Dubai : Wani Ango Ya saki Amaryarshi bayan mintuna 15 da daura Auren su.

Wani Al'amari mai rikitarwa da ya faru a lokacin bikin wani Aure a kasar Dubai.

 Wani Ango ya saki matarshi bayan Mintuna 15 da Daura Aurensu.. Abun ya faru ne sakamakon qin amincewa da sharuɗan Uban Amarya da Ango yayi.



Angon ya kashe kudi sama da Dirham 100 000 ( wato kusan Euro 23 000 ) a auren. 

A yayin da aka daura kowa cikin farin ciki... 

Sai Mahaifin Amarya ya gindayawa ango sharadin cewa zai bar Amarya ta rinqa Aiki ( Wato aikin Gwamnati ).. Shi kuwa Ango a fa fir yaqi yarda tareda cewa sai dai ya saketa. Haka kuwa akayi duk da kudin da ya kashe a take anan ya saketa.. wanda abun saida ya baiwa kowa dake wurin mamaki.



Ance Wannan ba shine karon farko ba, da aure ya mutu a take ba, sakamakon kin bin sharuɗan Uban Amarya.

Tags

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)