Faransa : Wani Matashi ɗan Kasar Ivory Coast Mai shekaru 18 yayi wa Yan Mata Yan ajinsu 20 Ciki a kasar Faransa tareda Gudowa Kasarshi.



Wani Matashi  ɗan Asalin Kasar Ivory Coast, dake karatu a kasar Faransa, ya gudo kasarshi sakamakon Yaudarar 'Yan matan ajinsu  20 tareda yiwa kowacce ciki.



Matashin Mai suna Lauren Bless mai shekaru 18, yazo Faransa karatu ne shekaru 2 da suka gabata, inda yayi wani abu wanda ba kasafai aka fiye jin labarin ba.



Mun Tuntuɓi Matashi Lauren dake zaune a Abijan tare da iyayenshi inda ya bamu labarin duk yanda abun ya wakana. 



Yan matan sun fahimci suna ɗauke da juna biyu ne sakamakon Gwajin da akeyi a makarantar yayin jarabawa, inda kowacce ta fahimci lallai cikin nashi ne.


A yanzu dai Haka daya daga cikin iyayen Yan Matan ya maka Matashi Lauren kotu, akan dole sai ya karbi cikin tareda Auren ɗiyarshi.

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)