An Kama Wani Pasto Mai Siyar da Tikitin Shiga Aljanna


A kasar Zimbabwe 'yan sanda sun cafke wani pasto dake sayar da tikitin shiga Aljanna.

Paston mai suna Tito Wats yana amsar mutane makudan kudade kimanin dalar amurka $500 a duk mutum daya akan zai siya mashui irin Lambun da Ubangiji ya sanya Adam da Hauwa a ciki, Kawai kana mutuwa zaka tarar da abunka a can.


Wasu kuwa da bazasu iya biyan irin wadannan kudade, to suna zuba dala 2 wato $2 a rana.




A yanzu haka dai wannan pasto ya shiga hannu, inda ya bayyanawa 'yan sanda cewa ai Jesus ne yace ya riqa amsa, a ziyarar da yake kawo masa kullum a dare.

Duk da tonuwar asirinsa har yanzu wasu daga cikin Mabiyansa na koken a sakar masu Pasto

Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)