.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)