An binne gawar wani mutum tareda kwalaban giya, kudi, tufafi da kuma wayoyin Salula (Hotuna)


A afrika ta kudu anyi wata jana'iza mai ban mamaki, inda wasu 'yan uwa da abokan wani mamaci suka binne gawarshi da giya, tufafi, kudi da kuma wayoyin salula.

Mamacin magidanci ne mai 'ya'ya uku ya mutu ne ranar Iyaye Maza ta duniya da akeyi a kowacce shekara, yayin da yake cikin shan giya rai yayi halinshi, hakan yasa 'yan uwanshi da abokanshi suka shirya mashi gagarumar jana'iza ta ban girma.


Wannan mamaci dai ya samu wannna girmamawane inda mutane sukayita jefa Wayoyin hannun su wasu kuma na cire tufafinsu suna jefawa a ciki wasu kuma suna bulbula ruwan giya a cikin kabarin.








Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)